Mene ne yawan man fetur ɗin Venezuela kuma me ya sa Amurka ke kwaɗayin shi?

Lokacin karatu: Minti 6

Sa'o'i kaɗan bayan da Amurka ta yi garkuwa da shugaban Venezuela Nicolas Maduro, shugaba Donald Trump ya sha alwashin cewa zai koma iko da albarkatun man ƙasar.

"Za mu samar da kamfanonin man Amurka masu girma, wanda ya fi kowanne a faɗin duniya, za mu shiga , za mu kashe biliyoyin kuɗaɗe, domin gyara matatun da suka lalace - sannan mu fara samarwa da ƙasar kuɗi," kamar yadda Trump ya faɗa a wani taron manema labarai ranar Asabar.

Kalaman Trump na zuwa ne a daidai lokacin da buƙatar man fetur ke ƙaruwa a kasuwannin duniya. Sai dai farashin man fetur bai ƙaru ba, sannan babu tabbacin ko za a samu buƙatar son mai yayin da duniya ke matsawa zuwa ababen hawa masu amfani da lantarki.

Yaya yawan fetur ɗin Venezuela?

An yi kiyasin cewa Venezuela tana da ganga biliyan 303 na man fetur, hakan ne ya sa ta kasance ƙasar da ta fi yawan mai a duniya - "tana da kashi 17 na yawan man duniya," a cewar Gideon Long, wakilin BBC kan ɓangaren kuɗi da aiki.

Saudiyya ita ce a matsayin na biyu na wadda ta fi yawan mai inda take da ganga biliyan 267.2, a cewar ƙungiya ƙasashe masu arzikin man fetur (OPEC). Waɗannan ƙasashe huɗu sun haɗa sama da rabin yawan man duniya.

Sai dai man da Venezuela ke samarwa ya yi kaɗan idan aka kwatanta da na ƙasashen.

A watan Nuwamba, an kiyasta cewa ƙasar ta samar da mai ganga 860,000 a kwana guda, a cewar rahoton da hukumar kula da makamashi ta duniya ta fitar.

Wannan dai bai fi kashi uku ba cikin man da take samarwa shekaru goma da suka wuce, kuma ƙasa da kashi ɗaya na man da ake samarwa a duniya.

Bambancin shi ne, an bayyana cewa Amurka na samar da gangar mai miliyan 13 a rana, in ji hukumar kula da makashi ta ƙasar.

Man fetur ɗin Venezuela na ɗauke da wasu abubuwa masu tauri a cikinsa wanda yake da wahala wajen tacewa idan aka kwatanta da na'uin mai mafi haske, amma shi ya fi kyau wajen samar da dizel da kwalta.

"Abu mafi muhimmanci shi ne yawan man Venezuela yana a gabashin ƙasar ne, kuma yana da wahalan kai wa, da yawa na cikin ƙungurmin daji, don haka ba abu ne mai sauki a iya haƙo shi daga ƙasa ba," in ji Long.

"Ɗanyen mai ne mai girma. Yana da yawa, amma ba shi ne ya fi inganci ba sai an sarrafa shi yadda ya kamata.... kuma wurare kaɗa kawai ake da su a duniya wajen iya sarrafa shi," inda wasu matatun da ke aikin ke a Texas, in ji shi.

Ƙona kowane irin mai na taimakawa wajen kawo sauyin yanayi, sai dai man Venezeula na cikin na'ukan "mai masu datti" a ɓangaren ɗumamar yanayi saboda irin sindarin gas da ke fita yayin tace shi," a cewar ƙwararru.

Me ya sa man da Venezuela ke samarwa ya ragu?

Man da Venezuela ke samarwa ya ragu cikin sauri tun shekara ta 2000, yayin da tsohon shugaban ƙasar, Hugo Chavez wanda Maduro ya gada ya tsaurara iko kan kamfanin man ƙasar, PDVSA, abin da ya janyo kwararrun ma'aikata da dama suka ajiye aikinsu.

Takunkumin da Amurka ta fara saka wa ƙasar kan zargin laifukan take hakkin ɗan'adam a 2015 lokacin mulkin tsohon shugaba Barack Obama, ya saka mutane ƙasa zuba jari a ƙasar.

"Babban kalubale da suka fuskanta shi ne a ɓangaren kayayyaki," in ji Callum Macpherson, shugaban kula da farashin kayayyaki a wata ƙungiyar zuba jari.

Wani babban mai bincike a cibiyar kula da makamashi a Oxford, Bill Farren Price ya faɗa wa BBC cewa akwai lokacin da ɓangaren man fetur na Venezeula "ya yi tashe da samun nasarori gomman shekaru da suka wuce" sai kuma ya samu koma-baya cikin sauri a shekaru 20 da suka wuce.

"An yi wadaƙa da kuma satar kayayyakin samar da mai da dama har ma da sayar da su," in ji shi.

Amurka ta taɓa kasancewa mai sayan man Venezuela, sai dai tun bayan zuwan Maduro kan mulki, China ta zama ƙasar da ɗaukacin man yake tafiya sama da shekara goma da suka wuce.

"A baya Amurka ta kasance tana sayan kashi 40 na man Venezuela a kowace shekara kuma tana yin haka ne saboda tana da damar sarrafa shi a Mashigar Mexico," in ji wakilin BBC Long.

"A lokacin Amurka na da damar samun ɗanyen mai a kusa da ita a Venezuela, ba sai ta je zuwa Gabas Ta Tsakiya ko kuma Rasha ba, tana kuma da girman sarrafa shi, kuma hakan ya yi wa duka ƙasashen aiki yadda suke so," in ji shi.

