Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Alhamis 07/05/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi da Aisha Aliyu Jaafar da Nabeela Mukhtar Uba

  1. Rufewa

    A nan za mu kawo ƙarshen wannan shafin na labaran na kai-tsaye.

    Sai kuma gobe idan Allah ya nuna mana.

    Mu kwana lafiya.

  2. Zimbabwe za ta mayar da gonaki ga turawa

    Zimbabwe ta ce za ta mayar da gonaki guda 67 ga ‘yan kasashen Turai 4, kusan shekara 25 bayan da aka kwace su a wani shirin sake fasalin mallakar filaye da ya janyo rudani a baya.

    Ministan Aikin Gona na kasar, Anxious Masuka, ya shaida wa majalisar dokoki cewa matakin wani bangare ne na yarjejeniyoyin kare zuba jari da aka kulla, da kasashen Denmark da Switzerland da Jamus da kuma Netherlands.

    Shugaban kasar, Emmerson Mnangagwa, wanda ya daɗe a matsayin na hannun daman da marigayi Robert Mugabe, na kokarin gyara alaka da kasashen yammacin duniya.

    Masu bayar da lamuni na kasa da kasa sun bukaci a gudanar da sauye-sauye, ciki har da warware rikicin filaye, a matsayin sharadin sassauta bashin da ake bin kasar.

  3. FIFA za ta yi kyauta ga wanda ya saya tikitin kallon gasar kofin duniya mai tsada

    Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA, Gianni Infantino, ya yi alkawarin ba da wata kyauta ta musamman ga duk wanda ya sayi tikitin gasar cin kofin duniya kan farashi da yake mai tsananin tsada, yayin da ya sake kare tsarin farashin tikitin.

    An dai sha suka sosai kan farashin tikitin, inda aka wallafa wasu a shafin sayar da tikitin na FIFA, kan kuɗi fiye da dala miliyan biyu.

    Mista Infantino ya yi barkwanci cewa idan har wani ya siyi tikitin a irin wannan kudin, shi da kansa zai kai masa kayan kwalam da maƙulashe a matsayin karramawa ta musamman.

  4. Yaƙin son rai da Trump ya ƙaddamar ne ya rage mana kuɗin shiga - Jamus

    Jamus

    Asalin hoton, EPA

    Ministan Kudin Jamus, Lars Klingbeil, ya dora alhakin raguwar kudaden harajin da ake sa ran kasar za ta samu kan abin da ya kira yaƙin Donald Trump kan Iran da ya ƙirƙira don son rai.

    Wata majalisar kwararrun masu hasashen kudaden haraji ta rage kiyasin kudaden shiga zuwa shekarar 2030, wanda ya kai fiye da dala biliyan 100 idan aka kwatanta da hasashen baya.

    A cewar wakiliyar BBC asarar kuɗaɗen harajin tarayya da na jihohi da ma na kananan hukumomi na bana kaɗai da aka tafka ta kai kusan dala biliyan 13.

    Gwamnatin kasar dai na fama da kokarin farfaɗo da tattalin arzikin ta wanda ya daɗe yana tangal-tangal.

  5. Aƙalla jiragen ruwa dubu 20 ne suka maƙale a mashigar Hormuz - MDD

    Iran

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙungiyar kamfanonin jiragen ruwa ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce akwai aƙalla jiragen ruwa dubu 20 da suka maƙale saboda rufe mashigar Hormuz da Iran ta yi.

    Sakatare-janar na ƙungiyar, Arsenio Dominquez ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya yi a Panama, inda ya ce ƴan babu ruwanmu da suka maƙale a sanadiyar lamarin.

    A ranar Litinin ne Amurka ta sanar da fara rakiyar jiragen dakon man fetur wu riƙa wucewa ta mashigar, amma daga bisani ya dakatar.

    Yanzu dai Iran ta sanar da cewa tana nazarin daftarin yarjejeniyar zaman lafiya daga Amurka domin kawo ƙarshen yaƙin da buɗe mashigar.

  6. Hare-haren JNIM sun yi ajalin mutum 30 a Mali

    Mali

    Asalin hoton, AFP

    Jami'an tsaro a Mali sun tabbatar da cewa hare-haren da ƙungiyar JNIM da ke mubaya'a ga Al-Qaeda ta ɗauki alhakin ƙaddamarwa sun yi sanadiyar mutuwar sama da mutum 30.

