Me ya sa shugaban Iran ya nemi afuwar maƙwaftan ƙasar?

Pezeshkian

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban ƙasar Iran Masoud Pezeshkian
    • Marubuci, Amir Azimi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Persian
  • Lokacin karatu: Minti 5

Shugaban ƙasar Iran Masoud Pezeshkian ya bai wa mutane da dama mamaki bayan ya nemi afuwar maƙwaftan ƙasar bisa ga hare-haren da ƙasar ta ƙaddamar a cikinsu.

Shugaban ya nemi afuwar ne a ranar Asabar, a matsayinsa na ɗaya daga cikin mambobin kwamitin riƙon-ƙwarya na jagorancin ƙasar.

Abu ne mai wahala wata ƙasa ta nemi afuwar wata, musamman a alokacin da ake gwabza yaƙi, haka nan ma kalmomin da ya yi amfani da su, sun ɗauki hankali.

A mafi yawan lokuta da wahala ka ga shugabanni sun yi amfani da kalamar "nadama", sannan kuma ba su cika ɗaukan alhaki ba kai-tsaye.

Amma shi Pezeshkian kai-tsaye ya amince cewa an kai farmaki kan ƙasashe masu maƙwaftaka sannan ya ce a yanzu an buƙaci dakaru su tsagaita daga kai musu hari har sai idan daga cikin ƙasashen ne aka kai wa Iran hari.

"Na ga dacewar na nemi afuwar ƙasashe maƙwafta waɗanda aka kai wa hari," in ji shi. "Ba aniyarmu ba ne mu far wa maƙwaftanmu."

To sai dai tambayar ita ce: shin wannan neman afuwa ta kai zuci, kuma me ya sa sai yanzu?

Wata ƙila mataki ne na shugabancin ƙasar wajen ganin yankin bai hargitse ba.

Ƙasashe da dama na yankin sun samu kansu a tsakiyar musayar wuta tun bayan harin da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar kan Iran ranar Asabar 28 ga watan Fabarairu.

Pezeshkian ya bayyana cewa "dole ne" ta sanya Iran ta ƙaddamar da hare-hare bayan harin da aka kai mata wanda ya yi sanadiyyar kashe manyan jagorori da kwamandojin ƙasar.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ta hanayr neman afuwa, Iran ta nuna cewa ba ta son yaƙi ya rincaɓe tsakaninta da maƙwaftanta.

Haka nan kuma saƙon na alamta halin da siyasar yankin ke ciki: Duk da cewa Amurka na da sansanoni da kuma dakaru a wasu daga cikin ƙasashen da ke maƙwaftaka da Iran, ƙasar za ta mayar da kanta saniyar ware idan ta riƙa kai musu hari.

Sai dai babu tabbas kan ko za a ga afuwar a aikace.

Rahotanni daga yankin na nuna cewa har yanzu Iran ba ta daina kai hare-hare ba.

Qatar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa duk sun sanar da kakkaɓo makaman da Iran ta jefa musu.

Idan waɗannan hare-hare suka ci gaba, zai ɗora ayar tambaya kan ko akwai matsalar shugabanci a ƙasar ta Iran.

Tun bayan hare-haren farko da aka kai wa Iran waɗanda suka hallaka jagororin Iran, ciki har da jagoran addini na ƙasar Ayatollah Ali Khamenei, tafiyar da ƙasar ta koma hannun wani kwamitin riƙon-ƙwarya.

A rubuce, wannan tsari zai bai wa mutane irin su Pezeshkian ƙarin faɗa a ji, fiye da a baya lokacin da mutum ɗaya ke da wuƙa da nama.

A aikace kuwa, tsarin zai haifar da rashin tabbas kan wanda ke da ikon jan ragamar dakarun sojin ƙasar, masu matuƙar ƙarfi, kamar dakarun juyin juya-hali.

Idan har aka ci gaba da ganin Iran na lkai hare-hare maƙwafta duk da kalaman shugaban ƙasar, hakan zai nuna cewa ko dai akwai matsala game da tsarin isar da saƙo ko kuma akwai wadanda ke nuna turjiya game da batun rage kai hare-hare.

