Yadda za a yi karon-batta tsakanin Kamaru da Moroko, Senegal da Mali

Lokacin karatu: Minti 8

Za a ci gaba da wasannin zagayen kwata fainal da za a yi fafatawa biyu a gasar cin kofin nahiyar Afirka da ake yi a Morocco.

Za a fara da kece raini tsakanin Senegal da Mali sannan kuma na Kamaru da Morocco mai masaukin baƙi.

Senegal tana da Afcon ɗaya, Mali ta taɓa kaiwa zagayen karshe, Kamaru tana da biyar da kuma Morocco mai guda ɗaya.

Shin wace tawaga ce za ta kai daf da karshe a Afcon a Morocco?

Wasan Kamaru da Morocco mai masaukin baƙi

Tawagar Kamaru za ta kara da mai masaukin baƙi Morocco a kwata fainal a filin wasa na Prince Moulay Abdellah da ke birnin Rabat a ranar Juma'a.

Wannan shi ne karo na huɗu da ƙasashen biyu za su haɗu a gasar Afcon, inda Kamaru ba ta taɓa shan kashi ba a hannun Morocco ba a gasar cin kofin Afirka da yin nasara uku da canjaras ɗaya.

Hakan kuma shi ne karo na farko da za su haɗu a wannan ƙarni, sannan haɗuwarsu ta farko a gasar cikin tsawon shekaru 39 da wata 11 da kwanaki 29.

Haɗuwarsu ta farko a Afcon ita ce a shekarar 1986 da suka tashi 1-1 a karawar rukuni na biyu.

Kamaru ta fitar da Morocco, wadda ke matsayin mai masaukin baki, a wasan kusa da na ƙarshe a gasar a 1988.

Sun sake haɗuwa karo na uku a AFCON a shekarar 1992, inda Kamaru ta doke Morocco da ci 1-0 a wasansu na farko a rukuni na biyu.

Kamaru ba ta taɓa shan kashi ba a hannun Morocco a haɗuwarsu 13 ta farko daga 1981 zuwa 2017, inda ta yi nasara shida tare da yin canjaras huɗu.

Sai dai Morocco ta lashe haɗuwarsu biyu, ciki har da nasarar 2-0 a wasan neman gurbin shiga AFCON 2019 a ranar 16 ga Nuwamba 2018.

Morocco ta kuma yi nasara a haɗuwarsu ta baya-bayan nan a gasar CHAN ta 2020, wato ta ƴan wasan da ke taka leda a gida, inda ta doke Kamaru 4-0 a zagayen kusa da na ƙarshe, kafin daga bisani ta ɗaga kofin gasar.

Kamaru ta taɓa fuskantar ƙasashen da ke karɓar bakuncin Afcon sau 13 a baya, inda ta samu nasara shida, canjaras biyar, da shan kashi biyu.

Rashin nasara biyu kacal da Kamaru ta yi a hannun masu masaukin baki a Afcon sun haɗa a matakin rukuni a 1970 da 1996, inda ta sha kashi 2-0 a hannun Sudan da kuma 3-0 a hannun Afirka ta Kudu.

Kamaru ba ta sha kashi ba a wasa shida da ta buga da ƙasashen da ke karɓar bakuncin Afcon, inda ta yi nasara uku da canjaras uku.

Kamaru ta taɓa fuskantar ƙasashen da ke karɓar bakuncin gasar a matakan ziri ɗaya kwale sau shida a baya, inda ta yi rashin nasara a wasan ƙarshe a 1986 a hannun Masar.

Ta doke Senegal da ci 1-0 a kwata fainal a 1992, ta yi nasarar cin Morocco 1-0 a wasan kusa da na ƙarshe a 1988, sannan ta lallasa Mali da cin 3-0 a wasan kusa da na ƙarshe a 2002, sai ta doke Ghana 1-0 a wasan kusa da na ƙarshe a 2008, sannan ta yi nasara a kan Najeriya a bugun fenariti a wasan ƙarshe a 2000 bayan an tashi 2-2 har da karin lokaci.

Babbar nasarar Kamaru a kan ƙasar da ke karɓar bakunci, ita ce doke Mali 3-0 a wasan kusa da na ƙarshe a 2002, yayin da mafi muni da aka ci ta ƙwallaye da yawa shi ne rashin nasara 3-0 a hannun Afirka ta Kudu a wasan farko na rukuni a 1996.

An kara tsakanin Kamaru da Morocco su 13, Kamaru ta yi nasara biyar aka doke biyu da canjaras biyar da cin ƙwallo 11 aka zura mata tara a raga.