    Wata majiyar tsaron ƙasar ta bayyana cewa an kai hare-haren ne a kusan tare, sannan jami'an tsaron suka ƙara da cewa an kwashe kayayyakin mutane a ƙauyukan Kori-Kori da Gomossogou, sannan an yi ƙone-ƙone.

    Ƙungiyar JNIM mai iƙirarin jihadi ce ta sanar da cewa ita ce ta kitsa tare da kai hare-haren, waɗanda suka zo kimanin mako biyu bayan hare-haren ƙungiyar da na ƴan aware.

  7. Za a ɗauki matasa aikin soja a Nijar

    Nijar

    Asalin hoton, CNSP

    A jamhuriyar Nijar, hukumomin kasar ne suka bayyana aniyarsu ta daukar matasa aikin soja.

    Gwamnatin mulkin sojin ƙasar dai ta dade tana yaki da matsalar rishin tsaro da ke neman ya zama ruwan dare a kasar.

    Matasan ƙasar da suka dade suna kokawa kan rashin ɗaukarsu aikin soja sun yi na’am da wannan mataki na gwamnati.

  8. Ƴansanda sun tabbatar da garkuwa da ɗaliban Jami'ar Jihar Nasarawa

    Ƴansanda

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar ƴansandan jihar Nasarawa ta tabbatar da garkuwa da ɗaliban Jami'ar Jihar Nasarawa da suke karatu a tsangayar kimiyya da fasaha ta jami'ar da ke garin Gudi a ƙaramar hukumar Akwanga ta jihar Nasarawa.

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Ramhan Nansel ya fitar, inda ya ce rundunar ta samu kira ne daga yankin, inda a cikin wani ya tabbatar musu cewa a safiyar Alhamis, wasu ƴanbindiga sun kwashe ɗaliban.

    Sanarwar ta ƙara da cewa maharan sun yi dirar mikiya ne a ɗakin kwanan ɗaliban da ke Unguwar Ninzo a garin na Gudi, sannan suka kwashi ɗaliban da ba a tantance adadinsu ba.

    Rundunar ta ce an tantance mutum shida da suka ɓace, kuma dukansu ɗaliban injiniyanci ne, sai wani wanda ya ziyarci ɗan uwansa ɗalibi.

    Sanarwar ta ce Kwamshinan ƴansandan jihar, Shettima Jauro Mohammed ya ziyarci yankin, sannan ya yi umarnin a tura ƙarin jami'ai domin bibiyar sahun maharan, tare da haɗin gwiwar sojoji da sauran jami'an tsaro domin ceto sauran ɗaliban.

  9. Kotu ta fitar da 'takardar kisan kan' Jeffery Epstein

    Epstein

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani alƙali a Amurka ya bayar da umurnin sakin wani takarda da aka ce ita ce takardar da mutuminan da aka kama a laifin cin zarafin ƙananan yara Jeffrey Epstein ya rubuta wata guda kafin ya kashe kansa.

    A cikin takardar wadda aka bayyana ta a jiya Laraba, ya ambato binciken da aka shafe watanni ana yi kansa, inda ya ce ''ba a gano komai ba'', kuma ya ce '' abin jin daɗi ne a ce mutum na iya zaɓen lokacin da zai bar duniya''.

    Tun da farko abokin zaman gidan yari na Epstein ya yi iƙirarin cewa ya gano takardar ce a cikin wani littafi ne bayan Epstein ɗin ya yi ƙoƙarin kashe kansa a watan Yulin 2019.

    Wata guda bayan nan aka tsinci gawarsa a ɗakinsa na gidan yari.

    BBC ba ta tabbatar da sahihancin cewa Epstein ne ya rubuta takardar, kuma hukumomin Amurka ba su ce uffan ba.

    Mutuwarsa, wadda hukumomi suka ce kashe kansa ne, ya faru ne a yayin da yake zaman jiran shari'ar da ake masa kan yin safarar ƙananan yara domin yin lalata da su.

