Sau nawa Kwankwaso, Atiku da Obi suka sauya jam'iyya daga 1999 zuwa yau?

Asalin hoton, Multiple
- Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
Masu bibiyar al'amuran siyasa a Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayinsu dangane da sauya sheƙar da jiga-jigan adawar ƙasar biyu, Peter Obi da Kwankwaso daga jam'iyyar ADC zuwa NDC.
A ranar Lahadi ne ƴansiyasar biyu suka sanar da matakinsu na shiga jam'iyyar NDC, bayan fitarsu daga haɗakar ƴan hamayya ta ADC.
Obi da Kwankwaso sun bayar da dalilan rikicin cikin gida da shari'o'i da halin rashin tabbas da jam'iyyar ADC ke ciki, a matsayin abin da ya sa suka yanke shawarar fita daga cikinta.
A ranar 31 ga watan Disambar 2025 ne Peter Obi ya sanar da shiga jam'iyyar ADC a hukumance bayan kwashe watanni ana tattaunawa tsakanin jiga-jigan adawar ƙasar.
Shi kuwa Kwankwaso ya shiga ADC ne a ranar 30 ga watan Maris bayan ya sanar da ficewa daga jam'iyyarsa ta NNPP.
Shi kansa jagoran adawar ƙasar, Atiku Abubakar na gaba-gaba cikin masu yawan canja jam'iyya a siyasar ƙasar.
Yayin da wasu ke sukar ƴansiyasar da yawan sauya jam'iyya, wasu na ganin hakan a matsayin ƴancin da tsarin dimokraɗiyya ta ba su.
Cikin wannan muƙala mun duba lokutan da waɗannan jiga-jigan siyasar suka sauya jam'iyya tun komawar ƙasar tsarin dimokraɗiyya a 1999.
Atiku: PDP → AC → PDP → APC → PDP → ADC

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A farkon komawar Najeriya jamhuriya ta huɗu a 1999, Atiku ya shiga jam'iyyar PDP, yayin da tsohon shugaban ƙasar, Olusegun Obasanjo ya ɗauke shi a matsayin mataimakinsa.
Atiku Abubakar ya shafe tsawon shekara takwas a matsayin mataimakin shugaban ƙasa, daga 1999 zuwa 2007, sai dai a ƙarshen mulkin nasu sun samu saɓani da Obasanjo kan batun takarar shugaban ƙasa, lamarin da ya sa ya fice daga PDP.
A ranar 20 da watan Disamban 2006 ne Atiku ya shiga jam'iyyar AC, ya kuma samu tikitin yi mata takarar a zaɓen 2007, sai dai bai yi nasara ba.
Sai dai a AC ma zaman bai yi daɗi ba, domin kuwa a shekarar 2009, tsohon mataimakin shugaban ƙasar sake komawa tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP, bayan da aka fara samun rikicn shugaban AC, musamman da Bola Tinubu.
Bayan sake komawarsa PDP, Atiku ya ƙudiri aniyar takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2011, amma ya sha kaye a zaɓen fitar da gwani a hannun tsohon shugaban ƙasar, Goodluck Jonathan.
Sai dai shekara uku bayan haka, Atiku ya sake fita daga PDP, inda a farkon shekarar 2014 ya haɗa kai da jiga-jigan adawar ƙasar na wancan lokacin wajen kafa haɗakar jam'iyyar APC.
Atiku ya so tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2015 ƙarƙashin APC, amma ya sha kaye a hannun tsohon shugaban Najeriya, Marigari Muhammadu Buhari.
Shekara biyu bayan zaɓen 2015, Atiku Abubakar ya fita daga APC tare da sake komawa PDP a ranar 2 ga watan Disamban 2017.
Dalilin da ya bayar a lokacin shi ne matsalolin da suka addabi PDP, lokacin da yake mataimakin shugaban ƙasa tsakanin 1999 zuwa 2007, sun gyara don haka ungulu ta koma gidanta na tsamiya.
Ya kuma tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, ƙarƙashin jam'iyyar ta PDP, inda ya zo na biyu a zaɓen da Bola Tinubu na APC ya lashe.
Atiku Abubakar ya sake fita daga PDP zuwa haɗar ƴan'adawa ta ADC a 2025 da nufin haɗa hannun don ƙalubalantar Bola Tinubu na APC a zaɓen 2027.
Akwai alamomi masu ƙarfi da ke nuna cewa Atiku zai sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ƙarƙashin jam'iyyar ta ADC.
Kwankwaso: PDP - APC - PDP - NNPP - ADC - NDC

