Larabawan da suka ɗauki kasadar ceton Yahudawa lokacin kisan kiyashi

Asalin hoton, Family handout
- Marubuci, Swaminathan Natarajan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 6
An karrama mutum 28,000 waɗanda ba Yahudawa ba saboda ɗaukar kasada na ceto rayukan Yahudawa lokacin kisan kiyashi na Holocaust - sai dai duk da cewa an kashe dubban mutane lokacin da ƴan Nazi suka mamaye Arewacin Afirka, babu Balarabe ɗaya da aka taɓa karramawa saboda ceto ran Bayahude a ƙasar Larabawa.
"Wani Balarabe mai sana'ar gasa biredi a Tunisiya ya kasance yana barin ƙarin biredi a shagonsa a kowace rana - domin bai wa Yahudawan da ba su da ƙarfi."
"Matan Larabawa na ɗaukar ƴaƴan Yahudawa zuwa gidajensu domin kula da su - saboda babu abinci ko kuma madara."
"A Algiers, an hana Musulmai ɗaukar kayan Yahudawa da aka ƙwace - kuma babu Balaraben da ya tsallake wannan umarni."
Waɗannan na cikin labaran da Dakta Rob Satloff, babban darektan wata cibiya a Washington ya tattara, na yadda ƴan Arewacin Afirka ke taimakon Yahudawa lokacin yaƙin duniya na biyu.
Ƴan Nazi sun kashe sama da Yahudawa miliyan shida a Turai, sai dai sun kuma gallazawa al'ummomin Yahudawa da ke arewacin Afirka, wanda ya samu goyon baya daga shugabancin Vichy, abin da ya janyo kashe-kashe, ɗaiɗaitawa da kuma lalata kayakin Yahudawa da dama.
"Duk abin da ya faru da Yahudawa a Turai ya faru da Yahudawa a ƙasashen Larabawa," kamar yadda Satloff ya shaida wa BBC.
A cewar cibiyar tunawa da kisan kiyashin Yahudawa da ke Amurka, kusan Yahudawa rabin miliyan ne ke rayuwa a ƙasashen Moroko, Aljeriya, Tunisiya da kuma Libya. Kuma Satloff ya yi kiyasin cewa waɗanda aka kashe zai iya kai wa tsakanin 4,000 zuwa 5,000.

Asalin hoton, Rob Satloff
Ɗaukar babbar kasada
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Akwai wasu Larabawa uku da suka cancanci lambar yabo a wajen tunawa da kisan kiyashin Yahudawa, a cewar Yad Vashem.
A Tunisiya, ƙasar da ƴan Nazi suka mamaye baki ɗaya a arewacin Afirka - daga Nuwambar 1942 zuwa Mayun 1943 - an tilasta wa Yahudawa saka abubuwa da ke taurari masu alamar ruwan ɗorawa.
Sai dai lokacin ƴan Nazi suka buƙaci dukkan Yahudawa su fito don tilasta musu aiki, ɗaya daga cikinsu mai suna Joseph Naccache ya tsere.
Gomman shekaru bayan nan, ya faɗa wa Satloff a Paris yadda wani Balarabe ya ɗauki kasadar ba shi mafaka.
"Sojojin Nazi sun yi ta yaɗa labarai kan matasan Yahudawa, a watan Disambar 1942," a cewar Satloff. "
Idan aka kama wani yana bai wa mutumin da sojojin ke nema, wannan babban laifi ne.
"Naccache ya tsere daga neman da ake yi masa, inda yake ƙoƙarin ganin ƴan Jamus ɗin ba su tafi da shi ba, inda ya kare da komawa wani gidan wanka."
Mai gidan wankar, Hamza Abdul Jalil, ya faɗa wa Naccache cewa zai kare shi ta hanyar ɓoye shi a wurinsa.
"Ba wanda aka tseratar kaɗai na samu gani ba, na samu damar komawa Tunis kuma na samu gidan wankar da kuma ɗan mutumin da ya ceci Naccache," kamar yadda Satloff ya faɗa wa BBC. "Yana da dukkan bayanai. Labari ne mara daɗi kuma na same shi daga dukkan ɓangarori."
Tsohon magajin garin Tunis, Si Ali Sakkat, shi ma ya ɗauki kasada domin samar da abinci da kuma mafaka ga Yahudawan da suka tserewa azabtarwa, a garin mahaifarsa da ke tsaunin Zaghouan, mai nisan kilomita 55 daga babban birnin ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images
'Yin fito na fito da barazana'
Sai dai, ɗaya daga cikin labaran Satloff shi ne Khaled Abdul-Wahab, wanda ya jiyo wani sojan Nazi na cewa ya mayar da hankalinsa kan wata Bayahudiya a Tunisiya.
Da tsakiyar dare, Abdul-Wahab ya tseratar da matar da iyalanta, waɗanda ke cikin ɓuya, ya ɗauke su zuwa gonarsa mai nisan kilomita 30 daga Tunis, inda ya ɓoye su.
Sai dai wannan shi ne mafarin - kafin mamayar Nazi ta kawo karshe, ya ɓoye mata 20 da kuma yara, bayan da aka tilasta wa mazajensu zuwa aikin dole.
Uku daga cikin matan sun buƙaci cibiyar Yad Vashem da ta karrama Abdul-Wahab - sai dai an yi watsi da buƙatar har sau biyu.
Mutumin "kirki" ne, a cewar cibiyar, kuma labarin da aka bayar na abin da ya yi ya nuna dattako, sai dai bai wa Yahudawa mafaka yana bisa ka'ida kuma sun zauna cikin gonar Abdul-Wahaba tare da sanin ƴan Nazi, abin da ya sa bai cancanci karramawar ba da ake bai wa mutanen da suka sayar da ransu wajen ceto Yahudawa daga kashe-kashen ƴan Nazi lokacin kisan kiyashi.
"Saboda mamayar Nazi a Tunisiya ta ɗauki akalla watanni shida, hakan bai kai ga daɓɓaka tsarin son kawo karshen Yahudawa ba," in ji cibiyar Yad Vashem.
A watan Dismabar 2011, Eva Weisel, wadda Abdul-Wahab ya bai wa mafaka tana shekara 13, ta rubuta wani littafi a jaridar New York Times, inda ta nuna fushinta kan kin karrama shi.
"Na san cewa ina iya rayuwa saboda Abdul-Wahab ya yi fito na fito da marasa imani wajen ceto rayuwata, kamar yadda ya tseratar da sauran iyalaina," in ji ta. "Ina fatan cibiyar Yad Vashem za ta sake duba batun kafin a ce babu wanda ya rage da zai bayar da labari."

