Me zai faru idan Iran ta datse mashigar Hormuz sanadiyar hare-haren Isra'ila?

Asalin hoton, Stocktrek / Getty Images
- Marubuci, Newsroom reporters
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Persian
- Lokacin karatu: Minti 7
Musayar wuta da ake yi tsakanin Isra'ila da Iran ta jawo fargabar yiwuwar Iran ta datse hada-hadar jiragen ruwa a mashigar Hurmuz, wanda shi ne hanyar dakon man fetur mafi muhimmanci a duniya.
Kusan kashi biyar na ɗanyen man da ake amfani da shi a duniya yana bi ta mashigar ne mai girman kilomita 40.
Iran za ta iya ɗaukar matakin hana wucewa ta mashigar, kamar yadda kwamandan rundunar sojin ruwa na ƙasar Iran ya bayyana.
Tsohon shugaban hukumar leƙen asirin Birtaniya wato M16, Sir Alex Younger ya shaida wa BBC cewa daga cikin manyan matsalolin da yaƙin zai haifar akwai datse tekun. "Datse tekun zai haifar matsalar tattalin arziki mai girma saboda yadda zai shafi farashin man fetur."

Asalin hoton, Atta Kenare / Getty Images
Yawan fetur da ake jigila ta tekun
Hukumar ƙididdigar makamashi ta Amurka US Energy Information Administration (EIA) ta ƙiyasta cewa a farkon shekarar 2023 an yi dakon kusan ganga miliyan 20 na fetur a a kullum ta tekun.
Wannan ke nufin ana kasuwancin kusan dala biliyan 600 na makamashi duk shekara ta tekun.
Duk wani tsaiko a tekun zai iya jawo matsala a hada-hadar man fetur a duniya, wanda nan take za a iya gani ta hanyar tashin farashin man.
Sai dai masana suna gargaɗin cewa ɗaukar wannan matakin zai iya zafafa rikicin na Isra'ila da Iran.
Wannan kuwa shi ne zai jawo wasu ƙasashen cikin rikicin, ciki har da Amurka, wadda take ta'allaƙa da man fetur daga ƙasashen Larabawa.
Yaya girman mashigar Hormuz?

Mashigar Hormuz na tsakanin Iran da Oman ne. Tekun na da faɗin kilomita 50.
Taswirar tekun ta nuna ɓangarorin da suke da kyau a tsaya, da wuraren da ba a so a tsaya da kuma tudun mun tsira a tsakanin ɓangarorin biyu.
Idan tankokin mai za su wuce, sai su wuce ta kusa da tsibirin Greater da Lesser Tunb - inda ake takun-saƙa tsakanin Iran da ƙasashen Larabawa kan mallakinsa.
Masana sun ce yaƙi na cikin abubuwan da suke jawo tsaiko a hada-hada ta mashigar kamar yadda ya faru a yakin Iran da Iran a shekarar 1980 zuwa 1988.

Asalin hoton, Gallo Images via Getty Images
Amfani da tekun domin kare kai?
Masana sun ce a wajen Iran, datse hada-hada a mashigar Hormuz na nufin amfani da wata dama domin kare kanta.
Kamar yadda ƙasashen duniya suka daɗe suna adawa da yunƙurin Iran na samun nukiliya, manyan ƙasashen duniya sun sha nanata cewa ba za su bari Iran ta yi amfani da tekun ba wajen shaƙe duniya game da samun makamashi.
Masana sun yi hasashen cewa Iran za ta iya datse mashigar na wani ɗan lokaci. Amma wasu na ganin Amurka da ƙawayenta ba za ta bari hakan ya ɗauki lokaci ba, inda suke hasashen Amurka za ta iya amfani da ƙarfin soji wajen buɗe mashigar.
Ta yaya Iran za ta iya datse mashigar Hormuz?

Asalin hoton, NurPhoto via Getty Images
A wani bincike da cibiyar bincike ta Congressional Research Service ta Amurka ta nuna, ta ce Iran za ta iya ɗaukar matakin a hankali. Hanyoyin sun ƙunshi:
- Sanar da hana sufurin jiragen ruwa ba tare da bayyana hukuncin saɓa dokar ba
- Sanar da tantance jiragen dakon man ko kuma ƙwacewa
- Yin ɓarin wuta kan jiragen dakon
- Kai farmaki kan wasu jiragen dakon
- Binne wasu nakiyoyin ruwa a tekun
- Kai farmaki kan wasu jiragen kasuwanci da na soji

Asalin hoton, AFP via Getty Images
A yaƙin Iran da Iraq, Iran ta yi amfani da makamin Silkworm domin kai farmaki kan tankokin man fetur, sannan ta dasa nakiyoyi a cikin teku.
Ɗaya daga cikin nakiyoyin ne ya fasa jirgin USS Samuel B Roberts, wanda ya sa Amurka ta mayar da martani.
Sai dai duk da haka Iran ba ta datse mashigar ba baki ɗaya, amma ta ƙara harajin shige da fice, sannan taa lafta wasu ƙa'idoji da suka jawo cunkuson jirage wajen ficewa daga gaɓar tekun.

