Tawagar Najeriya ta kai zagayen daf da karshe a Afcon, bayan da ta doke Aljeriya 2-0 a wasan kwata fainal ranar Asabar a Morocco.
Super Eagles ta ci ƙwallon ta hannun Victor Osimhen da kuma ta hannun Akor.
Karo na biyu a jere da ƙwallo bai shiga ragar Najeriya ba, bayan da ta doke Mozambique 4-0 a zagayen ƴan 16.
Kenan Super Eagles ta zura ƙwallo 14 a raga, inda huɗu ne suka shiga ragarta.
Ranar Laraba Nageriya za ta kara da mai masaukin baki Morocco, wadda ta fitar da Kamaru ranar Juma'a.
Idan anjima za a buga wasan kwata fainal na karshe tsakanin Masar da Ivory Coast.
Duk wadda ta yi nasara a fafatawar za ta fuskanci Senegal a daf da karshe ranar Laraba.
Ita dai Senegal ta kai daf da karshe sakamakon nasara a kan Mali ranar Juma'a.