KAI TSAYE, Yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya 13/03/2026
Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Juma'a 13 ga watan Maris 2026.
Sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya ce "an raunata" jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei kuma akwai yiwuwar an "illata shi", (sai dai editan labaran ƙasashen waje na BBC ya ce ba mu da tabbacin hakan).
Lokacin da ya kafa hujja da sanarwar da Mojtaba ya fitar a ranar Alhamis, wanda aka karanta a gidan talabijin na gwamnatin Iran, Hegseth ya ce me ya sa ba a ga bidiyon shi ba.
"Na san kun san me ya sa," kamar yadda ya bayyana.
Sakataren tsaron na Amurka ya ce Mojtaba na "tsoro" kuma "an raunata" shi.
Hotunan yadda ƴan harka Islamiyya ke zanga-zangar Ranar Qudus a Kano da Abuja
Ga wasu hotunan da ke nuna yadda 'yan Shi'a ke gudanar da zanga-zangar lumana ta "Ranar Qudus" ta duniya domin bayyana rashin jin daɗinsu da mamaye Gaza da gaɓar yamma da tekun Jordan.
A kowacce ranar juma’a ta karshen watan Ramadan ce ranar Qudus ta duniya, inda magoya bayan Falasɗinu ke gudanar da zanga-zangar lumana ko kuma muzaharar nuna adawa da ƙasashen Amurka da Isra'ila, a sassan duniya.
Asalin hoton, Getty Images
Za mu ci gaba da datse Mashigar Hormuz - Mojtaba Khamenei
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Iran ta ce za ta ci gaba da toshe Mashigar Hormuz, wadda ita ce muhimmiyar hanyar jigilar kayayyaki ta teku, a cewar wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na gwamnati, wadda aka danganta ga sabon jagoran addinin kasar.
Mojtaba Khamenei bai fito a bainar jama’a ba tun bayan da ya gaji mahaifinsa, sai dai akwai rade-radin da ke cewa ya ji rauni, amma ba a tabbatar da hakan ba.
Babu alamar cewa an raunana gwamnatin Iran - Sharhi, Jeremy Bowen
Har yanzu babu wata alama da ke nuna cewa an raunana duk da tsammanin da wasu a Amurka suka yi cewa kashe jagoran addinin ƙasar a ranar farko ta yaƙi zai haddasa rikicewa cda rushewar gwamnatin kasar in ji masu sharhi.
Masu sharhin sun ce wasu a Washington sun yi tunanin cewa bayan mutuwar Ali Khamenei, tsarin mulkin Iran zai iya rugujewa cikin sauri. Amma har yanzu babu wata shaida da ke nuna hakan, domin tsarin mulkin ƙasar ba ya dogara da mutum guda kawai.
Shugaban Amurka Donald Trump mutum ne da ke yawan magana kan muhimmancin shugabanci mai ƙarfi. Wata kila wasu a Amurka sun yi tunanin cewa bayan mutuwar Khamenei za a samu irin abin da ya faru a Venezuela, inda rikicin siyasa ya iya jawo sauyin gwamnati cikin gaggawa.
Amma irin wannan tunani na iya nuna rashin fahimtar yadda tsarin mulkin Iran yake in ji masu sharhi.
Tsarin gwamnatin ƙasar ya rarraba iko tsakanin manyan cibiyoyi na addini da gwamnati da kuma rundunar juyin juya halin Ira, wanda ke da ƙarfin iko sosai.
Iran kuma na da dogon tarihi na ƙin amincewa da Amurka da Isra’ila, lamarin da ke sa gwamnati da al’ummar ƙasar su haɗa kai lokacin da ake ganin akwai barazana daga waje.
A halin yanzu, Isra’ila ta bayyana cewa za ta yi ƙoƙarin kashe sabon jagoran Iran Mojtaba Khamenei. Sai dai har yanzu babu tabbacin ko ya ji rauni ko a’a.
Haka kuma ana mamakin cewa duk da ƙoƙarin da Tehran ke yi na gina martabar sabon jagoran, har yanzu ba a fitar da hotuna ko saƙonni da yawa daga gare shi ba.
Amurka za ta kai hare-hare mafiya girma kan Iran a yau - Hegseth
Asalin hoton, PENTAGON
Bayanan hoto, Sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth
Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth ya bayyana cewa a yau ne kasar za ta ƙaddamar da hare-hare mafiya girma kan Iran.
Hegseth ya jaddada cewa ƙudurin Amurka “ba zai girgiza ba,” yana mai cewa ƙasar a shirye take ta kai hari mafi girma kan Iran.