Asalin hoton, Norbert Schiller via Getty Images
Ƙarfin sojin Iran
Kwana biyu kafin harin Isra'ila da ya kashe kwamandan dakarun juyin juya-halin Iran Manjo Janar Hossein Salami, kwamandan ya ziyarci sashen sojin ruwa da ke aiki a mashigar.
Ya bayyana yankin tekun a matsayin ɗaya daga cikin muhimman yankunan kare kai da ƙasar ke da su.
Ya bayyana jirgin da zai iya tafiya tsawon kilomita 10 cikin minti uku a yankin.

Asalin hoton, NurPhoto via Getty Images
Janar Salami ya ce za su yi amfani da manyan makaman masu cin dogon zango domin kare ƙasarsu. Ya kuma ce za su yi amfani da nakiyoyin ruwa.
Salami ya ce za su faɗaɗa ayyukan jirage maras matuƙa.
Me masana suke hasashe?
Masana suna hasashen ɗaya daga cikin hanyoyin da Iran za ta bi domin datse dakon kusan jirage 3,000 da suke wucewa ta tekun a kusan duk wata ita ce dasa nakiyoyi da amfani da jirage masu cin dogon zango domin kai farmaki kan jiragen.
Sojojin Iran da dakarun juyin juya-hali na ƙasar za su iya kai farmaki kan jiragen dakon man ƙasashen waje.
Sai dai kuma Amurka da Isra'ila za su iya kai farmaki kan manyan jiragen ruwan soji idan Isra'ila suka yi amfani da su.
Yanzu haka kafar bibiya harkokin tekun ƙasar da ke amfani tauraron ɗan'adam sun nuna jiragen yaƙin Iran a yankin kudancin ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images
Waɗanne ƙasashe ne za su fi shiga cikin tasku?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Binciken da masana daga cibiyar Vortexa suka yi ya nuna cewa Saudiyya tana fitar da ɗanyen mai kusan ganga miliyan 6 a kullum ta Hormuz - sama da duk wata ƙasa a yankin.
China da India da Japan da Koriya ta Kudu na cikin manyan ƙasashen da sufurin ɗanyen man fetur ta tekun.
EIA ta ƙiyasta cewa a 2022, kusan kashi 82 na ɗanyen man fetur da ake dakonsa ta mashigar, ƙasashen Asia ake zuwa da su.
A ranar 16 ga watan Afrilun 2025, kwana uku kafin Isra'ila ta kai hari kan tsaron sararin samaniyar Iran, kamfanin dillancin labaran Iran IRNA ya ruwaito shugaban Afirka ta Kudu Yoon Suk-yeol ya ce kashi 60 na man fetur ɗin ƙasar na biyowa ne ta mashigar Hormuz.
Haka kuma EIA ta ce Amurka na shigo da kusan ganga 700,000 na ɗanyen mai ta mashigar a kullum - kimanin kashi 11 na man da take shigo da shi, kuma kashi uku da man da take amfani da shi a ƙasar.
Ƙasashen turai baki ɗaya ba sa shigo da fetur da ya haura sama da ganga miliyan 1 a kullum.
Don haka, ƙasashen Larabawa da Asia ne za su fi fuskantar ƙalubale idan aka datse mashigar, sama da Amurka da turai da suke da alaƙar siyasa da Isra'ila.
Sannan akwai ƙasashen Asia da dama da suke da alaƙa mai kyau da Iran.
Rawar da China za ta taka

Asalin hoton, CFOTO / Future Publishing via Getty Images
China na cikin ƙasashen da suka fi amfani da man fetur da ake jigila ta Hormuz. Iran na sayar da mai a farashi mai rahusa, ƙasa da farashin kasuwannin duniya, wanda hakan ya sa ƙasar ke samun sauƙi kan takunkumin tattalin arziki da Amurka ta ƙaƙaba mata.
Saboda yadda take matuƙar amfani da man fetur, China ba za ta yi maraba da duk wani abu da zai jawo tashin farashin mai ba, ko kuma samun tsaiko a dakonsa. Wannan ya sa China za ta yi amfani da diflomasiyya wajen hana yiwuwar ɗaukar wannan matakin.

Asalin hoton, Chip Hires via Getty Images
Akwai wata hanya daban bayan tekun?
Saboda barazanar da ake yawan fuskanta ta datse mashigar a shekarun da suka gabata ne ya sa ƙasashen da suke dakon man fetur a yankin suka samar da wata hanyar daban.
Wani rahoton EIA ya ce Saudiyya ta fara amfani da bututun gabas maso yammaci mai nisan kilomita 1,200, wanda za a iya tura ganga miliyan 5 a kullum.
A shekarar 2019, Saudiyya ta gyara wasu bututun gas domin su yi ɗaukar ɗanyen man fetur.
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta haɗa gaɓar tekunta na tudu da gaɓar Fujairah da ke gaɓar Oma da bututun da zai iya ɗaukar gangan mai miliyan 1.5.
A watan Yulin 2021, Iran ta ƙaddamar da bututun Greh-Jask, wanda zai iya jigilar mai zuwa gaɓar Oman. Yanzu haka bututun zai iya ɗaukar ganga 350,000 a kullum.
Rahoton EIA ta ƙiyasta cewa waɗannan hanyoyin za su iya jigilar ganga miliyan 3.5 a kullum - kusan kashi 15 na man da ake jigila ta tekun a kullum.