Asalin hoton, Getty Images
'Labaran da suka fi dacewa'
Cikin sama da mutum 28,000 da aka bai wa lambar girmamawa saboda tseratar da Yahudawa lokacin kisan kiyashi, mutum 70 cikinsu sun kasance Musulmai amma ɗaya ne Balarabe, wani likita a ƙasar Masar Mohamed Helmy, wanda ya ɓoye wata Bayahudiya da kuma taimakawa iyalanta a Berlin.
Yayin da labaran Satloff suka kasance masu ƙarfi, Dakta Mehnaz Afridi, darekta a Jami'ar Manhattan a Amurka, ya ce suna duba labaran da suka fi dacewa.
Afridi ta faɗa wa BBC cewa: "Ga wasu da ke Isra'ila, karramawa Larabawa da suak ceci Yahudawa yana da tsarkakiya a siyasance. Ga wasu kuma a ƙasashen Larabawa, bayyana cewa Yahudawa na son ceto daga ƴan Nazi a ƙasashen Larabawa yana saka shakku kan kisan kiyashin."

Asalin hoton, Getty Images
'Gabatowar kisan kiyashi'
Afridi ita da kanta tana kira don ganin an karrama sarkin Moroko.
"Lokacin gwamnatin Vichy na ƴan Nazi, an umarci Moroko da ƴan birnin Tangiers cewa su tursasa Yahudawa fita zuwa sansanin tara masu aikin tilas.
Sarkin Moroko, Mohammed V, ya yi watsi da buƙatar aiwatar da dokokin haramta wariya ga Yahudawa ko kuma tura Yahudawan Moroko zuwa Faransa," in ji ta.
A shafin intanet na cibiyar Yad Vashem, Jackie Metzger, daga makarantar nazarin kisan kiyashin Yahudawa, wadda ta daɗe da yin ritaya, ta rubuta cewa: "Idan kisan kiyashi na nufin ɗaruruwan kashe-kashe, to hakan bai faru a arewacin Afirka ba.
Ya kamata tarihin Yahudawa a wannan lokaci ya yi maganar cewa an kusa afkawa cikin kisan kiyashi, amma ba a kai ga haka ba.
Sai dai a wani martani da cibiyar ta mayar, ta ce "Arewacin Afirka na cikin ɓangaren kisan kiyashi na Yahudawa."
"Ƴan Nazi sun yi niyyar aikata wa Yahudawan Afirka da na Falasɗinawa da kuma Gabas Ta Tsakiya abin da suka yi a Turai," a cewar cibiyar.

Asalin hoton, Getty Images
Ana yin muhawara sosai kan kowane irin labari da ake son karramawa, ba tare da nuna bambanci ba, in ji cibiyar, sai dai kwamitin tantancewa na cibiyar ba ya duba "batun karrama Yahudawa da suka yi ceto ba" saboda babu buƙatar hakan daga wani wuri yanzu.
Labarai irin na Abdul-Wahab na ci gaba da samun karɓuwa, in ji Afridi. "A 2009 an shuka wata cibiya don karrama shi a Wahington da kuma birnin Milan, inda aka yi wnai biki a gaban ƴarsa, Faiza," a cewar Afridi.
Satloff ya ce: "Ina alfaharin cewa ƙungiyoyi da kuma hukumomi da dama a arewacin Afirka da kuma Turai na karrama jajircewa da kuma namijin koƙarin waɗannan Larabawa da suka tashi tsaye don kare Yahudawa a wancan lokaci," in ji shi.
Kuma ganin cewa hujjoji na ƙara fitowa, Satloff na fatan cewa akwai ƙarin damarmaki na girmama waɗannan mutane a nan gaba.






