Me ya sa magana kan yaƙin Isra'ila da Iran ta zama laifi a Najeriya?

Me ya sa aka kama Sani Waspapping

Asalin hoton, X/Multiple

Bayanan hoto, Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS ta kama wasu matasa biyu a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin ƙasar
    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

Ƙungiyar kare hakkin ɗan'adam ta Amnesty International ta nuna damuwa kan yadda hukumomi a Najeriya ke ci kama 'yan ƙasar da suka yi tsokaci kan yaƙin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.

Rahotanni na cewa a cikin makon nan Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS ta kama wasu matasa biyu a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin ƙasar, saboda kalaman da suka yi a shafukan sada zumunta game da yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran.

A wata sanarwa da Amnesty ta fitar, ta ce yawancin mutanen da hukumar DSS ɗin take kamawa, sun kasance “masu nuna adawa ne ga Amurka da Isra'ila”.

Ƙungiyar ta yi zargin cewa ana ƙoƙarin gurfanar da matasan da aka kama bisa wasu zarge-zargen da ba su da wata ma'ana, lamarin da ta ce zai jefa tsoro a zukatan 'yan ƙasar da take haƙƙin faɗin albarkacin bakinsu.

Kungiyar ta kuma yi Allah wadai da kama mutune biyun da aka yi, inda ta ce ɗaya daga cikinsu har yanzu yana tsare ba tare da samun damar ganin iyali ko lauyoyinsa ba.

Kungiyar ta ce “akwai tayar da hankali matuƙa kan yadda ake gaza girmama dokokin ƙasa da kuma da kare haƙƙoƙin bil'adama a Najeriya”.

Amnesty ta ce: "Ya zama wajibi hukumomin Najeriya su daina take haƙƙin 'yan ƙasar saboda sun bayyana ra'ayinsu a shafukan sada zumunta"

Mutanen da aka kama

Tun bayan ɓullar rahotannin kama matasan a makon nan, 'yan ƙasar da dama sun yi ta nuna bacin ransu a shafukan sada zumunta da neman a saki mutanen da aka kama.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ruwaito cewa an kama wani fitaccen mai amfani da shafin X, Sani Buhari, wanda aka fi sani da Waspapping a jihar Kaduna a ranar Juma'ar da ta gabata.

Sani Waspapping shi ne mutum na biyu da DSS ta tsare dangane da halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya.

Bayani sun nuna cewa an kama Waspapping ne bayan wasu ra'ayoyi da yake wallafawa a shafinsa na X, da nuna goyon bayansa ga Iran tare da sukar Amurka da Isra'ila.

Sai dai takamaimai ba za a iya tantace wane saƙo ne ya sa aka kama matashin ba.

Kafin kama shi, DSS ɗin ta fara gayyatar wani matashi mai suna Abubakar Adamu da aka fi sani da AbbakarAffan a shafin X, daga jihar ta Kaduna bayan ya wallafa wani ra'ayi a kan yaƙin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.

Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ruwaito cewa DSS ta gurfanar da Affan a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Kaduna, inda ta ce wani sakon da ya wallafa yana kira da a kashe Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, na iya haddasa rikicin kasa da kasa da zai shafi Najeriya.

BBC ta nemi jin ta bakin hukumar DSS, amma ba ta ce komai ba game da batun.

Abin da muka sani zuwa yanzu

DSS sun kama Sani Waspapping

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa an saki Sani Waspapping, amma ana ci gaba da masa ɗaurin talala a gida.

Bayanan sun ce an umurci matashin ya ci gaba da zama a gida, kuma an sanya wa wasu makusantansa takunkumin yin magana kan batun.

BBC ta tuntuɓi wasu makusantansa inda suka ce "ba za su iya cewa uffan kan maganar ba sai sun samu izini."

Har yanzu dai DSS ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan kama Waspapping ba.

Haka ma babu wani ƙarin bayani kan matashi Affan da aka gurfanar a gaban kotu, amma Amnesty ta yi Allah wadai da salon da hukumomin ƙasar suke bi wajen hana faɗin albarkacin baki.

‘Ana yi mana barazana’

Bayan abin da ya faru na kama wasu matasa kan yin sharhi game da rikicin na Iran da Amurka da kuma Isra’ila, wasu masu amfani da shafukan sada zumunta sun ce a yanzu suna cikin taoro.

Wani matashi da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce ya samu wasu saƙonni da ke gargaɗinsa da "ya bi a hankali, domin ana bibiyar duk abin da yake wallafawa a soshiyal midiya; ya san abin da zai riƙa faɗa".

Ya ce, ya yi amannar hakan ya biyo bayan wasu tsokaci da ya yi ne, da suke suna goyon bayan Iran da adawa da Amurka da Isra'ila.

"Ina wallafa mabanbantan ra'ayoyi, amma ba a taɓa min saƙon gargaɗi irin wannan ba," in ji shi.

Shi ma wani sanannen mai amfani da shafukan sada zumunta mai suna Dr. Tsiga ya wallafa shafinsa na Facebok cewa ya amsa gayyatar DSS a ranar Talata game da wani ra'ayi da ya wallafa.

Ya ce, saƙon da ya wallafa ya shafi yanayin tsaro ne a yankin arewa maso gabashin ƙasar da yadda ake siyasantar da batun.

Sai dai daga bisani ya wallafa wani saƙo da ke nuna cewa, DSS ɗin ta sake shi ya koma gida bayan ya yi ƙarin bayani da amsa wasu tambayoyi.

"Bayan tattaunawar da muka yi kuma na yi ƙarin bayani, an ba ni izinin komawa gida ga iyalina," in ji shi.