Maja ko mara wa jam'iyya ɗaya baya: Mece ce mafita ga ƴan adawa a Najeriya?

Jagororin ƴan adawa a Najeriya, Peter Obi, Atiku Abubakar da kuma Rabi'u Kwankwaso

Asalin hoton, FB/Multiple

Lokacin karatu: Minti 4

Jam'iyyun hamayya a Najeriya na ci gaba da shirye-shirye gabanin babban zaɓen ƙasar na shekara ta 2027.

A baya-bayan nan an ga yadda ƴan adawar ke haduwa da juna, kuma tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya tabbatar wa duniya cewa suna tattaunawa domin ganin sun yi haɗakar da za ta ƙalubalanci jam'iyyar PDP a zaɓen ƙasar mai zuwa.

Sai dai wani abu da har yanzu bai fito fili ba shi ne dabarar da ƴan adawar ke son yin amfani da ita wajen tunkarar jam'iyyar mai mulki a 2027.

Masu lura da al'amuran yau da kullum na ganin cewa jam'iyyun na da zaɓi biyu, ko dai su haɗe wuri ɗaya tare da fito da sabuwar jam'iyya, wato maja, ko kuma su goya wa wata jam'iyya ɗaya baya.

Tsoshon mataikamakin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa a shiyyar Arewa maso yamma, kuma jigo a tattaunawar yin haɗakar jam'iyyun adawa a Najeriya, Salihu Muhammad Lukman ya ce: "Ana ƙoƙarin a ga an samu jam'iyyar da za a gyara ta, a gina ta sannan a ga yadda za a yi amfani da ita domin yin takarar shekarar 2027".

Sai dai ya ce babban abin da ke ba su tsoro shi ne yadda aka shiga aka dagula jam'iyyun da ake da su a ƙasar.

Jam'iyyun adawa da dama na ƙasar na fama da rigingimu na cikin gida, lamarin da ke barazana ga haɗin kansu.

Tun bayan babban zaɓen ƙasar na 2023 ne babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta faɗa rikici na shugabanci, lamarin da ya kai ga cire shugaban jam'iyyar Iyorchia Ayu, tare da ɗora Iliya Damagun.

Kuma tun daga wancan lokacin ne wasu ke ƙorafi game da yankin da shugaban jam'iyyar ya fito.

Haka nan a baya-bayan nan jam'iyyar ta yi fama da rikicin sahihin sakataren jam'iyyar na ƙasa, lamarin da ya kai har kotun ƙoli.

Jam'iyyar LP ma na fama da rikicin shugabanci tsakanin Julius Abure da ɓangaren Sanata Nenadi Usman.

Jam'iyyar NNPP ma tana fama da tata matsalar ta cikin gida inda ɓangarori biyu ke jayayya kan mallakin jam'iyyar tsakanin NNPP mai alamar kayan marmari da kuma NNPP mai alamar littafi da alƙalami.

Maja ko mara wa jam'iyya baya?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A tattaunawarsa da BBC, Salihu Muhammad Lukman ya ce "Muna son idan zai yiwu a yi amfani da ɗaya daga cikin jam'iyyun in kuma ba zai yiwu ba, mun yi nisa wajen tattaunawa da jam'iyyun nan kuma idan an cimma yarjejeniya za mu fito mu bayyana wa jama'a."

Sai dai a wata tattaunawar da BBC, ɗaya daga cikin manyan ƴan'adawa a Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau ya ce zai yi wahala jam'iyyun su iya dunƙulewa domin samar da adawa mai ƙarfi a 2027.

"Idan ka kalli sunayen waɗanda ke taruwa, jam'iyyun ba su a cikin tattaunawar saboda haka nan akwai kuskure," in ji Shekarau.

Ya ƙara da cewa "A 2012 zuwa 2013 lokacin da muka fahimci cewa akwai buƙatar a kawo canji, ba daidaikun mutane ne suka hadu suka yi APC ba, jam'iyyu ne suka taru suka samar da ita."

A watan Fabarairun 2013 ne wasu daga cikin jam'iyyun siyasa na Najeriya, waɗanda suka hada da CPC da ACN, da ANPP, da kuma hadin kan wasu ƴan siyasa da suka ɓalle daga jam'iyyun PDP da APGA suka haɗe wuri ɗaya inda suka samar da jam'iyyar APC, wadda kuma ita ce ta yi nasarar ƙwace mulki a hannun jam'iyyar PDP mai mulki a shekarar 2015, inda Muhammadu Buhari ya zama shugaban ƙasa.

Me masana ke cewa?

Farfesa Kabir Sufi na makarantar share fagen shiga jami'a a Kano, ya ce dukkanin zaɓi biyu da ƴan adawar ke da su ba abu ne mai sauƙi ba.

Sai dai ya ce shiga jam'iyya mai rajista a yanzu shi ne ya fi sauƙi cikin zaɓin guda biyu.

Saboda, a cewarsa ko a baya lokacin da aka kafa jam'iyyar APC a shekara ta 2013 abin bai zo da sauƙi ba: "An sha wahalahalu wajen neman wasu su jefar da rajistar jam'iyyarsu domin su shiga cikin jam'iyyar APC, misali shi abin da ya faru da jam'iyyar CPC, lokacin da sanata Rufa'i Hanga ya dage kan cewa ba zai bayar da takardar rajistar jam'iyyar ba," in ji Kabir Sufi.

Haka nan ya ce cika ƙa'idojin rajistar jam'iyya a wurin hukumar zaɓe shi ma wata ɗawainiya ce ta daban.

"Saboda haka shiga wata jam'iyya da ke da rajista ya fi sauƙi a yanzu," in ji Sufi.

Sai dai ya ce wannan tsarin yana da tashi matsalar "ta yadda za a iya samun darewar jam'iyyar, inda wasu za su ga cewa jam'iyyarsu ce, sai ka ga an samu rarrabuwar kai tsakanin ƴan asalin jam'iyyar da kuma waɗanda suka shiga."

A ɓangare ɗaya kuma farfesan ya ce idan ana maganar tasiri ne "to samar da sabuwar jam'iyya shi ne ya fi", domin a cewarsa za a iya kauce wa darewar kawuna tsakanin ƴan asalin jam'iyya da kuma baƙi.