Daga ciki sau uku suka fafata a Afcon, inda Kamaru ta ci wasa biyu da canjaras ɗaya da cin ƙwallo uku, ɗaya ya shiga ragarta.

Sakamakon wasannin da suka buga a Afcon:

1986 – Rukuni na biyu – ranar 11 ga watan Maris 1986

  • Cameroon 1 - 1 Morocco

1988 – Wasan daf da karshe – ranar 23 ga watan Maris 1988

  • Morocco 0 - 1 Cameroon

1992 – rukuni na biyu – ranar 12 ga watan Janairu 1992

  • Cameroon 1- 0 Morocco

Kokarin da Kamaru ke yi a gasar kofin Afirka

Ta yi nasarar doke Afirka ta Kudu 2-1 da ta samu zuwa zagayen kwata fainals.

Wasan da ta ci Afirka ta Kudu, ita ce nasara ta 49 a Afcon a tarihi.

Za ta buga wasa na 11 a zagayen kwata fainal a Afcon, Najeriya ce a gabanta mai 12 a jerin kan gaba a buga gurbin ƴan takwas.

Cikin wasa 10 da ta buga a kwata fainal ta yi nasara biyar da canjaras biyu aka doke ta uku daga ciki.

Ta kuma yi nasara a kwata fainals a 1992 da 2000 da 2002 da 2008 da kuma 2021.

Ta lashe zagayen kwata fainal a bugun fenariti, bayan tashi 0-0 da Senegal a 2017.

An doke ta a zagayen kwata fainals a hannun Jamhuriyar Congo a 1998 da Najeriya a 2004 da Masar a 2010 da kuma Ivory Coast a bugun fenariti a 2006.

Wasan kwata fainals da ta buga an kai ga karin lokaci a wasa da Tunisiya a 2008 da ta yi nasara 3-2 da wanda Masar ta doke ta 3-1 a 2010.

Wasa ɗaya ne ta fuskanci mai masaukin baƙi a zagayen kwata fainals, inda ta yi nasara a kan Senegal a 1992.

Kuma da zarar ta yi nasara a kan Morocco ranar Juma'a, za ta kai daf da karshe na 11 kenan.

Bryan Mbeumo ya samar da damar cin kwallo har karo tara a Morocco, shi ne kan gaba a wannan kwazon tsakanin ƴan wasan Kamaru.

Ƙwazon da Morocco ke a gasar Afcon

Ta kai kwata fainal karo na biyar, bayan da ta yi nasara a kan Tanzaniya da cin 1-0.

Wasa huɗun da ta kara a zagayen kwata fainals 1998 da 2004 da 2017 da kuma 2021.

Ta yi nasarar cin zagayen a kwata fainal da doke Aljeriya 3-1 a 2004 a karin lokaci.

Ta kuma yi rashin nasara a zagayen kwata fainals a 1998 da 2017 da kuma 2021.

A zagayen kwata fainals huɗun da ta buga biyu daga ciki sai da ta kai da karin lokaci, inda ta yi nasara a 2004, sannan aka doke ta a 2021.

Dukkan kwata fainals huɗun da ta yi ba wanda ta kai ga bugun fenariti.

Gasar da ta kai daf da karshe a baya-bayan nan ita ce a 2004.

Brahim Diaz ya ci ƙwallo huɗu a wasannin bana, shi ne kan gaba a yawan zura ƙwallo a raga, shi ne kan gaba a wannan bajintar a tawagar Morocco a gasa ɗaya a Afcon

Morocco ce kan gaba a yawan raba kwallo a wasannin bana mai 2,184.

Wasan Senegal da Mali da za su kara a filin Tangier

Senegal da Mali za su fafata a zagayen kwata fainal a filin wasa na Grande Stade de Tanger.

Senegal ta buga dukkan wasanninta huɗu a birnin Tangier. Mali kuma ta yi karawa uku a Casablanca, ciki har da guda biyu a cikin rukuni da kuma zagaye ƴan 16, sannan ta buga ɗaya a zagayen rukuni a Rabat.

Wannan shi ne karo na biyu da Mali da Senegal za su haɗu a gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Haɗuwarsu ɗaya tilo a baya sun yi ne a 2004 a matakin rukuni, lokacin da suka hadu a rukuni na biyu. Wasan ya ƙare da sakamakon 1-1.

Dukkan tawagar biyu sun tsallaka zuwa kwata fainal a 2004 lokacin da aka haɗa su a rukuni na biyun, inda Mali ta kare a matsayin ta farko a rukunin, Senegal ta zo ta biyu a kan sauran da suka haɗa da Kenya da Burkina Faso.

