Me ya sa Iran ke kai wa ƙasashen Musulmi da ke maƙwaftaka da ita hari?

Asalin hoton, REUTERS/Stringer
- Marubuci, Vitor Tavares
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Da BBC News Brasil em São Paulo
- Lokacin karatu: Minti 5
Mitoci kaɗan ne tsakanin tsohon garin Dubai da kuma magudanar ruwan da ta raba tsakiyar birnin. Hayaƙi ya turnuƙe sararin samaniya a daren Talata 3 ga watan Maris.
Kamar yadda gwamnatin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawan ta tabbatar, wani harin jirgi maras matuƙi ya sauka a birnin bayan yaƙin da aka fara tsakanin Iran da Isra'ila da Amurka.
Sabon harin ya farmaki ofishin jakadancin Amurka ne, kuma ya sauka a kan wajen ajiye motoci amma babu wanda ya raunata.
A wani harin da Iran ta kai kafin wannan ma, jirgi maras matuƙi ya kai hari kan ofishin jakadancin Amurka da ke Riyadh a Saudiyya.
Waɗannan misalin su ne na baya-bayan nan a rikicin da ake yi, wanda aka fara tun bayan kisan Ayatollah Ali Khamenei.
Waɗannan hare-haren na matuƙar tasiri a ƙasashen yankin Gulf ko kuma a ce ƙasashen Larabawa, irinsu Dubai da Qatar da Bahrain da Kuwait da Oman da Saudiyya.
Iran ta bayyana cewa ta kai harin ne kan sansanonin Amurka a waɗannan ƙasashen, amma kuma tarkacen makamai masu linzamin da na jirage marasa matuka sun riga sauka a kan wasu otel-otel da filayen jiragen sama a yankin.
Har yanzu babu tabbacin ko da gangan Iran ta kai hari wajen shaƙatawa da wasu muhimman wurare ko kuma kawai tsautsayi ne ya faɗa kansu a lokacin da take ƙoƙarn kai harin a Amurka, kamar yadda Farfesa Daniel Rio Tinto, ƙwararre a fannin tsaron ƙasa da ƙasa ya yi hasashe.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sai da a ra'ayin Rio Tinto, Iran tana son nuna wa ƙasashen yankin Gulf cewa haɗa kai da Amurka zai haifar musu da babbar asara.
"Wannan kamar a ce ne: idan kuka bari Amurka ta kai min har daga yankunan ku, ko kuma ba ku ƙalubalanci yadda Amurkan take amfani da sansanoninku wajen kai min hari ba, to ku ma za ku ɗanɗana kuɗarku," in ji shi.
Tsawon shekaru da dama, shugabannin Iran sun yi ta ƙoƙarin ganin ƙasashen yankin Gulf sun fatattaki sojojin Amurka daga yankin domin neman kariya daga wajenta amma sun ƙi ba da haɗin kai.
To amma me ya sa waɗannan ƙasashen suka bar Amurka a yankunan su duk da suna ci gaba da hulɗa da Iran?
Amsar dai ba ta wuce yadda kowane ɓangare ke ƙoƙarin kare manufarsa a yankin ba.
Sansanin Amurka mafi girma a yankin gabas ta tsakiya shi ne na Al Udeid, a Qatar. Manufar Amurka a yankin ita samun kusanci da yankunan da take hari. Ita kuma Qatar tana kallon abin ta fuskar da za ta amfani daga hulɗa da Washington, in ji Farfesan.
"Ba lallai Qatar ta iya ganin alfanun sansanin Amurkar da wuri ba, amma za ta iya amfana da hakan wajen cin gajiyar goyon bayan Amurka a wasu tsare-tsare na ƙasashen ƙetare," a cewar masanin.
Wani misalin shi ne alaƙar ta da Saudiyya, inda ta bar sojojin Amurka ƙasar, wanda a madadin hakan, gwamnatin Amurka tana kare muƙamin Yariman Mohammed bin Salman a idon duniya.
Masu sharhi kuma sun yi amannar cewa, fara yaƙi da Iran ta yi da ƙasashen maƙwabta da ke iyaka da Isra'ila, ya nuna girman barazanar da ke cikin katsalandan ga harkokin ƙasar.
Ko ma dai mene ne, waɗannan ƙasashe ne da ake yawan sufurin jiragen sama, irinsu Dubai da Doha. Matafiya da dama sun maƙale a waɗannan biranen sun kasa komawa garuruwansu.
Shin an yi raga-raga da tsibirin tsaro?

Asalin hoton, HANNIBAL HANSCHKE/EPA/Shutterstock
Illolin da hare-haren da ake kaiwa yankin Gulf za su fi shafar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, ƙasar da a 'yan shekarun nan ta kasance wadda aka fi zuwa yawon buɗe ido, da siyayyar kayan alfarma da damarmakin kasuwanci.