  10. MDD ta buƙaci Tunisia ta kawo ƙarshen take haƙƙin ƴan adawa da ƴan jaridar ƙasar

    Volker Turk

    Shugaban hukumar kare haƙƙin biladama na Majalisar ɗinkin duniya ya yi kira ga Tunisia da ta kawo ƙarshen abin da ya kira 'ƙaruwar danniyar' ƴan adawa, da ƴan jarida da kuma masu fafutukar kare haƙkin biladama.

    Volker Turk ya faɗi hakan ne bayan da aka dakatar da ayyukan wasu ƙungiyoyin fararen hula biyu na Tunisia, kuma aka kama wani ɗan jarida - ɗaya daga cikin ƴan jarida 29 da aka garkame a gidan yari.

    Mista Turka ya yi kira ga hukumomin Tunisia su saki duk mutanen da aka tsare saboda sun bayyana ra'ayinsu.

  11. Sakataren harkokin wajen Amurka ya yi ganawar sirri da Fafaroma Leo

    Fafaroma Leo na gaisawa da Marco Rubio

    Asalin hoton, Reuters

    Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, yayi tattaunawar sirri da Fafaroma Leo a fadar Vatican.

    Fafaroma Leo, wanda shi ne Ba’amurke na farko da ya jagoranci cocin Katolika, ya sha fuskantar kakkausar suka daga Shugaba Trump a bainar jama’a.

    Fafaroman ya soki gwamnatin Trump kan fara yaƙin Iran da kuma tsauraran manufofinta kan ƴan ci rani.

    Wani jami’in Amurka ya ce tattaunawar da aka yi tsakanin Fafaroma Leo da Mista Rubio, ta gudana cikin yanayi na fahimtar juna da kuma amfani.

    A cikin sa’o’i biyu da rabi da Mista Rubio ya shafe a fadar Vatican, ya kuma gana da babban jami’in diflomasiyyar Vatican, Cardinal Pietro Parolin.

  12. Afirka ta Kudu ta nuna damuwa kan shirin Najeriya na kwashe ƴan kasarta

    Ramaphosa

    Asalin hoton, Reuters

    Afirka ta kudu ta bayyana damuwarta kan shirin Najeriya na kwaso ƴan ƙasarta da ke son komawa gida.

    Ministan harkokin wajen ƙasar Ronald Lamola ya tattauna da takwararsa ta Najeriya domin lalubo hanyoyin da za a kawo ƙarshen zaman tankiyar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

    '' Mun san cewa Najeriya ƙasa ce mai ƴancin ɗaukr irin wannan mataki na kwashe ƴan ƙasarta da ke son tafiya, amma muna ganin cewa yin hakan ba zai magance matsalar shigar baƙi ta hanyar da ba ta dace ba.'' a cewar Ronald Lamola.

    A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, ministar harkokin wajen Najeriya Bianca Odumegwu - Ojukwu ta ce har yanzu suna ci gaba da shirya kwaso ƴan Najeriya, kuma ta buƙaci hukumomin Afirka ta Kudu su ɗauki tsatsauran mataki kan kisan ƴan Najeriya.

    ''Ba za mu zauna muna kallon cin zarafi da wulaƙanta ƴan ƙasarmu a Afirka ta Kudu ba, da kuma kisansu babu gaira babu dalili'' in ji ta.

    Ta kuma bayyana damuwa kan yadda ake hantarar yara a makaranta, sai dai Lamola ya ce hukumomin ilimi na ƙoƙari wajen kare yara.

    Zanga zangar ƙyamar baƙi da ake yi a makonnin baya bayan nan a Afirka ta kudu ya sanya damuwa a zuƙatan baƙi daga ƙasashen Nahiyar, musamman masu gudanar da kasuwanci, duk da zai zanga zangar na lumana ne.

  13. An ceto sauran mutanen da aka sace daga gidan marayu a jihar Kogi

    sojoji

    Asalin hoton, @DEFENSENIGERIA

    Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun ceto yara bakwai da manya biyu da aka sace daga wani gidan marayu a jihar Kogi a watan da ya gabata.

    Cikin wata sanarwar da ta fitar, runduar sojin ta ce an ceto su ne a wani aiki da jami'an tsaro suka yi.

    Satar mutane domin neman kuɗin fansa dai ya zama ruwan dare a Arewa ta Tsakiyar Najeriya, inda ƴan bindiga ke yawaita kai hari kan makarantu da kuma ƙauyuka.

