Abin da Mojtaba Khamenei ya faɗa a jawabinsa na farko

Asalin hoton, IRNA
Sabon jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei ya ce ƙasarsa za ta cigaba da rufe mashigar hormuz, wadda ke da matuƙar muhimmanci a hada-hada man fetur a duniya.
Mojtaba ya bayyana haka ne a sanarwa ta farko da ya fitar a matsayinsa na jagoran addinin Iran, wadda aka karanta a tashar talabijin ɗin ƙasar.
Rufe mashigar ta hormuz dai ta jefa ƙasashen duniya cikin damuwa bayan samun tsaiko a kasuwar ɗanyen man fetur ta duniya, kasancewa wani adadi mai yawa na man fetur ta mashigar yake wucewa zuwa ƙasashen duniya.
Wannan ne dai karon farko da aka ji ɗuriyar Mojtaba tun bayan da hare-haren Amurka da Isra'ila suka kashe mahaifinsa, Ayatollahi Ali Khamenei a ranar 28 ga watan Fabrairu.
Mojtaba Khamenei ya maye gurbin mahaifinsa ne a matsayin jagoran addini a ranar 8 ga watan Maris.
Mojtaba ne ɗa na biyu a cikin ƴaƴan marigayi Ali Khamenei, duk da cewa an daɗe ana tunanin shi ne zai iya gadon mahaifinsa.
Bayan mahaifinsa, hare-haren ranar sun kashe mahaifiyarsa da matarsa, sannan rahotanni suka nuna cewa shi ma ya ji rauni.

Asalin hoton, Getty Images
Abubuwan da ya faɗa
Datse mashigar Hormuz
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mojtaba ya umarci dakarun Iran da su ci gaba da datse mashigar Iran. Rufe mashigar Hormuz ya jefa duniya cikin garari, inda farashin makamashi ya yi sama.
Ana kallon rufe mashigar a matsayin babban makamin da Iran za ta yi amfani da shi a yaƙin.
A wani jawabi da ya yi ranar Talata, shugaban Amurka Donald Trump ya gargaɗi Iran game da "rufe mashigar Hormuz".
Amurka ta ce ta lalata sama da jirage 10 wadanda "Iran ta yi amfani da su wajen dasa nakiyoyi" a mashigar.
Aminci da ƙasashen Gulf
Sabon jagoran na Iran ya bayyana cewa suna da aminci da ƙasashen da suke maƙwabtaka da su, amma sai ya shawarce su da su kulle sansanonin sojin Amurka a ƙasashensu domin su cigaba da zaman lafiya.
Tun bayan ƙaddamar da harin Amurka da Isra'ila kan ƙasar, Iran ta riƙa kai hare-hare a ƙasashen yankin Gulf irin su Qatar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da kuma Bahrain.
A ranar Laraba ƙasashe suka kada ƙuri'ar yin alla-wadai da hare-haren da Iran ke kaiwa kan ƙasashen na Gulf.
Ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin Amurka
Mojtaba Khamenei ya ce ƙasarsa za ta ci gaba da kai hare-hare a kan sansanonin sojin Amurkar a ƙasashen na kusa da su.
Amurka na da sansanoni da dama a ƙasashen yankin Gulf, kuma tun bayan ɓarkewar yaƙin ne Iran ke ci gaba da kai musu hari.
Ɗaukar fansa
A game da mutanen da aka kashe musu a hare-haren, Mojtaba ya ce za su "rama jinin Iraniyawa da aka zubar."
Ya yi misali da harin Minab, inda Amurka ta kai wani hari a kusa da wata makaranta, wanda ya yi sanadiyar 'mutuwar mutum 168, da ƙananan yara 110'.
Iran dai ta nace cewa Amurka ce ta kai hari a makarantar, amma sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya shaida wa BBC a makon jiya cewa za su yi bincike.
Jinjina ga Hezbollah
Mojtaba Khamenei ya bayyana godiyarsa ga ƙungiyoyin Resistance Front a Yemen da Hezbollah a Lebanon da wasu ƙungiyoyin a Iraqi
Neman diyya
"Za mu nemi diyyar asarar da muka yi daga maƙiyanmu, idan suka ƙi biya, za mu kwashi kadarori daidai da asarar da muka yi, idan kuma bai samu ba, sai mu tarwasa kwatancin kadarorin da muka yi asara."
Ya ƙara da cewa, "kamar yadda muka yi gargaɗi a baya, muna kai hare-hare ne a sansanonin sojin Amurka a ƙasashen nan, kuma za mu ci gaba da kai hare-haren, duk da cewa mun yarda da zaman lafiya tsakaninmu da maƙwabtanmu."
Tun da farko, Ambasadan Iran a Cyprus, Alireza Salarian ya bayyana wa jaridar The Guardian ta Birtaniyya cewa, "na samu labarin cewa ya ji rauni a ƙafarsa da hannu. Ina tunanin yana kwance ne a asibiti yana jinya, ba na tunanin zai samu sukunin gabatar da jawabi."











