Super Eagles ta ɗauki fansa a kan Aljeriya a gasar Afcon da ci 2-0

Afcon

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Tawagar Najeriya ta kai zagayen daf da karshe a Afcon, bayan da ta doke Aljeriya 2-0 a wasan kwata fainal ranar Asabar a Morocco.

Super Eagles ta ci ƙwallon ta hannun Victor Osimhen da kuma ta hannun Akor.

Karo na biyu a jere da ƙwallo bai shiga ragar Najeriya ba, bayan da ta doke Mozambique 4-0 a zagayen ƴan 16.

Kenan Super Eagles ta zura ƙwallo 14 a raga, inda huɗu ne suka shiga ragarta.

Ranar Laraba Nageriya za ta kara da mai masaukin baki Morocco, wadda ta fitar da Kamaru ranar Juma'a.

Wasa mai zafi tsakanin Aljeriya da Najeriya a Afcon

Najeriya ta fara da ɗaukar Afcon a karon farko a tarihi a matakin mai masaukin baki a 1980 da doke Aljeriya 3-0 a Legas.

Itama Aljeriya ta fara da lashe Afcon na farko a 1990 kan Najeriya da cin 5-1 a wasan farko daga baya ta ci Super Eagles 1-0 a zagayen karshe a lokacin da Clemens Westerhof ke jan ragamar Najeriya.

Sai kuma a 2019 da Aljeriya ta yi nasara a kan Najeriya a zagayen daf da karshe, inda Riyad Mahrez ya ci ƙwallon a bugun tazara daga baya Aljeriya ta doke Senegal ta kuma lashe kofin.

Wasan karshe da suka fuskanci juna shi ne a sada zumunta a cikin Satumbar 2022 a Oran, inda Aljeriya ta yi nasarar cin 2-1.

Fitattun ƴan wasan Aljeriya

Afcon

Asalin hoton, Getty Images

Ƙyaftin ɗin tawagar Aljeriya, Riyad Mahrez yana taka rawar gani a Afcon a Morocco, duk da cewar shekaru sun ja, amma yana da gogewa da kwarewa, wanda yake da ƙwallo uku a raga kawo yanzu.

Haka kuma Ibrahim Maza ya ci ƙwallo biyu da Anis Moussa shima mai biyu a raga a Morocco, dukkansu masu zafi ne da zarar sun samu dama ba wasa.

Yana da mahimmaci Super Eagles ta sa ido a kan Mohamed Amoura, wanda shi ne kan gaba a yawan zura ƙwallaye a raga a wasannin neman shiga gasar kofin duniya ta 2026 da za a yi a bana a Amurka da Canada da kuma Mexico.

Haka kuma mai tsaron ragar Aljeriya, Luca Zidane ɗan gidan Zinedine Zidane ƙwallo ɗaya ne ya shiga ragarsa daga wasa huɗu kawo yanzu a Morocco, kenan yana kokarin ganin tawagarsa ta ɗauki wannan kofin a karo na uku jimilla.

Fitattun ƴan wasan Najeriya

Afcon

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tun kan fara Afcon an sa ran Victor Osimhen ne zai taka rawar gani a wasannin bana, sai dai kuma Ademla Lookman ne ke haskawa a tawagar ta Super Eagles.

Tun kan kammala gasar ana cewa Lookman ne fitatcen ɗan wasa a Afcon a Morocco, wanda ya ci ƙwallo uku kawo yanzu da bayar da huɗu aka zura a raga.

Haka kuma Lookman na aiki ne a matakin mai baiwa ƴan gaba ƙwallo, sannan ya taimaka wajen tsare gida, hakika Lookman na nuna kansa a wasannin da ake buga wa a bana

Har yanzu ana ganin Osimhen bai kai kan ganiya ba a gasar nan, domin yadda ya ƙware a zura ƙwallo a raga ya kamata waɗanda ya ci a Morocco su haura ukun da yake da su.

To sai dai a duk wasa yana sa ƙwazo yana damun masu tsare baya da kazar-kazar da ɓarar da damar maki, kenan Super Eagles ba ta samun matsi da yawa idan yana cikin fili.

Haka shima ɗan wasan gaba Akor Adam yana nuna kansa, wanda ya ci ƙwallo ya kuma bayar da biyu aka zura a raga, kuma Alex Iwobi yana raba ƙwallo tun daga tsakiya da kuma Wilfred Ndidi da yake da matukar mahimmancin a wasannin Najeriya.

Duk wadda ta yi nasara wacce tawagar za ta fuskanta?

Da zarar an tashi daga wannan wasan, duk wadda ta yi nasara za ta kara da Morocco ranar Laraba a wasan daf da karshe a Rabat.

Morocco ta kai zagayen daf da karshe ranar Juma'a bayan da ta doke Kamaru 2-0.

Itama Senegal ta kai daf da karshe, bayan cin Mali 1-0 a ranar ta Juma'a, wadda za ta fuskanci duk wadda ta yi nasara tsakanin wasan Masar da Ivory Coast da za a yi ranar Asabar.