  14. Bello El-Rufai ya fice daga jamiyyar APC zuwa ADC

    Bello El Rufai

    Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kaduna ta Arewa a majalisar wakilan Najeriya Hon. Mohammed Bello El-Rufai ya sanar da sauya sheƙarsa daga jamiyyar APC mai mulki, zuwa Jamiyyar ADC.

    A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafukansa na sada zumuta, Bello El-Rufai ya kuma ce zai sake neman takarar kujerar ɗan majalisar wakilai a ƙarƙashin sabuwar jamiyyarsa.

    A cewar sa, matakin sauya sheƙar bai zo masa da sauƙi ba, sai dai a matsayinsa na ɗan tsohon gwamnan Kaduna Mallam Nasir El Rufai, yana cike da ƙwarin gwiwa, da jajircewa da kuma imanin cewa alummar jihar na buƙatar wakilci na gari da kuma ci gaba.

    Ya kuma ce ya koma jamiyyar ADC ne tare da ɗan majalisa mai wakiltar Soba Hon Engr Suleiman Richifa, da kuma na Makarfi/Kudan Hon Umar Ajilo.

  15. Gwamnatin Sokoto ta ce yara 33 sun mutu sakamakon ɓarkewar cutar sankarau

    ana yi wa yaro allura

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin jihar Sokoto ta tabbatar da mutuwar yara 33 sakamakon ɓarkewar cutar sankarau a wasu sassan jihar.

    Kwamishinan lafiya na jihar Dr Faruk Abubakar, wanda ya tabbatar da hakan a jiya Laraba, kamar yadda jaridar DailyTrust ta ruwaito, ya ce tun bayan bullar cutar a watan da ya gabata, mutum 256 ne ake zargin sun kamu da ita a ƙananan hukumomi takwas na jihar.

    Dr Abubakar ya ce an samu mutum 63 da ake zargi sun kamu da cutar a ƙaramar hukumar Sabon Birni, sai mutum 60 a Wamakko, sai kuma mutum 51 a Shagari, a Tambuwal kuma an samu mutum 33, sai Dange Shuni mai mutum 26, a Kebbe kuma an samu 16, sai Bodinga da Kware an samu mutum biyu biyu, yayin da aka samu mutum ɗaya a Gada.

    Kwamishinan lafiyar ya ce akasarin waɗanda suka mutu saboda cutar, sun mutu ne a gida kafin a kai ga zuwa asibiti.

    Ya alaƙanta jinkirin da ake samu wajen kai marasa lafiya asibiti da mummunar fahimtar da ake yi cewa cutar aljanu ce ba ta asibiti ba.

  16. Kotu ta samu tsohon ministan lantarkin Najeriya da badaƙalar Naira biliyan 33

    Saleh Mamman

    Asalin hoton, Saleh Mamman/Facebook

    Wata babbar kotun tarayya a Najeriya da ke Abuja, ta samu tsohon ministan lantarki Saleh Mamman da laifuka 12 da suka shafi halasta kuɗaɗen haram kimanin Naira biliyan 33.

    Mai shari'a James Omotosho, wanda ya yanke hukuncin a yau Alhamis, ya jinkirta yanke masa hukunci har sai ranar 13 ga watan Mayun 2026, kasancewar tsohon ministan ba ya kotun a lokacin da aka same shi da laifin.

    A cikin bayanin da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ta wallafa a shafinta na sada zumunta, ta ce domin tabbatar da cewa bai fice daga ƙasar ba kafin nan, lauyanta Rotimi Oyedepo SAN, ya buƙaci kotun ta bayar da sammacin kawo tsohon ministan kotu.

    Saleh Mamman dai ya riƙe muƙamin minista ne daga shekarar 2019 zuwa 2021 ƙarƙashin gwamnatin marigayi tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

    A ranar 28 ga watan Afrilun wannan shekara ne kuma ya sayi fom ɗin neman takarar zama gwamna a jihar Taraba a ƙarƙashin jamiyyar APC mai mulki.

  17. Ta yaya tarwatsewar ƴan adawa zai shafi zaɓen 2027?

    .

