Sai Abba ya yi da na sanin barin mu - Kwankwaso

Kwankwaso samye da fararen tufafi da jar hula da kuma baƙin tabarau

Asalin hoton, Kwankwaso/x

Lokacin karatu: Minti 3

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma jagoran jam'iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce yana da yaƙinin cewa sai gwamnan Kano Abba Kabir da muƙarrabansa sun yi da na sanin fita daga jam'iyyar NNPP da suka yi.

Sanata Kwankwaso ya ce fitar gwamna Abba daga jam'iyyar NNPP ta zo da mamaki ga mutane da dama, kuma shi da kansa jin abin yake kamar a mafarki.

''Da yawa mutane ina da labarin, gani suke ma kamar wani tsari ne, da ni da shi, ko da ni da su. Nima sau da yawa ba na yarda cewar abubuwab da suke faruwa haka su ke.'' in ji Kwankwaso.

A ranar Litinin 26 ga watan Janairun 2026 gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya komawa jam'iyyar APC a hukumance, bayan sanar da ficewar sa daga NNPP a ranar Juma'a 23 ga watan Janairun 2023, ƙasa da shekara uku bayan cin zaɓen gwamnan Kano a cikin ta.

A wajen bikin komawarsa APC, gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce ya ɗauki matakin sauya sheƙar bisa la'akari da inda aka dosa a siyasar Najeriya da kuma buƙatar bin hanyar da za ta kawo ci gaba ga jama'ar Kano baki ɗaya.

Ya kuma ce sai da ya yi tuntuɓa a tsakanin abokan tafiyar shi a siyasance da sauran masu ruwa da tsaki kafin yanke hukuncin sauya shekar.

Amma a hirar ta farko da kafafen yaɗa labarai tun bayan raba gari da gwamna Abba Kabir, Sanata Kwankwaso ya shaidawa BBC cewa akwai takaici yadda gwamna Abba Kabir ''ya ɗauki haƙƙin ƴan jam'iyar NNPP da kuma jama'ar Kano ya miƙa ga tafiyar Gandujiyya'' ba tare da wata ƙwaƙƙwarar hujja ba.

Sanata Kwankwaso ya ce ''Ni kaina in na kwanta sai in waiwaya in ce me ya faru? waye ya yi laifi? Ni ne na yi laifi? jam'iyya ce ta yi laifi? ƴan jam'iyya ne suka yi laifi? na kasa samun amsa.''

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Jagoran jam'iyyar NNPP ya ce a ganin shi dukkan abubuwan da gwamnan ya faɗa mashi da kuma waɗanda ya tura a faɗa mashi game da dalilan sauya sheƙar, abubuwa ne da ba su wuce a gyara domin tafiya tare ba.

Ya kuma yi watsi da rikicin cikin gida na NNPP da gwamnan jihar Kano ya kafa hujja da shi wajen ficewa daga jam'iyyar, inda ya ce ai dama babu wata jam'iyya da ta rabauta da masu ƙorafi.

''Ina tabbatar maki a iya sani na babu wata jam'iyya da ta fi NNPP zaman lafiya da kwanciyar hankali, in kuma da shi, ki bari su yi wannan congres da convention, ai shi ne za ki ga rigima,'' in ji Kwankwaso.

Da kuma ya ke tsokaci kan yadda wasu da suka fice NNPP, kuma suke iƙirarin ci gaba da zama da aƙidar jar hula ta kwankwasiyya, sai Sanata Kwankwaso ya ce ''Magana ce an riga an gina haske, an gina duhu a Kano, idan za ka je ka yi Kwankwasiyya wa ya ce ka fita daga Kwankasiyyar? Ka tsaya mana ka yi Kwankwasiyyar a inda ta ke.''

Ya ƙara da cewa tun daga yadda tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya zamo wanda ya karɓi gwamna Abba Kabir zuwa cikin APC, har ya ɗaga mashi hannu, alama ce cewa ''Ya riga ya faɗi zaɓe,''

''Da Ganduje yana da hannun ɗagawa, da 2019 ya ɗaga, da Gandujen yana da hannun ɗagawa da ya ɗaga 2023,'' in ji Sanata Kwankwaso.

Ya jaddada cewa yana da tabbacin cewa zaman ƙunci gwamna Abba da maƙarrabansa za su yi a APC kuma nan gaba ''idan ma bai dawo ba, zai yi da na sani.''

Sanata Kwankwaso ya kuma bayyana makomar tafiyar Kwankwasiyya inda ya ce har yanzu Kano tana hannun NNPP, kuma tuni sun fara neman hanyar da za su haɗa kai domin ceto Najeriya baki ɗaya daga halin da ta ke ciki.

Wane muhimmanci Kwankwaso yake da shi a siyasa?

Tsohon gwamnan jihar Kanon, Rabi'u Musa Kwankwaso na ɗaya daga cikin ƴan siyasa a arewacin Najeriya da suka daɗe suna jan zarensu kuma suka shiga cikin zuciyar matasa.

Masana na cewa tun bayan Malam Aminu Kano ba a sake samun wani ɗan siyasa ba da ya fito da wani tsari na siyasa da ya sa wa suna wanda kuma yake da mabiya na ga-ni-kashe-ni, sai tsohon gwamnan na Kano wanda ya samar da aƙidar siyasa mai suna Kwankwasiyya da mabiyanta ke saka jar hula.

Sannan kuma Rabi'u Musa Kwankwaso shi ne gwamnan da bayan ya faɗi a ƙoƙarin neman wa'adi na biyu ya sake komawa kujerar bayan shekaru huɗu, inda ya kayar da ɗantakarar gwamna mai barin gado na lokacin.

Har ila yau, Kwankwaso ya tsayar da gwamnan Kano mai-ci, Abba Kabir Yusuf inda ya kayar da ɗantakarar gwamna mai barin gado, Nasiru Yusuf Gawuna.

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar NNPP a 2023, inda ya samu kuri'u fiye da 900,000 a jihar Kano, wadda ta fi yawan ƙuri'ar da kowanne daga sauran ƴan takarar jam'iyyun suka samu a jiha ɗaya tilo, ciki kuwa har da jam'iyya mai mulki ta APC.