Masu ra'ayin mazan jiya da ke cikin harkar tsaro ta ƙasar sun daɗe suna ganin cewa matsin lamba ga ƙasashen yakin shi ne babban makamin da Iran za ta iya amfani da shi wajen kare kanta daga Isra'ila.

Martanin da aka samu daga cikin gida ya nuna rarrabuwar kai game da hakan. Wasu masu ra'ayin riƙau a ƙasar sun soki lamirin kalaman shugaban ƙasar, inda suka bayyana kalaman a matsayin masu rauni.

Halin da siyasar ƙasar ciki yanzu yana da sammatsi: an kashe da dama daga cikin jagororin ƙasar waɗanda suka kasance masu tsattsauran ra'ayi, sauran da suka rage na ƙasa-ƙasa kuwa na yin taka-tsantsan.

Gare su, duk wani neman afuwa ga ƙasashen waje, tamkar miƙa wuya ne a wannan yanayi.

A wajen Iran kuwa, akwai martani daban-daban kan kamalam shugaban ƙasar.

Ba tare da ɓata lokaci ba, a shafinsa na sada zumunta, shugaban Amurka Donald Trump ya ce "Iran ta nemi afuwa kuma ta miƙa wuya" ga maƙwaftanta, inda ya ce matsin da Amurka da Isra'ila ke yi wa ƙasar na aiki.

Trump ya sha nanata cewa abu ɗaya da zai kawo ƙarshen rikicin Amurka da Iran shi ne idan Iran ɗin ta miƙa wuya.

Sai dai wannan tamkar abu ne mai wuya a harkar diflomasiyya.

A tarihi, abu ne mai wahala ka ga wata ƙasa ta miƙa wuya a lokacin rikicin, kawai a dalilin ruwan wuta ta sama, duk runtsi. Sai dai idan an samu dakaru ta kasa waɗanda za su tursasa yin hakan.

Me Iran ke nufi?

Ga shugaba Pezeshkian da jagororin Iran, akwai yiwuwar abin da suke tunani daban ne.

Tsagaita wuta zai iya samar da wani ɗan sarari.

Idan har wanda ya samu muƙamin jagoran addini na Iran ya zama mai tsattsauran ra'ayi, kafar cimma mafita ta hanyar diflomasiyya za ta ƙara tsukewa.

Haka nan kuma hakan zai ƙara ɗiga wata ayar tambayar: shin hakan na nuna cewa Pezeshkian mutum ne mai sauƙi hali wanda za a iya tattaunawa da shi, irin shugaban da ƙasashen Yamma za fi son su yi hulɗa da shi?

A cikin jawabinsa, ya yi ƙoƙarin haɗa bu biyu wuri ɗaya, turjiya da kuma bude ƙofa. Ya yi watsi da batun miƙa wuya, amma ya nuna buƙatar yin taka-tsantsan da ƙasashe maƙwafta.

A lokaci guda kuma, ana ci gaba da hasashen yadda jagorancin Iran zai kasance a nan gaba.

Manyan ƴan siyasa da malamai da kuma kwamandojin rundunar juyin juya hali za su iya ganin wannan a matsayin wata dama ta ƙarfafa kansu.

Idan har Pezeshkian ya gaza kawo daidaito da kuma nuna ƙarfin iko kan dakarun ƙasar, masu adawa za su ga cewa akwai buƙatar a samu wani jagoran wanda ya fi shi tsattsauran ra'ayi.

Ya zuwa yanzu akasarin maƙaftwan Iran na taka-tsantsan, wasu kuma sun yi gum da bakunansu, suna jira su gani ko afuwar da shugaban ya nema za ta kawo sauyi a halin da ake ciki.

Isra'ila, wadda ke kallon rikicin a matsayin wata dama ta raunana daɗaɗɗiyar maƙiyiyarta, da wuya ta fassara wannan neman afuwa a matsayin wadda ta kai har zuciya.

Akwai dai giɓi da yawa a cikin bayanin Shugaba Pezeshkian, kuma kila da gangan ne.

Zai iya yiwuwa saƙo ne na neman sassauta lamurra a halin da ake ciki, ko kuma wani mataki ne na nema wa Iran ƙarin lokaci ko kuma alamu na sauyin siyasa a ƙasar.

Ko kuma a yanayi irin wannan, zai iya zama duka ukun ne.