Samu ƙarin bayani kan shafinmu na tattalin data

Lokacin karatu: Minti 1

Kuna amfani da shafin labarai mai rubutu kawai na BBC Hausa wanda zai ba ku damar tattalin data. Abu mai muhimmnaci shi ne, duk rubutun da ke ƙunshe a labaranmu na cikin wannan shafi na tattalin data.

Burinmu shi ne mu samar da shafin labarai mai sauƙin buɗewa kuma maras tsada ga masu karatu. Mun san cewa masu bibiyar shafukanmu na BBC World News na zama ne a yankuna daban-daban na duniya, farashin data ya bambanta, ƙarfin intanet ya bambanta, sannan wayoyin da kuke amfani da su sun sha bamban.

Domin samar da wannan tsari na shafi mai tattalin data mun cire wasu abubuwa da za su sa a ga bambanci kaɗan a wurare daban-daban.

Misali, ba za a ga hoto ko bidiyo a shafin tattalin data ba. Hakan ba yana nufin kwata-kwata ba za ku iya samun su ba, kawai dai yana a babban shafin ne. Za ku iya ganin hotuna da bidiyo cikin sauƙi ta hanyar latsa nan idan kun fi son hakan.

Wannan shafi sabon tsari ne da muka ɓullo da shi, saboda haka har yanzu muna ƙoƙarin inganta shi. Muna fatan zai zamo mai amfani gare ku.