Fitattun ƴan wasa biyar da ba su taɓa lashe gasar AFCON ba

Asalin hoton, Getty Images
Dangantakar Mohamed Salah da Liverpool na taɓarɓarewa a halin yanzu, amma duk da haka ba a shakkar kokwanton nasarar da ya samu a Anfield.
Fitaccen ɗan wasan na Masar ya lashe gasanni da dama a lokacin da yake tare da ƙungiyar ta Reds, amma abin mamaki bai taɓa lashe gasar cin kofin Afrika (Afcon) da ƙasarsa ba.
Yayin da ɗan wasan gaban zai iya sauya wannan labarin a cikin wata mai zuwa a gasar ta 2025 da za a yi a Morocco, hankali ya fara komawa kan wasu daga cikin manyan ƴan wasan ƙwallon ƙafa na Afirka da ba su taɓa samun nasarar lashe kofin ba.
BBC Sport Africa ta zayyano manyan ƴan wasa biyar da suka kasance fitattu, amma ba su taɓa samun nasarar lashe babbar gasar ta ƙwallon Afirka ba.
Mohamed Salah (Masar)

Asalin hoton, Getty Images
A yanzu da yake da shekara 33, ko wannan ce damar ƙarshe da kyaftin ɗin na Masar ke da ita na lashe gasar?
Masar ita ce ƙasar da ta fi kowacce samun nasara a gasar, inda ta lashe kofuna bakwai.
Abin mamaki shi ne Masar ta kasa samun tikitin shiga gasar AFCON na 2012 da 2013 da 2015, wanda ke nufin ya buga gasarsa ta farko ne a 2017 lokacin da ƙasar da ke yankin arewacin Afirka ta sha kashi a hannun Kamaru a wasan ƙarshe.
Salah, wanda ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afrika a shekarar 2017 da 2018, ya jure rashin nasara a gida a gasar AFCON ta 2019, wadda Afrika ta Kudu ta yi waje da ita a wasan zagaye na ƴan 16.
Masar ta koma wasan ƙarshe a gasar ta 2021 - wasan da Salah ya sha kashi a hannun abokin wasansa na Liverpool a lokacin Sadio Mane a wasan da aka tashi da bugun fanerati.
Salah wanda yanzu yake na biyu a jerin ƴan wasan da suka fi zura ƙwallaye a tawagar Masar, ya ji rauni a matakin rukuni na gasar AFCON na 2023, lamarin da ya ya tilasta masa kallon yadda DR Congo ta fitar da tawagarsa a zagaye na biyu.
Didier Drogba (Ivory Coast)

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Drogba ya kasance ɗanwasa mai taka rawar gani a manyan wasanni a Chelsea, inda ya zura ƙwallaye tara a manyan wasannin ƙarshe 10 da ya buga wa Blues ya kuma ɗauki kofin a wasanni takwas cikin waɗannan wasannin.
Duk da ƙoƙarin ɗanwasan, bai samu nasarar samun nasara ba a wasannin ƙarshe biyu da ya jagoranci tawagar Ivory Coast a matsayin kyaftin.
A shekara ta 2006, Elephants ta buga fanerati da mai masaukin baƙi Masar, amma Drogba ya ɓarar da bugunsa, inda Masar ta yi nasara da ci 4-2.
Ƙasar ta Afirka ta yamma ta sake zuwa wasan ƙarshe a shekarar 2012 a matsayin ƙasar da aka fi tunanin lashe gasar, amma ta yi rashin nasara.
Sauran gasannin da ya buga wa ƙasar akwai wadda suka ƙare a matsayi ta huɗu a shekarar 2008 da guda biyu da aka cire su a matakin kwata fainal (2010 da 2013), kafin ya yi ritaya daga ƙwallon ƙafa a watan Agustan 2014.
Sai dai wata shida bayan ritayarsa, Ivory Coast ta doke Ghana a wasan ƙarshe na 2015, a bugun fanarati.
George Weah (Laberiya)