Gaba ɗaya, sun haɗu sau 41 a dukkan karawa, inda Senegal ta yi nasara 19, yayin da Mali ta ci takwas, sannan wasa 13 suka ƙare da canjaras.

Senegal ta samu tikitin shiga gasar Afcon karon farko a shekarar 1965, inda ta doke Mali 2 - 0 a wasan neman shiga gasar a waje da kuma 3-1 da ta yi nasar a gida, ta kare a saman tebur a gaban Guinea da Mali.

Senegal ba ta sha kashi ba a wasan 13 na da Mali, inda ta yi nasara shida tare da yin canjaras bakwai.

Nasarar ƙarshe da Mali ta samu a kan Senegal ta zo ne a wasan sada zumunta ranar 26 ga Nuwamba 1997, inda ta yi nasara 2-1 a Dakar.

Haɗuwarsu ta baya-bayan nan itama wasan sada zumunta ne, wadda aka buga a ranar 26 ga Maris a 2019 a Dakar, inda Senegal ta yi nasara da ci 2-1.

Sun yi tata ɓurza a tsakaninsu sau 41, Mali ta yi nasara takwas, Senegal ta ci wasa 19 da canjaras 13, sannan ta ci kwallo 61 Mali ta zura mata 38.

Duk wasan da aka kare a bugun fenariti ana kirga shi duro.

Ba a ƙirga wasannin African Games daga shekarar 1991 zuwa gaba a cikin tarihin haɗuwa kai tsaye ba, domin waɗannan wasanni na masu karancin shekaru ne wato (age-group).

Haɗuwar da suka yi a Afcon:

2004 – cikin rukuni na biyu – ranar 2 ga watan Fabrairu 2004

  • Senegal 1 - 1 Mali

Bajintar da Mali ke yi a gasar Afcon a tarihi

Ta kai kwata fainals ba tare da cin ko da wasa ɗaya ba, inda ta tashi kunnen doki a dukkan wasa huɗu.

Za ta buga kwata fainals karo na takwas, bayan da ta kara a 1994 da 2002 da 2004 da 2012 da 2013 da kuma 2023.

Ta kuma kai gurbin daf da karshe sau biyar a1994 da 2002 da 2004 da 2012 da kuma 2023.

Wasa ɗaya ta yi rashin nasara a kwata fainal, shi ne a 2023, wadda Ivory Coast ta doke ta 2-1 har da karin lokaci.

Ta lashe biyu a zagayen kwata fainals a bugun fenariti a 2012 da kuma 2013, sannan ta doke Masar 1-0 a 1994 da nasara 2-0 a kan Afirka ta Kudu a 2002 da doke Guinea 2-1 a 2004.

Za ta kai zagayen daf da karshe a Afcon karo na shida da zarar ta yi nasara a kan Senegal, bayan 1972 da 1994 da 2002 da 2004 da 2012 da kuma 2013.

Sai dai rabon da ta kai gurbin daf da karshe tun bayan 2013.

A can baya ta kai daf da karshe a 1972 ba tare da cin wasa ba da yin canjaras uku a dukkan karawar cikin rukuni.

Watakila ta zama ta farko da za ta kai matakin daf da karshe ba tare da cin wasa ba daga biyar a minti 90 ko kuma karin lokaci a tarihin Afcon

Kawo yanzu Mali ta yi wasa canjaras biyar daga 63 da ta yi da yin nasara 21 aka doke ta 17 daga ciki.

Bajintar da Senegal ke yi a gasar cin kofin Afirka

Wannan shi ne karo na 10 da ta kai kwata fainal, inda ta yi nasara a irin wannan mataki a shekarar 2002 da 2006 da 2019 da kuma 2021.

Sun sha kashi a kwata fainal sau biyar, ɗaya daga ciki a bugun fenariti aka yi waje da ita.

Sun lashe zagayen kwata fainal a shekarar 2002 da 2006 da 2019 da kuma 2021.

Tayi rashin nasara a kwata fainal a bugun fenariti da Kamary ta kai zagayen daf da karshe a 2017.

Wasan da ta buga a kwata fainal har da karin lokaci, sannan ta yi nasara a hannun Najeriya a 2000.

Ta ci wasa uku a kwata fainal daga huɗun da ta yi a baya-bayan nan a Afcon.

Idan har ta ci wasan nan, za ta kai gurbin daf da karshe a karo na biyar.

Sadio Mane ya na da hannu a cin ƙwalo a wasa uku baya a Afcon.

Ya kuma bayar da uku aka zura a raga a Afcon da ake a Morocco, kenan shi ne kan gaba a wannan bajintar mai tara a gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Tawagar Senegal ta yi laifi karo 75, ita ce kan gaba a yin laifi a Afcon a Morocco.