Yadda yaƙin Iran zai shafi farashin man fetur a Najeriya da duniya

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Ibrahim Haruna
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 7
Yaƙi na ci gaba da rincaɓewa tsakanin Iran da Amurka da kuma Isra'ila tun bayan kisan jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei.
Yayin da Isra'ila da Amurka ke ci gaba da kai wa Iran hari a biranenta, Iran ta matsa ƙaimi wajen kai hare-hare kan duk wata kadarar Amurka da wasu cibiyoyin makamashi a yankin Gabas ta tsakiya.
Wani abu da ake ganin wannan yaƙi zai shafa shi ne fannin makamashi.
Farashin gangar man fetur ya tashi da ƙarin kashi 4% yayin da rikicin ke ci gaba da ƙazancewa a Gabas ta Tsakiya.
A ranar Talata an riƙa sayar da gangan man fetur ɗaya kan dala 80, wanda shi ne farashi mafi tsada daga farkon wannan shekara.
Iran ta datse mashigar Hormuz - wanda wata ƙaramar mashiga ce da ake bi wajen safarar man fetur, wadda ta haɗa yankin Gulf da tekun Indiya.
Kimanin kashi 20% na man fetur ɗin da ake amfani da shi a duniya na bi ta mashigar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Iran ta cinna wa jiragen ruwa da dama waɗanda suka yi yunƙurin bi ta mashigar domin safarar man fetur.
Ta yaya yaƙin Iran da Amurka zai shafi Najeriya?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
BBC ta tuntuɓi masani kan harkar makamashi a Najeriya Farfesa Ahmed Adamu, wanda malami ne a jami'ar Philomath University da ke Najeriya, inda ya ce babu shakka halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya zai shafi farashin man fetur a Najeriya.
"Wajibi ne farashin man fetur a kasuwar duniya zai tashi saboda Iran ce ƙasa ta huɗu mafi samar da man fetur a duniya."
Ya yi gargaɗin cewa a Najeriya, za a iya samun hauhawar farashin man fetur da gas, bayan da farashin ɗanyen mai ya tashi a kasuwannin duniya.
Masanan na ganin duk da dai hauhawar farashin danyan man zai iya bunƙasa kuɗaɗen shigar Najeriya, amma hakan zai shafi farashin litar mai a ƙasar wanda kuma zai shafi fannoni da dama kamar sufuri da kayan masarufi.
"Ko a cikin gidanka ka ke samar da ɗanyen man fetur, farashinsa yana daidaituwa ne da farashin man fetur a duniya," in ji Farfesa Adamu.
"Saboda haka duk da a Najeriya ake samar da man fetur kuma ba a yaƙi a Najeriyar, sannan za mu sayar wa ɗan Najeriya (Dangote) ne man fetur ɗin, za mu sayar da shi ne a daidai farashin duniya, kamar yadda ake sayarwa a Amurka haka za a sayar da shi a cikin Najeriya.
Ya ƙara da cewa "saboda haka idan aka sayar wa matatun man fetur na Najeriya ɗanyen man fetur da tsada, su ma za su sayar da abin da suka tace da tsada, sannan kuma za a sayar wa al'umma da tsada".
Ko gwamnati za ta iya ɗaukar mataki?
"Babu abin da gwamnati za ta iya yi, saboda kasuwa a buɗe take, duk yadda farashi ya kasance a kasuwannin duniya, zai shafi farashin man fetur a cikin gida," a cewar masanin tattalin arziƙin na man fetur.
Mashigar Hormuz

Asalin hoton, Stocktrek / Getty Images
Mashigar Hormuz - hanyar safarar man fetur mafi muhimmanci a duniya - ta tsaya cak bayan a ranar Litinin Iran ta ce za ta "cinna wa duk wanda ya yi yunƙurin wucewa ta cikinta."
Mataimakin babban kwamandan rundunar juyin juya hali na Iran, Ebrahim Jabbari ne ya sanar da hakan lokacin da yake magana a kafar talabijin ta ƙasar.
"Kada su sake su zo wannan yankin. Za su fuskanci tsattsauran mataki daga wurin mu," in ji shi.
Kimanin kashi ɗaya cikin biyar na man fetur na duniya na ratsawa ne ta mashigar, wadda faɗin wuri mafi tsukewa a cikinta bai fi kilomita 40 ba.
Farashin makamashi ya ci gaba da tashi tun bayan da yaƙi ya ɓarke tsakanin Iran da Amurka da Isra'ila.
Tsohon jami'in hukumar leƙen asiri ta Birtaniya MI6, Sir Alex Younger ya taɓa shaida wa BBC cewa "rufe mashigar zai haifar da gagarumar matsalar tattalin arziƙi saboda tasirin hakan a kan farashin man fetur.

