Sojojin Amurka huɗu sun mutu a hatsarin jirgin soji a Iraqi

Asalin hoton, Reuters
Huɗu daga cikin ma'aikatan jirgin sojin Amurka shida da ya yi haɗari a Iraqi sun mutu, kamar yadda Cibiyar ayyukan sojin Amurka ta tabbatar.
Jirgin sojin na taimaka wa jiragen yaƙin Amurka ne da ke kai hare-hare a Iran, kuma ɗaya ne daga cikin jirage biyu da hatsarin ya rutsa da su, inda ɗaya jirgin ya sauka lafiya.
Jirgin sojin na KC-135 ya faɗo ne bayan wani "hatsarin" da ya shafi wasu jirage biyu.
Rundunar sojin Amurka ta ce "ana ci gaba da aikin ceto" a yammacin Iraqi - abin da sojoji suka ce ya faru ne a "yankin da ba na maƙiya ba."
"Lamarin ba ya faru ba ne a yankin da ake yaƙi ko kuma musayar wuta," in ji sanarwar.
Jirgi na biyu da lamarin ya shafa ya sauka lafiya, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Babu dai tabbas kan adadin mutanen da ke cikin jirgin da kuma makomarsu.
Sannan ba a san dalilin da ya haddasa hatsarin jirgin ba, da kuma asalin wurin da hatsarin ya faru.
Ana hasashen jirgin sojin wanda ke ba jiragen yaki na Amurka mai ya yi taho mu gama ne da wani jirgin a sararin samaniya.
Irin jiragen masu tankar mai na taka rawa sosai a yaƙi, inda jiragen yaƙi da masu kai harin bama-bamai ke dogaro da su musamman idan har sai sun yi dogon zango kafin inda za su kai hari.
Rundunar sojin Amurka ta ce lamarin ya faru ne a Iraƙi amma ba a san tazarar da ke tsakanin wurin da makwabciyarta Iran ba.
Wannan na zuwa bayan rundunar sojin Faransa ta ce wani harin jirgi marar matuki ya raunata sojojinta shida a yankin Kurdawa na Iraƙi a ranar Alhamis.
An kai masu hari ne a lokacin da suke atisaye tare da dakarun Iraƙi, kamar yadda rahotanni suka nuna.
Ƙungiyar da ke goyon bayan Iran ta ce aikinta ne
Kafar yaɗa labarai ta Reuters ta ruwaito ƙungiyar Islamic Resistance da ke Iraƙi na cewa ita ce ta kai hari kan jirgin tankar mai na Amurka da ya yi haɗari.
Islamic Resistance, ƙungiya ce a Iraƙi da ke samun goyon bayan Iran, ta saki wani bayani da ke cewa ita ce ta kai hari kan jirgin KC-135 a yunƙurin "tabbatar da ƴancin ƙasar Iraƙi da kuma sararin samaniyarta."
Bayan sanarwar da Amurka ta bayar na hatsarin jirgin nata, kafafen yaɗa labarai a Iran sun yi iƙirarin cewa an kai masa hari ne.
Hakan na faruwa ne duk kuwa da cewa Amurka ta ce jirgin ya yi hatsari ne.
Yadda jirgi ke shan mai a sama

Asalin hoton, Getty Images
Shan mai yayin da jirgi ke tafiya a sama ya ƙunshi jirage biyu da za su riƙa tafiya a kusa da juna, inda jirgin da zai yi ƙarin man zai je kusa da jirgin takar mai, daga nan ne sai wani bututu ya fito daga tankar, ya yi ƙasa-ƙasa.
Jirgin da zai sha man zai matsa sama kaɗan ta yadda bututun ƙarin man zai yi daidai da wurin tankin man jirgin, inda bututun zai manne da jirgin yaƙin.
Da zarar bututun ya shiga kafar da ke jirgin jirgin yaƙin, sai a tura man zuwa cikin tankin jirin, kuma hakan na daukar tsawon mintuna.
A tsawon lokacin shan man, bambancin taƙi kadan ne tsakanin jirgin da ke shan man da kuma jirgin tankar man, kuma a wasu lokutan hakan na faruwa ne a cikin dare.
Ana buƙatar ƙwarewa sosai kafin matuƙin jirgi ya iya shan man ba tare da tangarɗa ba.
Sannan a lokacin irin wannan shan mai akan kashe duk wata wuta da ke jikin jiragen domin kada maƙiya su hango su.











