Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shugabannin ƙasashe huɗu da Amurka ta kama
Amurka ta gurfanar da shugaban Venezuela Nicolas Maduro bayan samamen da ta kai a ƙasarsa ta kama shi, bisa zargin zama jagoran gungun masu safarar ƙwayoyi.
Lamarin ya janyo suka daga ɓangarori da dama, inda Majalisar Dinkin Duniya ta ce an "saɓa dokar ƙasa da ƙasa" a matakin na kama Shugaba Maduro.
Amurka ta ce ta ɗauki matakin ne a wani ɓangare na tuhumar da aka daɗe ana yi wa Maduro kan hannu a safarar ƙwaya da kuma aikata miyagun laifuka.
Wannan ba shi ne karon farko da Amurka ta ɗauki mataki irin wannan ba a kan shugaban wata ƙasa mai ƴanci.
Venezuela - Nicolas Maduro
A tsawon watanni, jami'an leƙen asiri na Amurka sun riƙa lura da duk wani motsi na Shugaba Nicolas Maduro.
Wata ƙanƙanuwar tawaga, ciki har da wasu a cikin gwamnatin Venezuela sun riƙa lura da inda Maduro ke kwana da abin da yake ci da tufafin da yake sanyawa har ma da dabbobin gidansa, kamar yadda majiyoyin soji suka tabbatar.
A farkon watan Disamban 2025 ne aka kammala tsara shirin kama shugaban, wanda aka yi wa laƙabi da "Operation Absolute Resolve" a turance.
Da misalin ƙarfe 11 na daren ranar Asabar 3 ga watan Janairun 2026 ne shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da umarnin kama Nicolas Maduro.
Trump ya kalli yadda aka kai samamen kama shugaban kai-tsaye a gidansa na Mar-a-Lago da ke jihar Florida, tare da shugaban hukumar CIA John Ratcliffe da kuma sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio.
Sama da jiragen yaƙin Amurka 150 aka tura a cikin wannan daren domin gudanar da aikin, waɗanda suka haɗa da jirage masu kai farmaki da kuma masu kai kayan aiki, in ji wasu majiyoyi na gwamnatin Amurka.
Daga nan aka fara jin saukar bama-bamai a birnin Caracas da misalin ƙarfe 2 na dare, inda nan take hayaƙi ya turnuƙe sararin samaniya.
Sashen tantance bayanai na BBC ya tabbatar da cewa an kai farmaki kan cibiyoyi biyar. Wasu daga cikin hare-haren na Amurka an kai su ne kan garkuwar Venezuela daga hare-hare ta sama da cibiyoyin soji.
Dakarun Amurka sun isa gidan ɓoyo na shugaba Maduro ne da ke tsakiyar birnin Caracas da misalin ƙarfe 2 na dare.
Bayan isar su an yi musayar wuta, kamar yadda jami'in sojin Amurka ya tabbatar. Kafin sojojin na Amurka suka ɓalla ƙofofin ƙarfe na gidan suka isa inda yake.
Duk da cewa shugaban na Venezuela ya yi ƙoƙarin tserewa, amma sojojin na Amurka sun samu nasarar kama shi, kamar yadda Trump ya bayyana.
Inda daga nan ne aka yi tsinke da shi zuwa birnin New York na Amurka, aka tsare shi, sannan kuma aka gurfanar da shi a kotu.
Iraqi - Saddam Hussein
A watan Disamban 2023 ne Amurka ta kama shugaban Iraqi Saddam Hussein bayan Amurkar ta mamaye ƙasar bisa zargin cewa Saddam ya mallaki makaman ƙare dangi.
An kama Saddam ne bayan wani bayanin sirri da aka ƙyanƙyasa wa dakarun Amurka, cewa shugaban na ɓuya a wani ƙaramin rami a kusa da wani gidan gona da ke birnin Tikrit, mahaifar shugaban.
Jami'in sojin Amurka da ya jagoranci samamen, Kanar James Hickey ya ce Saddam ya fito daga ramin sannan ya miƙa wuya jim kadan gabanin sojoji su jefa gurneti cikin ramin.
Wani mutum ne da aka kama a birnin Baghdad, kwana daya gabanin haka, ya fallasa maɓuyar shugaban.
An zaro Saddam daga cikin ramin da yake ɓoye ne da misalin ƙarfe 10:30 na dare.
Lokacin da sojoji suka leƙa ramin sai suka ga mutum ya miƙo hannuwansa biyu. "Alamar cewa mutumin na so ya miƙa wuya," in ji Kanar Hickey.
Daga nan aka zaro shi aka "sumar da shi" sannan "aka nannaɗe" shi.
Bai nuna turjiya ba duk kuwa da cewa yana ɗauke da ƙaramar bindigar fistol.