A ranar Talata, ma'akatar tsaro ta UAE ta bayyana cewa tsaron sararin samaniyar ta ya lalata makamai masu linzami 172 tun bayan da Iran ta ƙaddamar da kai hare-harenta a yakin. Wasu 13 kuma sun faɗa cikin teku yayin da ɗaya daga ciki ya faɗa ƙasar.
Ma'aikatar ta kuma gano jirage marasa matuƙa 812 da Iran ta harba, inda ya kakkaɓe 755 daga cikin su. 57 kuma sun faɗi a ƙasar.
UAE ta ƙara da cewa ta gano tare da lalata makamai masu linzami takwas "waɗanda suka lalata wasu wurare tare da hallaka mutum uku yayinda mutum 68 suka ji ƙananan raunuka," da kuma lalata "wasu wuraren gwamnati."
Wasu daga cikin mace-macen sun faru ne a filin jirgin sama na Abu Dhabi, a lokacin da karikitan jirgi maras matuƙi suka faɗo a bayan an ɓaro shi, kamar yadda hukumomin filin jirgin saman suka bayyana.
An lalata wani sashe na filin jirgin saman Dubai wanda shi ne aka fi zirga-zirga a faɗin duniya, inda gwamnatin ƙasar ta ce lamarin ya illata wasu ma'aikata huɗu.
An kuma ruwaito wasu abubuwa da suka fashe a wani babban otal da ke tsibirin Palm Jumeirah.
Wasu karikitan jirgi maras matuƙi sun kuma tayar da gobara a gefen babban masaukin baƙi na Burj Al Arab.
Amazon ma ta kulle cibiyarta da ke UAE na wucin gadi bayan wani harbin bindiga a ginin.
Cinzia Bianco, wani mai sharhi kan yankin Gulf ya wallafa a shafinsa na X cewa:
"Wannan babban ƙalubale ne ga Dubai, saboda ta dogara kacokan ne a kan tsaron yankin". "Wataƙila akwai hanyoyin da za su iya bi amma kuma hakan ba makawa," in ji shi.
A cewar Farfesa Rio Tinto, ko da akwai tsibiri mai tsaro idan yankin gabas ta tsakiya babu tsaro, ba lallai hankali ya kwanta ba, amma kuma ƙalubalen na wani ɗan lokaci ne, kuma ya danganta da tsawon lokacin da za a ɗauka ana rikicin.
"Muna magana ne a kan wurin da ya shahara wajen yawon buɗe ido, kuma ba na tunanin za ta rasa wannan damar a nan kusa, sai dai in har an samu gagarumin sauyin siyasa a yankin, wanda hakan ne zai iya zama barazana" in ji shi.
Masanin ya kuma ba da misali da ƙasar Masar, wadda take samun masu zuwa yawon buɗe ido duk da yake nahiyar turai ta yi gargaɗi kan tafiya zuwa yankin saboda rikicin da ake samu.
Sai dai ya ce, duk da za a samu koma baya ga harkar yawon buɗe ido, za a iya samun gagarumin sauyi a yankin.
Kamar yadda wani mai sharhi kan tsaro Frank Gardner ya yi nazari, Iran ta wuce gona da iri.
Ƙasashe irin su Qatar, Oman, Saudiyya da UAE sun daɗe suna shiga tsakanin rigingimun ƙasashen duniya.
Alal misali, Qatar ta kasance ƙasar da ke wanzar da zaman lafiya a tsawon shekaru 20. Ƙasar ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsagaita wuta a tsakanin Gaza da Isra'ila da Hamas, kuma ta taimaka wajen tabbatar da irin waɗannan a baya.
Babban dalilin hakan shi ne yadda Qatar take son haɓaka iskar gas ɗin da ke yankin Gulf ɗin da aka gano a shekarar 1990.
Rawar da Qatar take takawa wajen tabbatar da zaman lafiyar yankin an ɗabbaƙi a kundin dokoki tun a shekarar 2004.
Sai dai wannan matsayin ma iya samun tagarɗa.
"Abubuwa da dama su kan canza idan aka fara maganar ɗaukar matakin soji. Lamarin yana ƙara matuƙar wahala a samu shiga tsakani idan har wata ƙasa ta harba makami mai linzami a kanka," in ji Rio Tinto.
"Ba na tunanin za a ci gaba da kallon ƙasashen a matsayin masu shiga tsakani. Ba za mu ci gaba da ganin alaƙa mai kyau tsakanin ƙasashen ba."











