Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Afcon 2025: Mali 0-1 Senegal, Kamaru 0-2 Moroko

Wannan shafi ne da ya kawo muku bayani kai-tsaye kan wasan Mali da Senegal da kuma Kamaru da Moroko a zagayen kwata-fainal na gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2025 a Moroko.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Mohammed Abdu, Isiyaku Muhammad da Ahmad Bawage

  1. AN TASHI WASA: Moroko ta kai wasan daf da karshe, Kamaru 0-2 Moroko

    Tawagar kasar Moroko ta kai wasan daf da karshe a Gasar Çin Kofin Afirka, bayan doke Kamaru 2-0.

  2. Kamaru dai ba ta saduda ba tana ci gaba da matsin lamba a gidan Moroko.

    Sai dai har yanzu ta ƙasa farke kwallo.

    Tana da jan aiki a gabanta a halin yanzu....

  3. Goaaaal!! Moroko ta ci kwallo ta biyu, Kamaru 0-2 Moroko

    Moroko ta zura kwallo ta biyu a ragar Kamaru ta hannun ɗan wasanta na tsakiya Saibari.

    Wannan ce kwallonsa ta farko a gasar Afcon ta bana.

  4. Ɗan wasan Kamar Bryan Mbeumo ya faɗi a yadi na 18, sai dai alkalin wasa ya ce babu wani abu.

  5. Moroko ta sake samun wata dama mai kyau, sai dai ɗan wasan baya na Kamaru Samuel Kotto ya tare kwallon, inda ya hana Moroko ƙara kwallo.

  6. Kocin tawagar Kamaru a fusa ce, ya ƙagu ƴan wasan sa su farke kwallo.

  7. Babu abin da ake ji a cikin filin wasan sai sowa da ihun magoya bayan Moroko.

    Suna ƙarfafa wa ƴan wasansu.

  8. Kamaru ta cushe kwallo cikin yadi na 18 na Moroko, sai dai Moroko ta fitar ta ita daga wata barazana.

  9. Moroko na da mintoci 45 don samun damar zuwa wasan daf da karshe, amma sai ta jajirce wajen ganin ba a farke kwallon da ta jefa ba - ko kuma ta ƙara wani kwallon.

    Bisa dukkan alamu dai Kamaru ta dawo da karsashinta a wannan zagaye na biyu ganin yadda ƴan wasanta ke buga kwallo.

  10. An dawo daga hutun rabin lokaci, Kamaru 0-1 Moroko

    Ƴan wasan tawagogin biyu sun koma zagaye na biyu na wannan fafatawa mai zafi.

    Kamaru ce ta fara take kwallo.

  11. Hutun rabin lokaci, Kamaru 0-1 Moroko

    An tafi hutun rabin lokaci: Moroko na gaban Kamaru da 1-0.

  12. Moroko na ci gaba da mamaye wasan bayan haɗari na wasu lokuta da Kamaru ta nuna.

    Minti biyu ya rage a tafi hutun rabin lokaci.

  13. Kamaru ta samu bugun tazara kusa da gidan Moroko, sai dai kwallon ba ta yi wani haɗari ba.

  14. Goaaaaal! Moroko ta ci kwallo daya, Kamaru 0-1 Moroko

    Brahim Díaz ya zura wa Moroko kwallonta na farko a wannan fafatawa.

    Shi ne ɗan wasan da ya fi zura kwallo a gasar - yana da kwallaye biyar.

  15. Samuel Eto'o na bin wasan sau da ƙafa kuma yana ba da umarni ga ƴan wasan ƙasarsa ta Kamaru.

  16. Kamaru ta karɓi kwallo daga gidanta inda ta ruga ta nufi gidan Moroko, sai dai ba a yi nisa ba Moroko ta ƙwace kwallon.

  17. Hakimi ya kai kwallo zuwa yadi na 18 na Kamaru bayan bugun tazara, sai dai ɗan wasan baya na kamaru ya samu damar fitar da kwallon zuwa waje.

  18. Moroko na ci gaba da kai ƙora zuwa ragar Kamaru, ba sa barin Kamaru ta riƙe kwallo na tsawon lokaci.

  19. Filin wasa na Prince Moulay Abdellah da ke birnin Rabat ya cika maƙil da magoya bayan Moroko - waɗanda suka fito cikin ɗaruruwa domin marawa ƙasar su baya.

  20. An fara wasa tsakanin Kamaru da Moroko, Kamaru 0-0 Moroko

    An take wasa tsakanin Kamaru da Moroko a wasan zagayen kwata-fainal na Gaar Cin Kofin Afirka.