Ya kuma ce shugaban Amurka Donald Trump ne ke da ikon yanke shawara kan yadda yaƙin zai gudana.
“Shi ne zai ƙayyade yadda yaƙin zai kasance, yadda zai gudana da kuma lokacin da za a ɗauki matakai,” in ji Hegseth.
Ministan tsaron ya ƙara da cewa a yau Amurka za ta sake ƙaddamar da “hare-haren sama mafi yawan da ta taɓa kai wa a sararin samaniyar Iran.”
Dakarun juyin juya halin Iran sun yi barazanar ɗaukar mataki mafi tsauri kan masu zanga-zanga
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar tattara bayanan sirri ta rundunar juyin juya halin Iran IRGC ta yi gargaɗi cewa za ta ɗauki mataki mafi tsauri da ya fi wanda aka yi ranar 8 ga watan Janairu kan mutanen da ke shirin gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnati ƙasar,
Ranar 8 ga watan Janairu ta kasance ranar da aka samu tarzomar zanga-zangar adawa da gwamnati, wadda ta haifar da mutuwar mutane da dama a Iran.
Hukumar ta ce makiya na ƙoƙarin amfani da zanga-zangar domin cimma burinsu a fagen yaƙi, inda suke ƙoƙarin haifar da tsoro da hargitsi a tituna.
Rundunar IRGC ta kwatanta mahalarta zangar watan Janairu da suka haifar da tarzoma a matsayin “makiya,” sannan ta bayyana cewa waɗanda suka shirya sabon zanga-zangar za su fuskanci martani da ya fi na ranar 8 ga Janairu.
An ji ƙarar fashewa kusa da wurin zanga-zangar Ranar Quds a Tehran
An ji ƙarar fashewa a wasu wurare kusa da inda ake gudanar da zanga-zangar Ranar Quds a Tehran.
Wani gini da ke kusa da hanyar wurin zanga-zangar a titin Enghelab ya samu hari.
A lokaci guda, shaidu sun ce sun ji ƙarar fashewa mai ƙarfi a kusa da titin Fatemi da kuma wajen ginin Ma’aikatar Cikin Gida.
Haka kuma, an ruwaito wasu fashe-fashe a arewacin da yammacin birnin Tehran.
Majalisar dattawa za ta gana da jami’an IMF kan tattalin arzikin Najeriya
Asalin hoton, Getty Images
Ana sa ran shugabannin majalisar dattawan Najeriya za su gana da manyan jami’an Asusun Lamuni na Duniya IMF domin tattauna halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki da shirye-shiryen gyara da ake aiwatarwa a ƙarƙashin gwamnatin Bola Tinubu.
Wannan wata tattaunawa ce da ake gudanarwa tsakanin IMF da Najeriya a kai a kai domin tantance manufofin tattalin arziki da kwanciyar hankalin kuɗi a ƙasar.
Mataimakin Shugaban Majalisar dattawa,Barau Jibrin ne ya sanar da taron da za a gudanar daga 4 ga Maris zuwa 17 ga Maris, 2026.
Ana sa ran wannan ganawar zai bai wa ‘yan majalisar damar fahimtar tsarin sarrafa tattalin arzikin gwamnati da kuma gano irin goyon bayan da wannan Asusun Lamuni na Duniya zai iya bayarwa wajen aiwatar da manyan sauye-sauyen tattalin arzikin Tarayyar Najeriya.
Sojojin Amurka huɗu sun mutu a hatsarin jirgin soji a Iraqi
Asalin hoton, Getty Images
Huɗu daga cikin ma’aikatan jirgin sojin Amurka shida da ke kan jirgin tankin mai KC-135 da ya faɗo a yammacin Iraqi sun mutu, kamar yadda Cibiyar ayyukan sojin Amurka ta tabbatar.
A cikin wani saƙo da Centcom ta wallafa a shafin X a safiyar Juma’a, rundunar ta ce “huɗu daga cikin ma’aikatan jirgin shida sun tabbata sun mutu.”
Centcom ta ce ana ci gaba da binciken yadda lamarin ya faru, kuma an tabbatar cewa “faɗuwar jirgin ba ta faru ne sakamakon harin maƙiya ko harin abokan aiki ba.”
Rundunar ta ce jirgin ya faɗo ne a “yankin iska na aminci,” yayin da wani jirgi na biyu da lamarin ya shafa ya sauka lafiya, ba tare da wata matsala ba.
