Yadda Najeriya ta kai mataki kwata fayinal a Gasar Kofin Afirka

Asalin hoton, Reuters
Najeriya ta samu gurbi a wasannain zagayen kwata fayinal a gasar Cin Kofin Afirka bayan doke Mozambique da ci 4-0.
Super Eagles ta zama ta farko da ta ci ƙwallo huɗu a bana a Morocco kuma ba tare da an zura mata ko ɗaya ba.
Tun da farko an fara karawa tsakanin Masar da Benin da karfe biyar na yammaci daidai da agogon Najeriya da Niger, inda Masar ta samu nasara da ci 2-1.
Super Eagles ta yi ta ɗaya a rukuni na uku da maki tara, ita kuwa Mozambique tana daga cikin huɗun da aka yi wa alfarmar zuwa zagaye na biyun da maki uku daga rukuni na shida da ta yi ta uku.
Masar ma ita ce ta yi ta ɗaya a rukuni na biyu da maki bakwai, Benin kuwa alfarma aka yi mata daga rukuni na huɗu da maki uku, bayan karewa a mataki na uku.
Wasan farko tsakanin Masar da Benin

Asalin hoton, Getty Images
Masar na buga wasannin da ake a Morocco da fatan lashe kofin nahiyar Afirka, karo na takwas jimilla, ita ce kan gaba a yawan ɗaukar kofin a tarihi.
Ita kuwa Benin na fatan kai wa zagayen ƙwata fainal a karo na biyu a tarihin Afcon.
Wasan da tawagogin biyu suka fuskanci juna a baya-bayan nan, shi ne a rukuni na uku a 2010 a lokacin Masar ta kai zagaye na gaba, duk da haka Masar ce ta yi nasarar cin 2-0
Jimilla sau huɗu suka fafata, inda Masar ta yi nasara uku da canjaras ɗaya, inda kuma ta ci ƙwallo a dukkan wasa huɗun, yayin da Benin ta zura ƙwallo a uku daga ciki.
Bajintar da Masar ke yi a gasar kofin Afirka

Asalin hoton, Getty Images
- Masar ce ta ja ragamar rukuni na biyu, sakamakon cin Zimbabwe da Afirka ta Kudu da yin canjaras da Angola.
- Tayi amfani da ƴan wasa 26 a Morocco, idan ka ƙwatanta da guda 22 da ta yi amfani da su a Afcon a 2023.
- Idan har Masar ta yi nasara za ta kai zagayen kwata fainal karo na 11 (1994, 1996, 1998, 2000, 2002, 2006, 2008, 2010, 2017 da kuma 2021).
- Mohamed Salah ya ci ya ci ƙwallo 10 a Afcon a tawagar Masar, zama na farko mai yawan cin ƙwallaye a Masar a Afcon.
- Sai dai bai taɓa cin ƙwallo a wasa uku ba a jere a Afcon
Ƙoƙarin da Benin take ta yi a Afcon

Asalin hoton, Getty Images
- Benin za ta buga zagaye na biyu a karo na biyu bayan 2019.
- A wasan da fara yin a zagayen ƴan 16 a 2019 ta tashi 1-1 da Morocco daga baya ta yi nasara 4-1 a bugun fenariti bayan karin lokaci.
- Wannan shi ne na huɗu da za ta fuskanci tawaga daga Arewacin Afirka.
- Ƙwallo ɗaya kawai ta ci a wasannin da ake yi a Morocco.
Yadda Najeriya ta casa Mozambique

Asalin hoton, X/Super Eagles
Najeriya na fatan lashe Afcon na huɗu a bana a Morocco, za kuma ta ƙara da Mozambique a wasan zagaye na biyu ranar Litinin a Stade de Fes.
Wannan shi ne karo na biyu da za su kece raini a gasar cin kofin Afirka.
Sun fara haɗuwa a karawar cikin rukuni a 2010, inda Najeriya ta yi nasara 3-0
Jimilla sau biyar suka fafata a tsakaninsu, Najeriya ta yi nasara huɗu da canjaras ɗaya.
Wasan baya-bayan nan da suka haɗu shi ne a sada zumunta da suka yi ranar 16 ga watan Oktoban 2023 a Portugal, Najeriya ce ta yi nasara 3-2.
Ƙwazon da Najeriya ke yi a tarihin Afcon

Asalin hoton, Getty Images
- Wannan shi ne karo na 18 da Super Eagles ta kai zagaye na biyu kai tsaye.
- Karo na 16 a jere ta kawo wannan matakin, bayan da ta kasa kai wa zagaye na biyu a 1982.
- Ta kuma lashe dukkan wasa uku da ta yi a rukuni a Morocco, bayan cin Tanzania 2–1 da doke Tunisia 3–2 da nasara akan Uganda da cin 3–1.
- Karon farko da Najeriya ta yi nasara a dukkan wasa uku a cikin rukuni tun bayan 2021.
- Idan har Super Eagles ta yi nasara, zai zama karo na 61 da za ta ci wasa a Afcon, ita ta biyu a yawan cin wasa a gasar kofin Afirka bayan Masar mai 62.
- Ta ci ƙwallo takwas a karawar cikin rukuni, karon farko da ta zura da yawa a raga a Afcon a fafatawar cikin rukuni.
- An kuma zura ƙwallo huɗu a ragar Najeriya a wasannin cikin rukuni a Morocco, kenan guda 99 aka ci Super Eagles a tarihin gasar.
- Idan aka zura mata ƙwallo a wasa da Mozambique za ta shiga jerin waɗanda aka ci 100 ko sama da haka da ya haɗa da Ivory Coast da ci ƙwallo 112 da Jamhuriyar Congo 112 da kuma Tunisiya da aka ci ƙwallo 102.
- Idan har Najeriya ta yi nasara za ta kai zagayen kwata fainals karo na 12, mai Afcon uku.
- Tun lokacin da fara kwata fainal a 1992, sau ɗaya ne Super Eagles ba ta kai zagayen ƴan takwas ba, shi ne a 2021.
Faɗi-tashin Mozambique a gasar cin kofin Afirka

Asalin hoton, Getty Images
- Mozambique ta kawo wannan matakin karon farko daga Afcon na shida.
- Ba ta kai zagaye na biyu ba daga karawa biyar baya a wasannin cikin rukuni.
- Mozambique da Zimbabwe su ne tawagogin da aka zura wa ƙwallaye a kowanne wasa 18 da suka yi a Afcon.
- Mozambique ta yi rashin nasara uku da ta fuskanci Ivory Coast ta fuskanci Masar sau huɗu an doke ta uku da canjaras ɗaya da fafatawa biyu da Ghana daga ciki ta yi canjaras ɗaya aka doke ta ɗaya.
- Sannan ba ta zura ƙwallo ba a raga daga wasa bakwai da aka doke ta da ta fuskanci tawaga daga Yammacin Afirka.