Asalin hoton, Getty Images
In dai batun lashe kyautuka a fagen wasa ne, tsohon ɗan wasan Paris St-Germain da AC Milan da Chelsea ya fi kowane ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Afirka.
Weah ya kasance mutum ɗaya tilo daga nahiyar da ya lashe kyautar Ballon d'Or, inda ya samu kambun a shekarar 1995 - a wannan shekarar ne ya zama gwarzon ɗan ƙwallon Afrika a karo na biyu.
Amma duk da haka bai iya samun irin nasarorin da ya samu a kulob ɗinsa da Laberiya ba.
Ƙasar ta yammacin Afirka ta buga wasanni biyu ne kacal a rukuninsu na farko a gasar a shekarar 1996, bayan da Najeriya ta fice daga gasar. An yi waje da ita daga gasar ne bayan da ta yi nasara a kan Gabon sai kuma ta sha kashi a hannun Zaire (DR Congo).
Laberiya ta koma gasar AFCON a shekara ta 2002, a lokacin da shekaru suka cimma Weah.
Yana da shekara 35, amma ya zura ƙwallo ɗaya tilo da ya taɓa ci a AFCON a wasan farko da suka buga da Mali, amma tawagar Lone Stars ta sake kasa fitowa daga rukuninta.
Bayan kasancewa kyaftin ɗin ƙasarsa, Weah ya ci gaba da jagorantar al'ummarsa a matsayin shugaban ƙasa tsakanin shekarar 2018 zuwa 2024.
Nwankwo Kanu (Najeriya)

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan na gaba ya lashe kofuna da dama a turai, ciki har da gasar zakarun Turai a Ajax da kuma kofin UEFA Cup a Inter Milan kafin ya samu nasarar lashe kofuna a Arsenal.
A lokacin ne Kanu ya rubuta sunansa a tarihin ƙwallon ƙafa na Najeriya a matsayin wani gwarzon ɗan wasa tawagar Najeriya a ɓangaren da suka lashe gasar cin kofin duniya na ƴan ƙasa da shekara 17 a 1993 da kuma lambar zinare a gasar Olympics ta 1996.
Sai dai kofin AFCON ne ya gagare shi, kuma ya kusa da lashewa a shekarar 2000, lokacin da Super Eagles ta yi rashin nasara a wasan ƙarshe a hannun Kamaru da bugun fanarati.
Kanu, mai shekara 23 a lokacin, bai yi nasara a nasa bugun ba, kuma Najeriya ba ta sake komawa wasan ƙarshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka ba a lokacin da yake taka leda.
Gwarzon ɗan ƙwallon Afirka sau biyu, ya yi ritaya da zinare a gasar Olympic amma azurfa da tagulla ne kawai ya samu daga gasar cin kofin Nahiyar Afrika.
Michael Essien (Ghana)

Asalin hoton, Getty Images
Gasar ƙarshe na AFCON guda huɗu da Ghana ta yi, ta zo ne a shekarar 1982, wanda hakan ke nufin manyan ƴan wasa da dama sun kasa ɗaukar kofin tare da Black Stars.
Daga cikin su akwai Essien, wanda za a iya cewa shi ne ɗan wasan tsakiya mafi hazaƙa a ƙasarsa.
Kamar Drogba, ya ci nasara tare da Chelsea tsakanin 2006 da 2012 amma bai samu irin wannan nasarar ba a ƙasarsa.
Lokacin da Essien yake matashi ya shiga tawagar da aka doke su a wasan daf da na kusa da na ƙarshe a shekara ta 2002, Ghana ta rasa samun gurbi a 2004, yayin da ya ji rauni a 2006.
An sanya sunan shi a cikin tawagar gasar a lokacin da Ghana ta karɓi baƙunci a 2008, amma Kamaru ta lallasa ta a wasan kusa da na ƙarshe kafin ta dawo ta ƙare matsayi na uku.
Essien ya ji rauni ne a tsakiyar gasar ta 2010, abin da ya tilasta masa kallon yadda abokan wasansa suka koma wasan ƙarshe a karon farko cikin shekaru 18, amma Masar ta doke su da ci 1-0.