"Sunana Saddam Hussein. Ni ne shugaban Iraqi kuma a shirye nake a tattauna," kamar yadda ya faɗa wa sojojin Amurka a cikin harshen Ingilishi, in ji Manjo Bryan Reed, jami'in tsare-tsare na birged na ɗaya.
Daga ƙarshe an kashe Saddam Hussein a ranar Asabar 30 ga watan Nuwamban 2006 ta hanyar rataya a arewacin birnin Baghdad.
An yi hakan ne bayan kama shi da laifukan cin zarafin bil'adama, ciki har da zargin kisan ƴan Shi'a 148.
Panama - Manuel Noriega
Amurka ta kai samame a ƙasar Panama a watan Disamban 1989 inda ta tsige shugaban ƙasar bisa zargin ayyukan da suka ci karo da dimokuradiyya da ayyukan rashawa da safarar ƙwaya da kuma yunkurin kare fararen hula.
Amurka ta yi amfani da dubban sojoji wajen kai samamen, wanda ya wakana ta ruwa da sama da kuma ta ƙasa.
Lamarin ya faru ne a ranar 20 ga watan Disamban 1989, lokacin da dangantakar Amurka da Manuel Noreiga ta yi taɓarɓarewa da ba za ta iya gyaruwa ba.
A wani jawabi da ya yi wa al'ummar Amurka, shugaban ƙasar na wancan lokaci George H W Bush ya ce ya tura sojoji zuwa Panama domin "kare rayukan Amurkawa" da kuma gurfanar da Noriega a gaban shari'a.
Sanarwar na zuwa ne ƴan kwanaki bayan dakarun Panama sun kashe wani jami'in Amurka. Kuma a wannan lokacin Noriega na fuskantar tuhuma kan safarar ƙwaya da kuma zargin maguɗi a zaɓen ƙasar na 1989.
Samamen na Amurka ya ƙunshi dakaru sama da 20,000 waɗanda suka kutsa ƙasar suka ƙwace iko da manyan cibiyoyin soji na ƙasar.
A hukumance an bayyana cewa an kashe sojoji da fararen hula ƴan Panama 514, sai dai wasu majiyoyi a ƙasar na cewa yawan mutanen da aka kashe ya kai 1,000. Haka nan jami'an sojin Amurka 23 ne aka kashe.
Samamen ya mayar da birnin Panama City wani fagen yaƙi.
A wannan lokaci Noriega ya nemi mafaka a ofishin jakadancin Vatican da ke birnin. Sojojin Amurka sun kasance a wajen ofishin suna dakonsa.
A ƙarshe shugaban ya miƙa wuya a ranar 3 ga watan Janairun 1990, bayan kwashe kwana 11 a cikin ofishin.
Daga nan ne aka tafi da shi ofishin yaƙi da miyagun ƙwayoyi da ke birnin Miami na Amurka domin gurfanar da shi a kotu, inda daga ƙarshe aka kama shi da laifin safarar ƙwaya da halasta kuɗin haram.
Noriega ya shafe sauran rayuwarsa a gidan yari a Amurka da Faransa sai kuma lokacin da aka yi masa ɗaurin talala a gidansa da ke Panama.
Ya rasu a shekarar 2017 yana da shekara 83 a duniya.
Honduras - Juan Orlando Hernandez
A watan Fabarairun 2022 ne Amurka ta kama tsohon shugaban Honduras jim kadan bayan ya sauka daga mukaminsa. Daga nan aka kai shi Amurka bisa zargin ayyukan rashawa da safarar ƙwaya.
An kama Mista Hernandez ne a gidansa, makonni kaɗan bayan kammala wa'adin mulkinsa na biyu.
An tura jami'an ƴansanda zuwa gidansa da ke Tegucigalpa, babban birnin ƙasar, sa'o'i bayan Amurka ta buƙaci a miƙa mata shi.
Lokacin da jami'an ƴansanda suka isa gidansa, Hernandez ya miƙa wuya, inda nan take aka garƙama masa ankwa aka fitar da shi.
Ya mulki Honduras ne daga watan Janairun 2014 har zuwa 2022.
A watan Maris na 2024 ne wata kotu a birnin New York ta kama tsohon shugaban ƙasar da laifin hada baki wajen shigar da hodar ibilis Amurka da kuma mallakar miyagun bindigogi.
Sai dai a shekarar 2025 ne shugaban Amurka Donald Trump ya yafe wa tsohon shugaban ƙasar na Honduras Juan Orlando Hernández bayan a baya kotu ta yanke masa hukuncin ɗauri na shekara 45.
Trump ya yi zargin cewa hukuncin da aka yanke wa Hernandez bi ta da ƙullin siyasa ne kuma akwai "rashin adalici sannan an tsaurara."
Yafiyar da Trump ya yi wa tsohon shugaban na Honduras ta bai wa mutane da dama mamaki ganin irin laifukan da aka kama shi da su.