Me ƙasashen Afirka suka ce kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila?

Wasu shugabannin Afirka

Asalin hoton, Multiple

Lokacin karatu: Minti 5

Ƙasashen Afirka na ci gaba da yin martani kan yaƙin da ya ɓarke a Gabas ta Tsakiya tsakanin Amurka da Iran da kuma Isra'ila.

A ranar Asabar ne Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da hare-hare kan Iran bayan da Shugaban Amurka ya ce ya kasa gamsuwa da tattaunawa da wakilansa ke yi da Iran kan shirinta na nukiliya.

Hare-haren sun yi sanadin kisan jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei da wasu ƙusoshin gwamnatin ƙasar.

A nata ɓangare Iran ta mayar da martani ta hanyar ƙaddamar da hare-haren makamai masu linzami zuwa cikin Isra'ila da wasu sansanonin sojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya.

Rikicin ya haifar da martani daga ƙasashen duniya, ciki har da na Afirka, inda wasu suka riƙa kiraye-kirayen kai zuciya nesa.

A wannan muƙala mun duba martanin da wasu ƙasashen Afirka suka yi kan yaƙin.

Ƙungiyar AU

Ƙungiyar Haɗin kan Afirka ta AU ta yi kiran kai zuciya nesa a yaƙin da ta ce zai iya yin barazana ga zaman lafiyar duniya.

Cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Mahmoud Ali Youssouf ya fitar ya ce ricikin ka iya haifar da barazana ga fannin samar da abinci da makamashi da tattalin arziki da kuma matsalar jin ƙai da ƙaruwar rikice-rikice a wasu sassan duniya ciki har da nahiyar Afirka.

''Mun yi matuƙar kaɗuwa da hare-haren da aka kai wa Iran, waɗanda za su iya tayar da rikici a ilahirin yankin Gabas ta Tsakiya'', in ji shi.

Najeriya na son a yi taka-tsantsan

Shugaba Tinubu zaune a wurin taron

Asalin hoton, Bola Ahmed Tinubu

A nata ɓangare Najeriya- wadda ake yi wa kallon giwar Afirka - ta yi kiran gaggauta komawa kan teburin tattaunawa.

Cikin wani saƙo da ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta wallafa a shafinta na X, Najeriya ta yi gargaɗin cewa ci gaba da yaƙin zai haifar da tashin hankali a ilahirin yankin Gabas ta Tsakiya da ma duniya baki-ɗaya.

''Muna son a koma bin dokokin Majalisar Dinkin Duniya na taron Geneva, wanda ya martaba ƴancin da ke kare yankunan kowace ƙasa, ta hanyar warware matsaloli ta hanyar lalama'', in ji sanarwar.

Najeriya ta kuma yi kiran rage amfani da ƙarfi saboda kare rayukan fararen hula da kauce wa duk wani mataki da zai iya karya ƙa'idojin da dokokin duniya.

Masar ta gargaɗi Iran

Abdel Fattah al-Sisi

Asalin hoton, Getty Images

Shugaban ƙasar Masar, Abdel Fattah al-Sisi ya yi gargaɗin cewa hare-haren makamai masu linzami da Iran ke kai wa cikin wasu ƙasashen Larabawa na barazana da zaman lafiyar Gabas ta Tsakiya.

Rahotonni sun ambato cewa Shugaba Sisi ya yi waya da shugabannin ƙasashen Haɗaɗɗɗiyar Daular Larabawa da Jordan da Qatar da Saudiyya da Bahrain, bayan da Iran ta kai wa sansanonin sojin Amurka hari a ƙasashen.

Kakakin shugaban ƙasar, Mohamed El-Shennawy, ya ce Shugaba Sisi ya yi Allah wadai da ƙeta alfarmar ƙasashen Larabawa yana mai cewa tsaron waɗannan ƙasashe musamman Saudiyya na da matuƙar muhimmanci ga ilahirin ƙasashen Larabawa.

Afirka ta Kudu ta buƙaci a tsayar da yaƙin

Cyril Ramaphosa

Asalin hoton, Getty Images

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya buƙaci ''duka ɓangarorin da ke yaƙi da juna su mutunta dokokin duniya ta hanyar dakatar da yaƙin.

Cikin wata sanarwa da ya fitar game da yaƙin, Mista Ramaphosa bai ambaci Amurka ko Isra'ila ko ma Iran ba, sai dai ya ce rikicin na yin barazana ga zaman lafiyar duniya.

''Wannan yaƙi na haifar da mummunar barazana ga zaman lafiyar yankin da ma duniya baki ɗaya, wanda zai iya yin illa ga ayyukan jin ƙai da hulɗar diflomasiyya da ma tattalin arziki'', kamar yadda ya bayyana.

Chadi na tare da Iran

Mahamat Idriss Deby Itno

Asalin hoton, Mahamat Idriss Deby Itno/FB

Shi ma shugaban ƙasar Chadi, Mahamat Idriss Deby Itno a ranar Lahadi ya aike saƙon ta'aziyya ga gwamnati da al'ummar Iran bayan kisan jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei a hare-haren Amurka da Isra'ila.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ya bayyana labarin mutuwar Khamenei a matsayin ''abin baƙin ciki''.

''Chadi na son zaman lafiyar duniya, kuma tana jajanta wa al'ummar Iran cikin wannan yanayi mai muni'', kamar yadda ya wallafa.

Kenya ta soki Iran kan mayar da martani

William Ruto

Asalin hoton, Getty Images

Shugaban ƙasar Kenya, William Ruto ya yi gargaɗin cewa faɗaɗa rikicin zuwa duka yankin Gabas ta Tsakiya ka iya yin barazana ga zaman lafiya da tsaron duniya.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Mista Ruto ya ce Nairobi ta yi Allah wadai da hare-haren ramuwar gayya da Iran ta ƙaddamar a ƙasashen Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Saudiyya da Qatar da Iraƙi da Oman da Kuwait da Jordan da kuma Bahrain.

Ya ƙara da cewa faɗaɗa yaƙin zuwa sauran ƙasashen yankin zai haifar da barazana ga tsaron lafiyar duniya.

Mista Ruto ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki na duniya su tattauna domin kawo ƙarshen yaƙin.

Ghana na son a dakatar da yaƙin

John Dramani Mahama

Asalin hoton, John Dramani Mahama

Ita ma ƙasar Ghana ta fitar da sanarwar kiran dakatar da yaƙin.

Cikin wata sanar da ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta fitar, ta yi kiran gaggauta dakatar dayaƙin, tana mai gargaɗin cewa ci gaba da yaƙin zai haifar da illa mai yawa ga fararen hula da tattalin arzikin duniya.

Don haka ne hukumomin ƙasar suka shawarci ƴan ƙasar mazauna yankin Gabas ta Tsakiya su kauce wa tafiye-tafiyen da ba su zama wajibi ba

''Muna shawartarku da zama a gida, tare da kauce wa shiga taron ɗimbin jama'a sannan ku riƙa tuntuɓar ofisoshin jakadancin Ghana a ƙasashen da kuke'', in ji sanarwar.

Sauran ƙasashe

Akwai dai sauran ƙasashen yankin da dama da suka yi kiran dakatar da rikicin ta hanyar bin sulhu.

Ƙasashen da suka yi irin wannan kiraye-kirayen sun haɗa da Senegal da Libya da Aljeriya.

Galibi dai ƙasashen Afirka kan zaiyarci yankin Gabas ta Tsakiya, wataƙila saboda addini ko neman ayyukan ƙwadogo.