Najeriya za ta kara da Morocco a daf da karshe a Afcon

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku bayanai kan wasan Aljeriya da Najeriya zagayen kwata fainals a gasar kofin nahiyar Afirka ta 2025 da ake yi a Moroko.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Nan muka kawo karshen shirin

    Nan na kawo karshen shirin da fatan za ku tara nan gaba kan sharhi da bayanai da muke kawo muku kai tsaye a gasar kofin Afirka daga Morocco.

    Da karfe 8:00 na dare daidai da agogon Najeriya da Niger za a fara wasan Masar da Ivory Coast mai rike da kofin.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skipper nake ce muku sai anjimanku.

  2. An tashi wasan - Najeriya ta kai daf da karshe, Aljeriya 0-2 Najeriya

    Afcon

    Asalin hoton, Getty Images

    Tawagar Najeriya ta kai zagayen daf da karshe a Afcon, bayan da ta doke Aljeriya 2-0 a wasan kwata fainal ranar Asabar a Morocco.

    Super Eagles ta ci ƙwallon ta hannun Victor Osimhen da kuma ta hannun Akor.

    Karo na biyu a jere da ƙwallo bai shiga ragar Najeriya ba, bayan da ta doke Mozambique 4-0 a zagayen ƴan 16.

    Kenan Super Eagles ta zura ƙwallo 14 a raga, inda huɗu ne suka shiga ragarta.

    Ranar Laraba Nageriya za ta kara da mai masaukin baki Morocco, wadda ta fitar da Kamaru ranar Juma'a.

    Idan anjima za a buga wasan kwata fainal na karshe tsakanin Masar da Ivory Coast.

    Duk wadda ta yi nasara a fafatawar za ta fuskanci Senegal a daf da karshe ranar Laraba.

    Ita dai Senegal ta kai daf da karshe sakamakon nasara a kan Mali ranar Juma'a.

  3. , Aljeriya 0-2 Najeriya

    Moses Simon na Najeriya ya karɓi katin gargaɗi, saboda ketar da ya yi.

  4. , Aljeriya 0-2 Najeriya

    Ɗan wasan Najeriya Raphael Onyedika daga Najeriya ya yi keta.

  5. , Aljeriya 0-2 Najeriya

    Farès Chaïbi ya samu bugun tazara, bayan da aka yi masa keta.

  6. , Aljeriya 0-2 Najeriya

    An yi wa Victor Osimhen na Najeriya keta daf da wajen jifa a gidan Aljeriya.

  7. , Aljeriya 0-2 Najeriya

    Najeriya ta saka Igoh Ogbu ya maye gurbin Bright Osayi-Samuel.

  8. , Aljeriya 0-2 Najeriya

    Redouane Berkane na Aljeriya ya yi laifi.

  9. , Aljeriya 0-2 Najeriya

    Alex Iwobi na Najeriya ya samu bugun tazara daga tsakiyar fili.

  10. , Aljeriya 0-2 Najeriya

    An yi karin minti shida daga nan idan Aljeriya ba ta farke ba sai a tashi wasan.

  11. , Aljeriya 0-2 Najeriya

    An bai wa ɗan wasan Najeriya, Stanley Nwabali katin gargaɗi.

  12. , Aljeriya 0-2 Najeriya

    Ramy Bensebaini na Aljeriya ya nemi raga da kafar hagu amma ta yi sama da faɗi.

  13. Aljeriya ta yi canji biyu, Aljeriya 0-2 Najeriya

    Himad Abdelli ya maye gurbin Hicham Boudaoui.

    Redouane Berkane ya maye gurbin Mohammed Amoura.

  14. , Aljeriya 0-2 Najeriya

    Baghdad Bounedjah na Aljeriya ya buga ƙwallon da Rafik Belghali ya buga masa, sai dai ta yi yawa.

  15. , Aljeriya 0-2 Najeriya

    Akor Adams na Najeriya ne ya saka wa ƙwallon da Bruno Onyemaechi ya bugu masa kai, amma ta yi sama ta fita waje.

  16. , Aljeriya 0-2 Najeriya

    Ademola Lookman daga Najeriya ya buga wata kwallon da Moses Simon ya bashi a cikin gidan Aljeriya, amma sun sa kafa sun tare ta.

  17. , Aljeriya 0-2 Najeriya

    Raphael Onyedika na Najeriya ya samu bugun tazara daga can baya.

  18. , Aljeriya 0-2 Najeriya

    Afcon

    Asalin hoton, Getty Images

    Hicham Boudaoui na Aljeriya ya karɓi katin gargaɗi, sakamakon ketar da ya yi wa Ademola Lookman na Najeriya. Kimanin ƴan wasa biyar daga Aljeriya sun karɓi katin gargaɗi.

  19. , Aljeriya 0-2 Najeriya

    Satar gida - ɗan wasan Najeriya, Akor Adams ya yi satar gida.

  20. , Aljeriya 0-2 Najeriya

    Ademola Lookman na Najeriya ya samu bugun tazara.