Wace dabara Carrick ke amfani da ita wajen samun nasara a United?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Simon Stone
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Manchester United reporter
- Lokacin karatu: Minti 5
Michael Carrick na da ƙwarewar da ba za ta sa ya shagaltu ba kan cewa ko yana son zama kocin Manchester United na dindin.
Yana cike da farin ciki lokacin da ya bayana cewa ƴayansa sun halarci wasan ƙungiyarsa da Arsenal a Emirates ranar Lahadi, inda suka shiga sahun dubban magoya baya da suka ɓarke da murna lokacin da Matheus Cunha ya ci kwallon da ya bai wa United nasara da ci 3-2, kuma nasararsu ta farko kenan a gidan Arsenal cikin shekara takwas.
An nuna mai ƙaramin hannun jari a Manchester United Sir Jim Ratcliffe cikin annashuwa lokacin da aka haska shi a Emirates. Babu lokuta da dama na yin murmushi sama da shekara biyu da ya sayi hannun jari a ƙungiyar ganin irin rashin kataɓus da suke yi.
Michael Carrick ya samu nasarar lashe wasanninsa na biyu tun fara jagoranci a United. Abu ne da Ruben Amorim ya taɓa samu sau ɗaya cikin watanni 14 da ya yi a ƙungiyar - lokacin da ya samu nasarar wasanni uku a jere a farkon fara wannan kaka, abin da ya sa ya samu kyautar kocin da a fi kwazo na watan Oktoba.
United ta samu maki shida karkashin Carrick. Amorim kuwa ya shafe wasanni biyar kafin ya samu haka - inda daga nan ya yi rashin nasara a wasanni uku da suka bi baya.
Makonni shida da suka wuce, babu wanda zai zaɓi Carrick a matsayin kocin United na gaba a kan kocin Crystal Palace, Oliver Glasner.
Amma yanzu fa?
'Aikina zan yi... ba zan bar wani abu ya shagaltar da ni ba'

Asalin hoton, Getty Images
Akwai muryoyi da dama da suka gargaɗi United kan maimaita abin da ya faru a kakar 2018-19.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kakar wasanni bakwai da suka wuce, aka naɗa Ole Gunnar Solksjaer a matsayin kocin riko, ya lashe wasanni takwas a jere, sai kuma wasanni shida cikin tara da suka bi baya ya samu gagarumar nasara a hannun Paris sT-Germain a gasar zakarun Turai, lokacin da United ta farfaɗo daga kwallon biyu da PSG ta Parc des Princes - daga nan aka ba shi aikin kocin ƙungiyar na dindindin.
Solskjaer ya jagoranci Man United zuwa wasan karshe na gasar Europa a 2021, inda Villareal ta doke ta a bugun fenariti.
Sai dai samun nasarar wasanni na iya juyawa cikin gaggawa kamar yadda ra'ayoyi suka bayyana - duk da cewa Carrick bai nuna alamun za a ci United da sauki ba a yanzu.
Carrick tare da ƴan wasansa sun nuna farin ciki kan irin nasarar da suka samu a kan Man City da kuma Arsenal.
Kocin Man United ɗin na riƙo ya yi wani irin tsalle a sama lokacin da Cunha ya ci kwallon da ta bai wa ƙungiyarsa nasara a minti na 87.
Amma wa zai ga laifinsa?
"Dole ne ka yi murna, saboda irin jajircewa da kuma ƙwarin gwiwa da ƴan wasa suka nuna," in ji Carrick. "Amma ya kamata mu kaskantar da kai da sanin abin da muke yi da kuma kallon yada muka sami nasara a waɗannan wasanni biyu.
"Ba za mu yi kallo da nisa ba. Ba za mu saka wani babban buri ba saboda yin haka zai dawo ya yi mana illa."
"Na zo nan ne don yin aiki," in ji shi. "Lokacin da na zo nan makonni biyu da suka wuce, na ce dole sai mun yi nazari sosai kan duk matakin da za mu ɗauka.