    Asalin hoton, Peter Obi/Facebook

    A daidai lokacin da babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027 ke ƙara ƙaratowa, masu bibiyar al'amuran siyasa na ganin salon na siyasar na ɗaukar salo daban-daban, musamman a ɓangaren ƴan hamayya.

    Tuni tsoffin ƴantakarar shugaban Najeriya biyu a zaɓen 2023 wato Rabiu Musa Kwankwaso da ya tsaya takara a NNPP a zaɓen 2023 da takwaransa na LP, Peter Obi suka dunƙule a sabuwar jam'iyyar NDC domin fafatawa da Bola Tinubu.

    Ƴantakarar biyu na cikin manyan jiga-jigan da a baya suka haɗu a jam'iyyar ADC da ake wa laƙabi da ta haɗaka, sabuwar haɗuwar manyan ƴan hamayya a cikinta domin fuskantar zaɓen 2027 a matsayin tsintsiya maɗaurinki ɗaya.

    A baya dai jam'iyyun hamayyar ƙasar sun gudanar da wani taron a birnin Badun na jihar Oyo domin samar da matsaya kan yadda za su fuskanci zaɓen, taron da ya samu halartar jiga-jigan PDP da ADC da Labour da NNPP.

  18. Ana ci gaba da neman wasu fasinjojin jirgin ruwan da aka samu ɓarkewar cutar HantaVirus

    jirgin ruwa

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'an lafiya daga ƙasashe da dama na ci gaba da ƙoƙarin gano fasinjojin da suka bar wani jirgin ruwan yawon buɗe ido kafin a tabbatar da ɓarkewar cutar HantaVirus a cikinsa.

    Gwamnatin Netherlands ta ce ana nema fasinjoji aƙalla 40 da suka fice aga jirgin samfurin MV Hondius a tsibirin Saint Helena kafin a samu rahoton ɓarkewar cutar.

    Turawa uku ƴan yawon buɗe ido sun mutu sakamakon kamuwa da cutar, yayin da aka kwashe wasu da dama domin su sami kulawa a asibitoci da ke Turai da Africa ta Kudu.

    A yanzu jirgin ruwan na kan hanyarsa ta zuwa Tsibirin Canary da ke Sipaniya.

  19. Shugaban Sudan ta Kudu ya kori babban hafsan sojin ƙasar da ministan kuɗi

    Salva Kiir na Sudan ta Kudu

    Asalin hoton, AFP

    Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya kori babban hafsan sojojin ƙasar da ministan kuɗi a sauye sauye na baya bayan nan da ya yi a gwamnatinsa.

    Bai bayar da dalilin yin hakan ba, amma masu sharhi sun ce ya yi hakan ne da nufin ƙarfafa ikonshi a yayin da ake samun rashin tabbas kan magajin shi.

    Sudan ta kudu dai ta yi ta fama wajen aiwatar da sauye sauye da aka amince da su ƙarƙashin yarjejeniyar zaman lafiya ta 2018 wadda ta kawo ƙarshen yaƙin basasar shekaru biyar, ciki har da gudanar da zaɓuka.

    An ɗage zaɓe har sau uku, inda a yanzu aka shirya yi a watan Disamban wannan shekara, sai dai har yanzu babu tabbacin ko zaɓen zai gudana.

  20. Ana ci gaba da jimamin mutuwar mutumin da ya kafa gidan talibiji na CNN

    Ted Turner

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana ci gaba da aikewa da saƙonnin ta'aziyya bayan mutuwar Ted Turner, mutumin da ya kafa kamfanin da ya mallaki gidan talabijin na CNN, wanda ya rasu yana da shekara tamanin da bakwai.

    Shugaban Amurka Donald Trump, ya bayyana attajirin a matsayin "ɗaya daga cikin jiga-jigan da suka sauya fuskar yaɗa labarai a duniya.

    Goggagiyar mai gabatar da shirye-shirye a CNN Christiane Amanpour na cikin waɗanda suka aike da saƙon ta'aziyyarsu.

    Ta ce ''ya sauya duniya, Ted shi ne ya kirkiri gidan talabijin na farko da ya shiga ko ina a faɗin duniya da ya ke watsa shirye-shirye babu kakkautawa''.

    Baya ga CNN saran tashohin da Ted Turner ya mallaka sun hada da TNT sports da Cartoon Network da kuma Turner Classic Movies