Ƴan wasan da suka fi zura ƙwallo a Gasar Kofin Afirka ta 2025

Lokacin karatu: Minti 2

Gasar cin kofin nahiyar Afirka ta kai matakin wasan kusa da ƙarshe.

Ƙasashen Moroko da Najeriya da Masar da kuma Senegal ne za su fafata a matakin, wanda daga shi sai wasan ƙarshe.

Za a buga wasan ƙarshe ne ranar 18 ga watan Janairun 2026.

Ya zuwa yanzu zaratan ƴan ƙwallo na ci gaba da ɗaga raga.

Ga jerin ƴan wasan da suka fi zura ƙwallo daga farkon gasar zuwa yanzu:

  • Brahim Díaz (Moroko): Ƙwallo - 5
  • Victor Osimhen (Najeriya): Ƙwallo - 4
  • Mohamed Salah (Masar): Ƙwallo - 4
  • Ademola Lookman (Najeriya): Ƙwallo - 3
  • Ayoub El Kaabi (Moroko): Ƙwallo - 3
  • Amad Diallo (Ivory Coast) - Ƙwallo - 3
  • Riyad Mahrez (Aljeriya): Ƙwallo - 3
  • Lassine Sinayoko (Mali): Ƙwallo - 3

Bayan nan akwai ƴan wasa 12 waɗanda suka zura ƙwallo bibbiyu daga farkon gasar, kamar irin su R. Onyedika da Addams A na Najeriya da C. Ndiaye na Senegal, da G. Kakuta na DR Congo da dai sauran su.

Sai kuma ƴan wasa 56 waɗanda suka zura ƙwallo ɗaɗɗaya, kamar Sadio Mane na Senegal, da A. Adams na Najeriya da sauran su.

Taimakawa a zura ƙwallo

Ɗan wasan Najeriya Ademola Lookman ne ya fi yawan taimakawa a zura ƙwallo, inda ya taimaka sau huɗu.

Daga nan sai ɗan wasan Senegal, Sadio Mane, wanda ya taimaka aka zura ƙwallo uku.

Akwai kuma wasu ƴan wasa 10 da suka taimaka sau bibbiyu wajen zura ƙwallo, kamar Osimhen da Adams A na Najeriya.

Za mu ci gaba da sabunta wannan shafi, yayin da ake ci gaba da wasannin.