"Ba za mu bar wani abu ya shagaltar da mu ba. Manyan sakamako ne masu kyau, sai dai za mu ci gaba da jajircewa.
"Ina jin daɗin abin da muke yi kuma zan ci gaba da yin abin da zan iya."

Asalin hoton, Getty Images
Carrick ya kawo sauyi na wasu matsaloli da aka samu lokacin Amorim - inda ya koma amfani da tsarin saka ƴan wasa na 3-4-3 zuwa ƴan wasa huɗu a baya, da dawo da Kobbie Mainoo cikin tawagar da kuma mayar da kyaftin ɗin ƙungiyar Bruno Fernandes komawa buga wasa can kusa da gaba, ba kamar lokacin Amorim ba.
Ya kuma wasu sauye-sauye masu ƙarfi. Matakin da ya ɗauka na fara wasa da Patrick Dorgu a ɓangaren hagu na gaban Man United maimakon Matheus Cunha ya fara yin tasiri.
Dorgu ya ci kwallo biyu a wasanni biyu karkashin Carrick, inda shi ma Cunha ya shiga fili ya ci wa United kwallo mai kyau da ta bai wa ƙungiyar ta Old Trafford nasara kan Arsenal da kuma bayar da kwallo a ci a wasansu da Manchester City.
"Shi Cunha yana amfani da damar da yake samu," in ji Carrick. "Bai ji daɗin rashin fara wasanni da suka wuce ba. Amma ya yi amfani da damar cikin yanayi mai kyau. Ya yi tasiri sosai a wasannin biyun.
"Zuciyata ta raya min cewa zai ci kwallo lokacin da aka ba shi kwallo. Ya cancanci hakan."
Cunha ya shaida wa shirin wasanni na BBC Match of the Day cewa yanzu "akwai ƙarin karfi" da kuma ƙwazo tun zuwan Carrick.
"Ya buga wasanni a nan na tsawon shekaru," in ji Cunha. "Ya san yadda Manchester United take. Ya yi magana da mu kuma ya faɗa mana irin babbar damar da mutum zai samu na buga wa wannan ƙungiya. Ya ce kowaye na adawa da mu, don haka ya kamata mu shiga filin wasa don ba da dukkan ƙarfin mu."
Ya rage ga wasu mutane don ganin tasirin Carrick saboda shi ya ce ba zai yi hakan ba.
"Carrick ya yi matukar ƙoƙari tun zuwansa," a cewar tsohon ɗan wasan baya na Ingila Micah Richards.
Sai dai, duk da irin wannan namijin koƙari da Michael Carrick ya fara da shi, tsoffin ƴan wasan ƙungiyar Roy Keane da Gary Neville, ba su amince cewa a ba shi mukamin kocin ƙungiyar na dindindin ba.
"Ina ganin ko da Manchester United ta lashe duka wasanninta har zuwa karshen kaka, ba zan bai wa Carrick kocin ƙungiyar ba," in ji Keane. "Ina ganin suna buƙatar kwararren koci wanda ya fi shi."
Nevilla ya goyi bayan haka shi ma: "Ina ganin yana da kyau Carrick ya ci gaba da rikon ƙwarya har zuwa karshen kaka, daga nan sai a miƙa ragama ga Thomas Tuchel, Carlo Ancelotti - ko kuma wani da yake da irin ƙwarewarsu.
Makonni uku da suka wuce, Carrick yana can yana hutunsa tare da Wayne Rooney a tsibirin Barbados. A ranar Juma'a, sun zauna tare a Old Trafford don kallon yadda Kai Rooney ya taimakawa tawagar ƴan ƙasa da shekara 18 na Man United zuwa zagayen 16 na FA Cup - ajin matasa.
Idan wani ya san yanda Carrick yake ji yanzu, to Rooney ne.
"Nasara biyu cikin wasanni biyu kan Manchester City da kuma Arsenal abu ne da bai taɓa mafarkinsa ba lokacin da karɓi aikin Man United a makon da ya gabata.
"Kun ga sauyawar ɗaukacin abubuwa tun bayan zuwansa."