Rundunar sojin ta ƙara da cewa “ana ci gaba da aikin ceto a yammacin Iraqi,” kuma lamarin ya auku a wani “yanki da ba na maƙiya ba.”
Sanarwar ta kuma nuna cewa lamarin bai faru a wani yanki na yaƙi ko musayar wuta ba.
'Sabon jagoran addnin Iran ya tsira daga hare-hare sau biyu'
Asalin hoton, Tasnim news agency
Wani ɗan majalisar ƙasar Iran ya bayyana cewa sabon jagoran addinin kasar, Mojtaba Khamenei, ya tsira daga hare-hare biyu da aka kai masa.
A cewar kamfanin dillancin labaran gwamnatin kasar, ɗan majalisar da ke wakiltar Jahrom, Mohammad Reza Rezaei Kochi, ya ce Mojtaba Khamenei yana tare da Ali Khamenei lokacin da aka kai hari kan gidan jagoran addinin, amma ya tsira daga yunƙurin kashe shi.
Kochi ya ƙara da cewa an sake kai wani hari a wani asibiti a lokacin da sabon jagoran ke wurin, amma Amurka da Isra’ila ba su cimma burinsu ba.
Sai dai ɗan majalisar bai bayyana sunan asibitin ko wurin da aka kai harin ba.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump a wata hira da tashar Fox News ya ce sabon jagoran Iran ya samu rauni a ranar farko ta hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai inda ya ce yana kyautata zaton cewa yana raye amma an ji masa rauni.
A jiya ne kuma aka wallafa saƙon farko daga sabon jagoran in da ya ce Iran za ta dauki fansar mutanenta da aka kashe a harin da Isra'ila da Amurka suka kai wa kasar.
An ji ƙarar fashewa a wurare daban-daban na birnin Tehran
An ji ƙarar fashewa a wurare daban-daban na birnin Tehran, babban birnin Iran, bayan da Isra’ila ta fara wasu sabbin hare-hare a yankin.
A cikin wani saƙo da rundunar sojin Isra’ila ta wallafa a shafinta na Telegram, ta ce ta fara wani gagarumin jerin hare-hare kan cibiyoyin da ta danganta da gwamnatin Iran a faɗin birnin Tehran.
A cikin ’yan mintunan da suka gabata kuma, an ruwaito samun fashe-fashe da dama a ciki da wajen birnin.
Yaƙin Iran: 'An kashe sojan Faransa ɗaya a Iraqi'
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron ya ce an kashe wani sojan ƙasar a yayin wani harin jirgin sama mara matuki da Iran ta kai a yankin Erbil na Iraq, inda wasu da dama suka ji rauni.
Ya bayyana cewa sojan da aka kashe shi ne Cif ofisa Arnaud Frion, wanda shi ne farkon mutumin Faransa da ya rasa rayuwarsa tun bayan fara yaƙi da Iran a ƙarshen watan da ya gabata.
“Ga iyalan mamamcin da abokan aikinsa, ina mika ta'aziyyata da kuma nuna dukkan ƙauna da goyon bayan ƙasa a gare ku,” in ji Macron a shafukan sada zumunta.
“Wasu daga cikin sojojinmu sun samu raunuka. Faransa tana tare da su da kuma iyalansu.”
Macron ya soki hare-haren da aka kai kan sojojin Faransa da ke yaƙi da kungiyar IS a yankin, yana mai cewa ba za a yarda da hare-haren ba
“Zaman su a Iraq wani ɓangare ne na yaƙi da ta’addanci saboda haka yaƙin Iran ba zai iya bayar da hujja ga irin waɗannan hare-hare ba.”
Ana gudanar da zanga-zangar Ranar Quds a birane daban-daban na Iran
Asalin hoton, Getty Images
Ana gudanar da zanga-zangar Ranar Quds a birane daban-daban na ƙasar Iran, inda jama’a suka fito kan tituna domin halartar gangamin.
Tashar talabijin ta ƙasar Iran na watsa hotunan zanga-zangar da ake gudanarwa.
Hotunan da aka fitar sun nuna yadda magoya bayan gwamnati suka fito kan tituna a biranen Semnan, Yazd, Ahvaz da Khorramabad domin shiga zanga-zangar.
Ranar Quds wani biki ne da ake yi duk shekara a ranar Juma’a ta ƙarshe a watan Ramadan, inda ake gudanar da gangami domin nuna goyon baya ga al’ummar Falasɗinu da kuma sukar manufofin Isra’ila.
Ana gudanar da irin waɗannan gangamun a daruruwan birane a faɗin Iran, inda mahalarta kan riƙa ɗauke da tutoci da kuma rera taken nuna goyon baya ga Falasɗinu.
