Abin da ya sa na fita daga APC na koma SDP - El-Rufa'i

Nasir El-Rufa'i

Asalin hoton, FB/Nasir El-Rufa'i

Lokacin karatu: Minti 3

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya tabbatar da ficewarsa daga jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar, tare da komawa jam'iyyar SDP.

Hakan ya kawo ƙarshen raɗe-raɗin da ake yi na inda tsohon gwamnan zai nufa bayan alamun da suka nuna cewa ya raba gari da jam'iyyar APC.

A ranar Litinin ne El-Rufa'i ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, inda ya ce: "A yau 10 ga watan Maris, 2025, na miƙa takardar fita daga jam'iyyar APC a mazaɓata da ke Kaduna, wadda za ta fara aiki nan take. Kafin wannan lokaci na kammala tuntuɓar magabatana, da abokan tafiya da magoya baya a faɗin ƙasar nan game da inda za mu dosa, yanzu na yanke shawarar komawa jam'iyyar Social Democratic Party, kuma zan kasance a cikinta wajen tafiyar da al'amurana na siyasa a nan gaba."

A kwanakin baya, lokacin tattaunawarsa da kafar talabijin ta Arise, El-Rufa'i ya koka kan cewa "jam'iyyar APC ta sauka daga kan manufifin da aka ƙirƙire ta a kai."

Waɗanne hujjoji El-Rufa'i ya bayar?

Sanarwar da ya fitar ta bayyana cewa: "Abubuwan da suka faru a shekaru biyu da suka gabata sun tabbatar min da cewa masu iko da jam'iyyar a halin yanzu ba su da aniyar amincewa ballantana su maganace lalurar da jam'iyyar ta faɗa ciki.

"A ɓangarena na yi ƙoƙarin janyo hankali a ɓoye da kuma baya-bayan nan a bayyane game da inda jam'iyyar ta dosa.

"Saboda haka a wannan lokaci na yanke shawarar cewa ya zama wajibi na nemi wani wurin na daban a ƙoƙarina na tabbatar da manufofina na kawo cigaba."

Tsohon gwamnan ya kuma bayyana irin ƙoƙarin da ya ce ya yi ga jam'iyyar domin ganin ci gabanta, sai dai duk da haka a yanzu ta juya masa baya.

"Na bauta wa jam'iyyar APC kuma na ba ta gudumawar da ta dace wajen samun nasara, amma na fahimci cewa jam'iyyar ta bauɗe daga hanya, inda ta bar ni ina tunanin yadda za a cimma manufofin iyayen da suka kafa ta.

"A matsayina na ɗan jam'iyya mai biyayya gare ta, na taimaka wajen samun nasarar jam'iyyar a 2015 da 2019 da kuma 2023... Waɗannan (nasarori da na taimaka wa jam'iyyar ta samu) jam'iyyar ta yanzu ba ta kallon su da wani muhimmanci, inda jam'iyyara a yanzu ta jefar da manufofinta kuma ta ke wa ƴaƴanta wani kallo a cikin shekaru biyu da suka gabata. Ba zan taɓa amincewa da hakan ba."

Ya yi zargin cewa jam'iyyar ta gaza kiran taron shugabanninta na ƙasa tsawon shekaru, wanda ya ce hakan ya saɓa wa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam'iyyar.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dama dai tun bayan rashin nasarar tsallake tantancewar majalisar dattijai domin nadawa a matsayin minista a gwamnatin shugaba Bola Tinubu, al'umma da sauran masu nazari kan siyasa ke neman sanin abin da ke kunshe a cikin zuciyar dan siyasar, wanda lokaci zuwa lokaci kan tayar da kura a fagen siyasar ta Najeriya, kamar yadda ya yi a tattaunawar tasa ta baya-bayan nan.

To sai dai an kwashe tsawon lokaci cikin rashin tabbas dangane da haƙiƙanin abin da tsohon gwamnan na jihar Kaduna, ke son cimmawa a siyasance.

Gabanin sauka daga mukamin gwamna, Nasir El-Rufa'i ya ce idan ya gama wa'adin mulkinsa na shekara takwas zai koma gefe ne domin gudanar da harkokinsa na karatu da sauran abubuwa, yana mai cewa ba zai shiga harkokin gwamnati a jiha da matakin ƙasa ba kuma ba zai karɓi muƙami ba.

Ko a lokacin kamfe na shugabancin ƙasar a 2023, sai da ɗantakarar jam'iyyar APC, Bola Tinubu ya nemi El-Rufa'i da ya kawar da alƙawarinsa na ƙin shiga gwamnati.

To sai dai duk da jajircewar da ya yi wajen kafa wannan gwamnati mai ci, tafiyar ba ta je ko ina ba, sai ga shi an gan su a rana.

A karshe kuma cikin tattaunawarsa da kafar talabijin ta Arise, sai ga shi El-Rufa'in ya kammala fallasa duk wani sauran sirrin da ya rage tsakaninsa da wadanda ake wa kallon abokan siyasarsa na kut da kut.