Asalin hoton, Atta Kenare / Getty Images
Yawan man fetur da ke ratsawa ta Hormuz
Fiye da ganga miliyan 20 na ɗanyen man fetur da dangoginsa ne suka ratsa ta mashigar Hormuz kowace rana a bara, kamar yadda alƙaluma suka nuna.
Wannan na nufin cewa makamashin da kuɗinsa ya kai dala biliyan 600 ne aka yi safararsa ta hanyoyin ruwa a shekara ɗaya.
Iran da sauran ƙasashe mamabobin ƙungiyar ƙasashen da ke samar da man fetur ta duniya OPEC, kamar Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabwa da Kuwait da Iraq suna fitar da ɗanyen man fetur ɗinsu ne ta mashigar, yawanci zuwa ƙasashen Asia.
Mene ne faɗin mashigar Hormuz?

Mashigar Hormuz wata hanyar ruwan teku ne da ke tsakanin Iran da ƙasar Oman.
Hanyar shigarta da ta fita na da faɗin kimanin kilomita 50 yayin da wurin mafi tsukewa a tsakiyar mashigar na da fadin kilomita 40.
Sai dai a taskiyar ruwan ne kawai ake da zurfin da zai bai wa manyan jiragen dakon mai damar wucewa.
Masu lura da sufurin ruwa sun tsara yadda ake wucewa ta mashigar, wanda ya nuna cewa jiragen na iya bi ne kawai ta wani wuri wanda faɗinsa bai wuce kilomita 10 ba.

Asalin hoton, Gallo Images via Getty Images
Mataki na tsaro
Masana na ganin cewa rufe mashigar Hormuz tamkar nuna wani ƙarfin iko ne daga Iran - tamkar mallakar makamin nukiliya.
Kamar yadda ƙasashen duniya suka tashi tsaye wajen ganin Iran ba ta mallaki makamin nukiliya ba, haka nan manyan ƙasashen duniya suka sha nanata cewa ba za su bari Iran ta yi amfani da yankin da take ba wajen datse hanyar da ake safarar makamashin duniya ba.
Masana na ganin cewa Iran za ta iya datse mashigar ce ta ɗan wani lokaci, inda daga baya Amurka za ta iya yin amfani da ƙarfin soji cikin gaggawa wajen ganin an buɗe ta.
Hanyoyin da Iran za ta iya datse mashigar Hormuz

Asalin hoton, NurPhoto via Getty Images
Wani rahoton majalisar dokokin Amurka a shekarar 2012 ya nuna cewa Iran na iya bin wasu matakai wajen datse mashigar Hormuz, waɗanda suka haɗa da:
- Sanar da daste mashigar ba tare da faɗin hukuncin wanda ya karya dokar ba
- Sanar da bincika ko ƙwace duk wani jirgin ruwa da ya bi ta mashigar
- Yin harbin gargaɗi ga jiragen da ke bi ta mashigar
- Yin amfani da ƙarfin soji wajen kai wa jiragen ruwa hari
- Dasa nakiyoyi a ƙarƙashin ruwan mashigar
- Amfani da jirage masu tafiya ƙarƙashin ruwa

Asalin hoton, Getty Images
Waɗanne ƙasashe za su fi wahala idan aka datse mashigar?
Bincike kamfanin Vortexa ya nuna cewa Saudiyya na fitar da ɗanyen man fetur kimanin ganga miliyan 6 a rana ta mashigar Hormuz - fiye da kowace ƙasa da ke maƙwaftaka.
Hukumar samar da bayanai kan makamashi ta Amurka ta yi ƙiyasin cewa kashi 84% na ɗanyen man fetur da dangoginsa da ake bi da shi ta mashigar na zuwa ƙasashen Asia ne a 2024.
Bayanin ya ce ƙasashen China da Indiya da Japan da Koriya ta Kudu ne ƙasashen da suka fi sayen man fetur ɗin da ke bi ta mashigar.

Asalin hoton, Chip Hires via Getty Images
Hukumar ta ce Amurka ta sayi man fetur wanda yawansa ya kai ganga 500,000 ta mashigar a 2024 - wato kimanin kashi 7% na jimillar man da ƙasar ke saye.
Ɗaukacin yawan man fetur da ƙasashen Turai ke saye ta mashigar ya bai kai ganga miliyan ɗaya ba a kowace rana.
Hakan na nuna cewa ƙasashen Larabawa da na Asia ne za su fi shan wahala idan Iran ta rufe mashigar, fiye da Amurka da Turai.

Asalin hoton, Getty Images
Wasu hanyoyin na daban
Barazanar da ake yawan samu game da datse mashigar Hormuz a tsawon shekaru ta sanya ƙasashen da ke fitar da man fetur a yankin suka nemi wata hanyar ta daban.
A shekarar 2019, Saudiyya ta sake wa wani bututun safarar gas fasali ta yadda zai iya ɗaukar ɗanyen man fetur.
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa kuma ta ja wani bututun da ya haɗa filayen haƙar man fetur haƙar ɗin ta da tashar ruwa ta Fujaira da ke gaɓar Oman










