Yadda Amurka da Isra'ila suka kwashe watanni suna kitsa kashe Ayatollah Khamenei

Hoton marigayi jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei a gefe guda kuma tutar ƙasar ce. An ajiye su ne a wani masallaci a birnin Cape Town, inda ake zuwa domin ta'aziyya.

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Gordon Corera
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Security analyst
  • Lokacin karatu: Minti 5

Kisan da aka yi wa Jagoran Addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya faru ne da safe, ba da tsakar dare ba, kamar yadda wasu za su yi tsammani.

Hakan ya faru ne saboda Amurka da Isra'ila sun yi amfani da wani bayanin sirri da ya zo musu ƴan awanni kafin lokacin.

Tsawon watanni, Amurka da Isra'ila sun riƙa dakon lokacin da manyan jagororin Iran za su haɗu wuri ɗaya, daga nan sai suka fahimci cewa Khamenei zai halarci wani gida a tsakiyan birnin Tehran da safiyar ranar Asabar.

Haka nan kuma sun gano wani wurin da manyan sojoji da jami'an tattara bayanan sirri suke yin wata ganawa a daidai wannan lokacin.

Tsawon watanni, Amurka da Isra'ila sun riƙa bibiyar duk wani motsi na jagoran addinin na Iran.

Hanyar da suka yi hakan abu ne na sirri, duk da dai shugaban Amurka Donald Trump ya ɗan bayar da satar amsa a bayanin da ya wallafa a shafin sada zumunta.

"Ya gaza zulle wa bayananmu na sirri da kuma nagartaccen tsarin bibiyar da muka yi amfani da shi."

Wannan zai iya zama mutum ne ke ba su bayanai ko kuma wata fasaha ta bibiyar jami'an Iran.

Shugaba Donald Trump a zaune sanye da farar hana-sallah mai ɗauke da rubutun USA, yana sauraron bayanin yadda ake aiwatar da harin da Amurka ta kai Iran.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Trump da tawagarsa sun bibiyi duk abubuwan da ke faruwa daga wani ɗakin ƙaddamar da yaƙi da aka samar a gidansa na Mar a Lago
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A yaƙin kwana 12 da aka yi da Irana watan Yunin bara, Isra'ila ta kai hari ne kan masana kimiyyar Iran masu alaƙa da shirin nukiliyar ƙasar, kuma an ruwaito cewa sun yi amfani da kutse a hanyar sadarwar waya da kuma wayoyin salular mutane domin bibiyar duk wani motsi nasu.

Wannan a wasu lokutan ya ƙunshi bibiyar dogaran da ke tsaron irin waɗannan jami'ai.

Idan aka yi haka a tsawon lokaci za a iya gane "tsarin yadda mutum ke tafiyar da rayuwarsa", ta haka za a iya kintatar lokacin da mutum yake a wurin da za a iya saurin samun shi.

Iran ta san cewa maƙiyanta na bibiyar jagoran addinin ƙasar, saboda haka gazawar da aka yi wajen ganowa da magance irin waɗannan lokuta da za a fi sauƙin samun shi a waɗannan watanni mau wahala, ya nuna wata gagarumar gazawa a tsarin tsaron ƙasar da kuma tattara bayanan sirri, ko kuma ya nuna yadda Amurka da Iran suna iya bin duk wata hanya wajen ganin sun ci gaba da bibiyar shi ta kowane hali.

Wataƙila gwamnatin Iran ta yi tunanin cewa zai yi wahala a kai mata hari cikin hasken rana.

A wannan karo, jaridar New York Times ta ce hukumar leƙen asiri ta Amurka (CIA) ce ta tattaro bayanan sirrin, daga nan sai ta tura wa Isra'ila domin ta ƙaddamar da harin.

Bayanai sun nuna cewa an raba aikin ne tsakanin Amurka da Isra'ila, inda Isra'ila ta ɗauki aikin kai hari kan shugabannin Iran, ita kuma Amurka ta ɗauki aikin kai hari kan cibiyoyin sojin Iran.

Abu mai muhimmanci shi ne an tattara bayanan sirri da wuri sosai game da duk wani motsin jagoran addini na Iran da kuma manyan jagororin ƙasar ta yadda aka samu isasshen lokacin tsara kai musu hari ta amfani da jiragen yaƙi masu jefa makamai masu cin dogon zango.

An yi ƙoƙarin cin gajiyar damar da aka samu ne, a matsayin alamar mafarin wasu jerin hare-hare domin cimma manufa.

Jiragen yaƙin Isra'ila za su iya ɗaukan kimanin awa biyu kafin su isa birnin Tehran, amma babu masaniya game da tazarar da suke da ita da birnin daga inda suka jefa makaman.

Lokacin da aka yanke shawarar ƙaddamar da harin, jiragen yaƙin sojin Isra'ila sun yi amfani da bama-bamai 30 domin yin luguden wuta a gidan da Ayatollah yake da misalin ƙarfe 9:40 agogon Iran.

Kalli abubuwan da ke faruwa
Bayanan bidiyo, Bidiyo ya nuna yadda hayaƙi ya turnuƙe bayan kai harin

Wataƙila an yi hakan ne kasancewar jagoran addinin na Iran na amfani da wani wurin ɓoyo na ƙarƙashin ƙasa domin kariya (duk da cewa wannan ba shi ne wurin ɓoyo mafi zurfi da gwamnatin ƙasar ke da shi ba).

Saboda haka ana buƙatar isassun bamabamai domin a tabbatar cewa an same shi a can ƙarƙashin ƙasa.

Haka nan an jefa bamabamai a wasu wauraren a birnin Tehran, ciki har da ofishin shugaban ƙasar Masoud Pezeshkian, wanda daga baya ya fitar da sanarwar cewa yana nan cikin ƙoshin lafiya.

Isra'ila ta bayyana sunayen manyan jami'an tsaron Iran bakwai cikin waɗanda ta hallaka, ciki har da sakataren Majalisar Tsaro ta Iran Ali Shamkhani, da ministan tsaron ƙasar Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh da kwamandan rundunar sojin juyin juya halin ƙasar Janar Mohammad Pakpour.

Lokacin da jiragen suka ƙaddamar da hare-haren, tsakar dare ne a gidan Donald Trump na Mar-a-Logo da ke jihar Florida, inda Trump da tawagarsa suke zaune suna bibiyar abin da ke faruwa.

An ɗauki tsawon awanni kafin tabbaci ya zo cewa an kashe Ayatollah.

Dama Iran ta shirya wa zuwan wannan lokaci, inda rahotanni suka ce an riga an tsara wanda zai gaji Khamenei da kuma da dama daga cikin manyan jagororn ƙasar.

Saboda haka har yanzu babu tabbas kan tasirin da kisan Khamenei da jagororin tsaron ƙasar zai yi ga wannan rikici.

Wuraren da aka ƙaddamar da hari a birnin Tehran
Bayanan hoto, Wuraren da aka ƙaddamar da hari a birnin Tehran