Waɗanne kamfanonin mai ke aiki a Venezuela?

Har yanzu wasu kamfanonin mai na ƙasashen yamma na aiki a Venezuela, ciki har da Chevron - kamfanin man ƙasar Amurka ɗaya tilo a ƙasar.

Sai dai, ayyukansu ya ragu matuka ainun yayin da Amurka ta faɗaɗa takunkumi da kuma ya shafi ɓangaren fitar da mai waje, inda suka yi haka da nufin daƙile damar Maduro na samun tattalin arziki mai nagarta.

Chevron ya samu lasisin aiki ne a 2022 karkashin mulkin tsohon shugaban ƙasar Amurka, Joe Biden, duk da takunkumai na Amurka.

Kamfanin, wanda ke da alhakin haƙo kusan kashi biyar na man Venezuela, ya ce ya mayar da hankali ne kan kariyar ma'aikatansa kuma yana "bin dukkan dokoki da sharuɗa".

Shin Amurka na bin Venezuela bashin kuɗin mai?

A wani taron manema labarai, shugaba Trump ya ce Amurka ce ta gina matatun man Venezuela, sai dai gwamnatin gurguzu ta ƙasar "ta sace su daga wurin mu".

"Mun gina mamatun man Venezuela ta hanya amfani da ƙwarewar Amurka da masu basirarta, amma gwamnati ta sace su daga wajenmu a jagoranci da suka gabata," in ji shi.

"Kuma sun sace su ne ta hanyar ƙarfi. Wannan ya zama ɗaya daga cikin sata mafi girma da aka yi wa ƙasarmu ta Amurka a tarihi," a cewar Trump.

Trump ya yi iƙirarinsa ne kan matakin da gwamnatocin Venezuela na baya suka ɗauka na mayar da harkar samar da mai na ƙasa baki ɗaya.

Karkashin dokar ƙasa da ƙasa, Venezuela na da ƴanci kan ɓangaren man fetur ɗin ta, abin da ya sa Amurka ba ta da hurumin cewa tana da iko da shi a doka.

A cewar sharuɗan da Majalisar Ɗinkin Duniya ta gindaya kan ƴancin albarkatun mai, ta ce ƙasashe masu ƴanci na da hakkin iko da da kuma amfani da albarkatunsu yadda suke so.

Amma kamfanonin ƙasashen waje, za su iya neman diyya idan aka yi amfani da kayayyakinsu.

Bayan da gwamnatin Hugo Chavez ta mayar da ɓangaren man ƙasar na ƙasa baki ɗaya a 2007, manyan kamfanonin man Amurka ExxonMobil da ConocoPhillips sun samu kwantiragi na biliyoyin daloli bayan hukuncin da kotu ta yanke. Venezuela ta yi watsi da hukuncin kuma ba ta bi umarnin da kotun ta bayar ba.

"Abubuwan da Chavez ya aikata suna da yawa kuma yanzu Venezuela ce za ta ɗanɗana kuɗarta, sai dai hakan ba yana nufin cewa man Venezuela ya zama mallakin Amurka bane. Suna da iko kan wanda aka ba su dama ne akwai," a cewar Francisco Monaldi, darektan wani shiri kan makamashi a Amurka.

Wane tasiri wannan lamari zai yi kan farashin mai?

Wani ƙwararre kan alkaluman farashi, Homayoun Falakshahi, ya ce abin da zai yi wa kamfanonin mai da ke jiran amfani da damar wajen cin gajiyar man Venezuela shi ne batun shari'a da siyasa.

Da yake tattaunawa da BBC, Homayoun ya ce kamfanonin na buƙatar kulla yarjejeniya da gwamnati, wanda hakan ba zai yiwu ba har sai an samu magajin Maduro.

Daga nan kamfanonin za su iya yin cacar biliyoyin dala kan ganin daidaituwar gwamnatin Venezuela a nan gaba, in ji shi.

"Ko da an samu daidaiton siyasa, lamari ne da zai ɗauki watanni," in ji ƙwararren.

Haka kuma, kamfanonin da ke son cin gajiyar matakin Trump za su buƙaci saka hannu kan yarjejeniya da sabuwar gwamnati kafin fara zuba jari a ɓangaren man Venezuela.

Masu sharhi sun yi gargaɗin cewa tsarin zai laƙume dubban biliyoyin dala - kuma zai iya kai shekara goma - domin ganin Venezuela ta koma fitar da irin man da ta saba.

Neil Shearing, wani ƙwararre kan tattalin arziki, ya ce tsare-tsaren Trump ba za su yi tasiri sosai kan ɓangaren samar da mai da kuma farashinsa a duniya ba.

"Akwai abubuwa da yawa da ya kamata a kaucewa kuma adadin lokacin da ake da shi na faruwar abubuwa yana da tsawo" cewa watakila ƙaruwar farashin mai kaɗan za a iya gani a 2026, in ji shi.

Shearing ya ƙara da cewa kamfanoni ba za su zuba jari ba har sai an samu gwamnati mai ɗorewa a ƙasar.

Ko da Venezuela ta koma samar da mai kamar a baya na ganga miliyan ɗaya a rana, ba zai sa ta shiga jerin ƙasashe goma na farko masu samar da mai a duniya ba, in ji Shearing.

Ya kuma bayyana irin yawan man da ƙasashe masu arzikin man fetur na Opec ke samarwa, inda ya ce duniya ba ta "cikin matsi na ƙarancin mai".