Asalin hoton, Rabiu Kwankwanso/FB
Sanata Rabiu Kwankwaso na daga cikin mutanen da suka kafa jam'iyyar PDP a 1998, inda kuma ya tsaya mata takarar gwamnan jihar Kano a zaɓen 1999, ya kuma yi nasara.
Kwankwaso ya sake tsayawa takarar gwamnan Kano domin neman wa'adin mulki na biyu a 2011, inda kuma ya yi nasara.
Sai dai a ƙarshen mulkin nasa, Kwankwaso ya samu saɓani da gwamnatin tarayya ta wancan lokacin ƙarƙashin Jonathan, lamarin da ya sa shi da wasu gwamnoni suka kafa ƙungiyar sabuwar PDP, tsagin Sanaka Kawu Baraje, daga baya kuma ya shiga APC.
Ya tsaya takarar sanatan Kano ta tsakiya a 2015 ƙarƙashin APC, ya kuma yi nasara.
Sai dai a shekarar 2018 ya sake komawa PDP bayan ficewa daga APC saboda saɓani da gwamnan Kano na wancan lokaci, Abdullahi Ganduje.
Kwankwaso ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2019, amma ya yi rashin nasara a zaɓen fitar da gwani.
A ranar 30 ga watan Maris ɗin 2022, tsohon gwamnan na jihar Kano ya shiga jam'iyyar NNPP, kwana guda bayan ficewarsa daga PDP.
Jagoran kwankwasiyyar ya kuma tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, sai dai bai yi nasara ba.
Duk da rashin nasarar da ya yi, jam'iyyarsa ta NNPP ta samu nasarar lashe zaɓen gwamnan jihar Kano mafi yawan jama'a a arewacin ƙasar.
Shekara huɗu bayan komawarsa NNPP, Sanata Kwankwaso ya fice daga jam'iyyar tare da shiga haɗakar ADC a ranar 29 ga watan Maris 2026.
Tsohon gwamnan jihar Kano ya ce ya ɗauki matakin ficewa daga NNPP ne la'akari da halin da siyasar Najeriya ke ciki, wanda ke bukatar haɗin kai.
Sai dai kimanin wata biyu bayan komawarsa ADC, Kwankwaso ya fice daga jam'iyyar tare da shiga NDC a ranar 3 ga watan Mayun 2026.
Peter Obi: APGA → PDP → LP → ADC → NDC

Asalin hoton, Peter Obi
Peter Obi ya shiga jam'iyyar AFGA, a farkon kafa ta a 2002, inda ya samu zarafin tsaya mata takarar gwamnan jihar Anambara da ke kudu maso gabashin Najeriya a 2003.
Ya kuma yi nasara, amma sai da aka tafka shari'a a kotu, lamarin da ya sa sai a 2006 a fara mulkinsa, sannan ya ƙare wa'adinsa na biyu a shekarar 2014.
A ranar 7 ga watan Oktoban 2017 ne tsohon gwamnan ya fice daga AFGA zuwa PDP.
A zaɓen 2019 Obi ya yi takara da Atiku a PDP a matsayin mataimaki, sai dai sun sha kaye a hannun Marigayi Muhammadu Buhari.
Sai kuma a shekarar 2022, Peter Obi ya fita daga PDP ya shiga LP, tare da tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023, sai dai bai yi nasara ba.
A ranar 31 ga watan Disambar shekara mai ƙarewa ne Peter Obi ya sanar da shiga jam'iyyar ADC a hukumance bayan kwashe watanni ana tattaunawa tsakanin jiga-jiganb adawar ƙasar.
Sai kuma a ranar Lahadi 3 ga watan Mayu, tsohon ɗantakarar shugaban ƙasar ya koma jam'iyyar NDC bayan ficewarsa daga ADC.