Amurka ta ba da damar sayar da man Rasha don rage tsadar mai
Asalin hoton, Getty Images
Amurka ta bayar da umarnin sayar da man Rasha na wucin-gadi, da cewa ta yi hakan ne da nufin magance karanci da tsadarsa a duniya.
Masu sayen man na jin radadin tashin, kuma bayan hakan a karshe ma zai shafi farashin sauran kayayyaki.
Zuwa jiya Alhamis Baitul-malin Amurka ya amince da bayar da lasisin sayar da mai da kayayyakin da aka yi da man wadanda tuni aka loda a jiragen ruwa.
An yi hakan ne kwana daya bayan kasashe 32 da hukumar makamashi ta duniya ciki har da Amurka suka amince su, saki ganganr mai miliyan 400.
To amma kuma duk da wannan mataki na hukumar, farashin man ya ci gaba da tashi a iya Alhamis, inda man samfurin Brent ya zarta sama da dala dari daya a ganga daya - a karon farko tun 2022.
Amurka ta ce ta kai hari kan kusan wurare dubu 6 a cikin Iran
Asalin hoton, Getty Images
Amurka ta ce ta kai hare-hare kan kusan wurare dubu shida a cikin Iran tun bayan fara yaƙi da ƙasar.
Ta ce hare-haren sun haɗa da kai farmaki kan gomman jiragen ruwa, wuraren kera makamai, da kuma kan garkuwar kare hare-haren sama.
A halin da ake ciki kuma, Isra’ila ta ce tana kai wasu sababbin jerin hare-hare ta sama kan babban birnin Iran ɗin, Tehran.
A daren da ya gabata ma, Isra’ilar ta ce ta kai wani hari a wani wuri da ke da alaƙa da kera makaman nukiliya.
Sai dai Iran ta dage cewa shirinta na nukiliya ba na kera makamai ba ne, yana da nufin ayyukan ci gaban ƙasa na zaman lafiya.
An kai waɗannan hare-haren na baya-bayan nan ne yayin da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ke cewa ƙasarsa na yi wa rundunar sojin juyin juya hali ta Iran gagarumar illa.
Isra'ilawa da dama sun jikkata sakamakon harin Iran
Asalin hoton, Getty Images
Isra'ilawa da dama ne suka jikkata bayan wani harin makami mai linzami da Iran ta harba a Isra'ila wanda ya faɗa wani ƙauye da ke arewacin ƙasar a safiyar Juma’a, kamar yadda hukumomin agajin gaggawa suka bayyana.
A cewar hukumar motocin daukar marasa lafiya ta Magen David Adom, jami’an jinya sun yi wa Isra'ilawa 58 da suka jikkata magani sannan suka kai su asibitocin yankin bayan harin da ya auku a garin Zarzir kusa da Nazareth.
Rahotannin kafofin watsa labaran Isra’ila sun ce wata mata ta samu rauni sakamakon gutsattsarin ƙarfen roka, kuma halin da take ciki bai da tabbas.
Sojojin Isra’ila sun bayyana cewa sun tura wata tawagar sojoji zuwa wurin da lamarin ya faru.
A cikin wata sanarwa, rundunar sojin ta ce jami’anta tare da hukumomin agaji da na ceto suna duba halin da ake ciki a wurin.
A jiya ne ma’aikatar lafiyar Isra'ila ta ce adadin mutanen da suka jikkata sakamakon hare-haren makamai masu linzami da Iran ke kai wa ƙasar ya kai 2,745.
Iyalin Ali Khamenei: Su wa aka kashe, su wane ne ke raye?
Labarin kisan da aka yi wa wasu daga cikin iyalan tsohon jagoran addinin Iran, Ali Khamenei ya haifar da tambaya game da waɗanda suka rage a dangin.
Surukai maza da mata nawa jagoran addinin ke da su, kuma waɗanne ne danginsa na kusa-kusa?
A tsawon lokacin mulkinsa, Ali Khamenei ya naɗa da yawa cikin iyalansa manyan muƙaman siyasa ko wasu ma'aikatun gwamnati.
Kuma da dama cikin dangin nasa daga baya sun koma masu adawa da shi, inda aka ɗaure wasunsu a gidajen yari ko suka tafi gudun hijira ƙasashen ƙetare.
Wannan muƙala ta tattaro wasu bayanan da ake da su game da iyalan tsohon jagoran addinin.
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a.
Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Aisha Babangida ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.
Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.