Abin da ya sa na amince na yi wa Peter Obi mataimaki - Kwankwaso

Asalin hoton, Saifullahi Hassan/FB
Jagoran Kwankwasiyyar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce shi da mabiyansa sun zaɓi shiga sabuwar jam'iyar NDC ne domin gujewa fuskantar matsala a haɗakar ADC.
Cikin wata hira da tsohon gwamnan na jihar Kano ya yi da gidan talbijin na AriseTV, ranar Litinin ya ce a yanzu ƴan Najeriya sun daina la'akari da yankin da ɗan takara ya fito ko ƙabila da addininsa.
Ya ce abin da ƴan ƙasar suke buƙata shi ne mutumin da zai fitar musu kitse daga wuta.
Cikin hirar wadda ta kai kusan sa'a ɗaya, BBC ta yi tsakure na wasu muhimman bututuwa guda biyar da suka fi ɗaukar hankali a ciki:
'Abin da ya sa na yarda na yi wa Obi mataimaki'
Sanata Kwankwaso ya ce ya amince ya yi wa Peter Obi mataimaki ne domin samar wa ƴan Najeriya masalaha daga abin da ya kira halin da ƙasar ke ciki.
''Idan za mu faɗa wa kanmu gaskiya a yanzu a ƙasar ba wanda ba ya ji a jikinsa, duk wanda ka samu akwai matsalar da ke damunsa game da wannan gwamnati, kama daga matsalar tsaro zuwa na tattalin arziki da ababen more rayuwa''.
''Don haka ne yanzu mutane ba su addini ko ƙabilar wanda zai jagorance su ba, abin da ke gabansu yanzu shi ne wane ne zai fitar da su daga halin da suke ciki'', in ji tsohon gwamnan na jihar Kano.
Kwankwaso ya ce zaɓen 2027 na daban ne, ba tsakanin jam'iyyu ba ne, zaɓe tsakanin ƴan Najeriya da waɗanda ya kira 'shugabanni'.
Ya kuma ƙara da cewa a halin yanzu ba ya tunanin akwai wata haɗakar ɗantakarar shugaban ƙasa da mataimaki da za ta fi Peter Obi da Kwankwaso.
'Abin da ya sa na amince a kai takara Kudu'

Asalin hoton, Saifullahi Hassan/FB
Kwankwaso ya ce tun da farko sun zauna sun tattauna batutuwa da dama game da sabuwar jam'iyar NDC, ciki har da batun mayar da takarar shugabancin ƙasa zuwa kudancin ƙasar na shekarar huɗu daga nan a mayar da shi arewa.
Ya ce mutane da dama na muhawara kan inda ya kamata NDC ta miƙa takarar shugabancin ƙasarta.
''Amma daga ƙarshen mun yanke a mayar da shi kudancin ƙasar saboda a halin da muke ciki yanzu, nan ne ya kamata a miƙa takarar'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Kwankwaso ya ci gaba da cewa a yanzu ba batun wane yanki ne zai yi shugabancin Najeriya ba ne.
''Batu ne na samun shugabancin nagari, ba wai yankin da shugaban zai fito ba, muna buƙatar mutanen da za su fitar da ƙasar nan daga halin da take ciki da ciyar da ita gaba'', kamar yadda ya bayyana.
'Za mu iya yin aiki da ADC gabanin zaɓen 2027'

Asalin hoton, Saifullahi Hassan/FB
Masu lura da al'amuran siyasa a Najeriya na ganin ficewar Kwankwaso da Peter Obi daga ADC zuwa NDC, tamkar karya logon hamayyar ƙasar ne.
Sai dai kwankwason ya ce akwai yiwuwar jam'iyyun biyu su yi aiki tare gabanin zaɓen 2027 da ke tafe.
''Ni kai da Peter Obi mun bar ADC ne ba don muna faɗa da Atiku ko wani a cikin ADC ba'', kamar yadda ya bayyana.
Ya ci gaba da cewa ya bar ADC ne saboda wasu dalilai, waɗanda zai yi wahala su bai wa ADC damar tsayar da ɗantakara a zaɓen 2027.
''A yanzu haka akwai matsaloli uku da suka dabaibaye ADC, waɗanda kuma idan ba a magance su da wahala jam'iyyar ta iya tsayar da ɗantakara'', in ji jagoran na Kwankwasiya.
'Ba abin da muka amfana a gwamnatin Buhari'

Asalin hoton, Presidency
Jagoran Kwankwasiyyar ya kuma koka kan abin da ya ce rashin amfana da mulkin tsohuwar gwamnatin Buhari, duk da gagarumar gudunmowar da ya ce ya bayar wajen kafuwar gwamnatin.
''Ni kan kaina na yi namijin ƙoƙari a zaɓen gwamnatin, mun samar da ƙuri'a kusan miliyan biyu, amma a matsayinmu na ƴansiyasa ba a nuna mana an ji daɗin abin da muka yi ba'', in ji shi.
Ya ci gaba da cewa duk da jefa rayukansu cikin hatsari da suka yi a lokacin yaƙin neman zaɓe, ba su ga amfanin hakan a ɗaiɗaikunsu ko a yankin da suke wakilta ba.
A zaɓen 2015, wanda marigayi Muhammadu Buhari ya lashe zaɓe, Kwankwaso na jam'iyyar APC, kuma shi ne ma gwamnan Kano a lokacin, kodayake daga baya ya fita daga jam'iyyar zuwa PDP.
Kwankwaso ya ce sun shiga sabuwar jam'iyyar NDC ne da nufin kawo sauyi a gwamnatin ƙasar, ya kuma ce jam'iyyar tasu na ci gaba da samun karɓuwa.
'Tinubu da gwamnoni sun dogara da juna don cin zaɓe'

Asalin hoton, Kwankwaso/X
Yayin da jam'iyyar APC ke ci gaba da mulki a da jihohin ƙasar 30, lamarin da ya da sa wasu ke ganin APC ta kama hanyar lashe zaɓen 2027, Kwankwaso ya ce yawan gwamnonin ba zai amfanar mata komai ba.
''Duk da yawan waɗannan gwamnonin da jam'iyyar ke da shi, sun dogara ne da Tinubu domin cin zaɓukansu, haka shi ma Tinubun da su ya dogara da su domin cin zaɓensa'', in ji shi.
Sai dai ya ce gwamnonin ba za su iya kawo wa Tinubun ƙuri'un jihohinsu ba, saboda tarin kura-kuran da suka tafka a jihohin nasu.
''Idan kana gwamnati, ka yi ƙoƙarin ɗaukar mutane masu ƙima daga yankuna daban-daban, domin su ne wakilanka a yankin'', in ji shi.









