Ƴan wasan da suka fi zura ƙwallo a Gasar Kofin Afirka ta 2025

Asalin hoton, Getty Images
Gasar cin kofin nahiyar Afirka ta fara nisa, inda yanzu haka aka kammala zagayen 'yan 16, kuma tuni aka san waɗanda za su buga kwata-fainal.
Ƙasashen da suka je gaba su ne: Masar, Kamaru, Najeriya, Algeria, Senegal, Mali, Ivory Coast da Kamaru.
Za a buga wasan ƙarshe ne ranar 18 ga watan Janairun 2026.
Ya zuwa yanzu zaratan ƴan kwallo na ci gaba da ɗaga raga.
Ga jerin ƴan wasan da suka fi zura ƙwallo daga farkon gasar zuwa yanzu:
- Brahim Díaz (Moroko): Ƙwallo - 4
- Ademola Lookman (Najeriya): Ƙwallo - 3
- Amad Diallo (Ivory Coast) - Ƙwallo - 3
- Victor Osimhen (Najeriya): Ƙwallo - 3
- Riyad Mahrez (Aljeriya): Ƙwallo - 3
- Ayoub El Kaabi (Moroko): Ƙwallo - 3
- Mohamed Salah (Masar): Ƙwallo - 3
- Lassine Sinayoko (Mali): Ƙwallo - 3
Bayan nan akwai ƴan wasa 12 waɗanda suka zura ƙwallo bibbiyu daga farkon gasar, kamar irin su R. Onyedika na Najeriya da C. Ndiaye na Senegal, da G. Kakuta na DR Congo da dai sauran su.
Sai kuma ƴan wasa 56 waɗanda suka zura ƙwallo ɗaɗɗaya, kamar Sadio Mane na Senegal, da A. Adams na Najeriya da sauran su.
Taimakawa a zura ƙwallo
Ɗan wasan Najeriya Ademola Lookman ne ya fi yawan taimakawa a zura ƙwallo, inda ya taimaka sau huɗu.
Daga nan sai ɗan wasan Senegal, Sadio Mane, wanda ya taimaka aka zura ƙwallo uku.
Akwai kuma wasu ƴan wasa 10 da suka taimaka sau bibbiyu wajen zura ƙwallo.
Za mu ci gaba da sabunta wannan shafi, yayin da ake ci gaba da wasannin.










