Mutumin da ya yanke shawarar komawa rayuwa a cikin ƙogo

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Redacción
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo
- Lokacin karatu: Minti 5
Idan kana amfani da wayarka ko kuma agogo, kana duba su sau da yawa a rana domin ganin lokaci.
Lokaci yana da ɗimbin muhimmanci a rayuwar mu, shi ya sa ko zamani da yawa da suka shuɗe suka bi hanyoyi da dama wajen auna lokaci, inda suke amfani da rana domin sanin lokaci.
Sai dai, me zai faru idan muka kasa sanin muna cikin rana ko kuma dare? Kuma me zai faru idan ba mu da agogon sanin lokaci?
Wannan ita ce tambayar da wani mai nazarin ƙasa ɗan Faransa Michel Siffre ya tambayi kansa a shekarun 1960.
A shekara ta 1961, ɗan tarayyar Soviet Yuri Gagarin ya zama mutum na farko da ya taɓa balaguro zuwa sararin samaniya.
Me zai faru idan ɗan'adam ya ɗauki tsawon lokaci a sararin samaniya? Siffre ya yi ajiyar zuciya. Ta yaya zai shafi yanayin barcin mu?
Domin amsa wannan tambaya, maimakon balaguro zuwa sararin samaniya, shiga cikin ƙasa Siffre ya yi.
Mutumin ƙogo
Siffre, wanda ya mutu ranar 25 ga watan Agustan 2024 a birnin Nice na Faransa, ya kasance masani wanda ya yi nazari kan yadda ƙogo yake.
A 1962, lokacin yana da shekara 23, ya gudanar da wani gagarumin bincike kan tasirin lokaci a jikin halittu.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya zauna cikin ƙogo mai nisan mita 130 na aƙalla watanni biyu shi kaɗai tare da fitila irin ta masu haƙar ma'adinai domin ya samu haske, inda ya riƙa amfani da hasken wajen samun damar dafa abinci, yin karatu da kuma rubutu a takardarsa.
"Na yanke shawarar yin rayuwa kamar ta dabbobi, ba tare da agogo ba kuma cikin duhu, ba tare da na san lokaci ba," kamar yadda ya bayyana a wata tattaunawa da mujallar Cabinet a 2008.
Siffre ya gudanar da bincikensa ne ƙarƙashin manyan tsaunuka masu ɗauke da dusar ƙanƙara.
"Na kafa tawaga a bakin shiga ƙogon. Na yanke shawarar cewa zan kira su idan na tashi, bayan cin abinci kuma daf kafin kwanciya bacci. Tawaga ta ba ta da ikon kira na, saboda kada na san wani lokaci ne a waje," in ji shi.
Ta wannan hanyar, ya iya gano cewa ɗan'adam na da tamkar "lokaci na halitta".
Sai dai, abin mamaki da binciken shi ne agogon ba ya aiki na sa'o'i 24 a rana, kamar yadda yake a cikin rayuwar mu ta yau da kullum.
Lokaci
A tsawon makonni takwas da ya shafe cikin ƙogon, Siffre ya ci abinci da kuma yin bacci ne kaɗai lokacin da yana ji haka a jikinsa.
Ƙari kan faɗa wa tawagar abin da ya yi a kowane lokaci, masanin kimiyyar ya yi wasu abubuwa biyu: Auna gwiwar hannunsa da kuma ƙirge daga 1 zuwa 120.
Ƙirgen ne ya kai ga yin wani gagarumin bincike.
Burin Siffre shi ne ƙirge zuwa 120, inda yake shafe daƙika ɗaya a kowace lamba, yayin da tawagarsa ke ƙirga lokacin.
Ta haka ne suka gano cewa masana kimiyya na ajiye da bayanai na lokaci a hankali.
"Na shafe minti biyar wajen kirge zuwa 120."

Asalin hoton, Getty Images
Batun cewa lokaci a cikin ƙogo na tafiya kaɗan-kaɗan ya tabbatu lokacin da Siffre ya fito.
Watanni biyu sun wuce, amma masanin kimiyyar ya ce wata ɗaya ne.
"An yanke min lokaci zuwa rabi," in ji shi.
Sa'o'i 48
Binciken Siffre ya gano cewa, ba tare da asalin lokaci da muke amfani da shi ta hanyar gano fitar rana da kuma faɗuwarta ba, jikin mu na nuna cewa muna da wani agogo wanda yake tafiya ko kuma zagayawa a sa'a 48.
Hakan ya tabbatu ta hanyar wasu bincike da ɗan Faransar ya yi a tsawon rayuwarsa a duniya, ya yi amfani da kansa da kuma wasu mutane domin yin gwaji.
Bayan fita daga ƙogon a 1962 - Siffre ya ƙara gudanar da bincike a wasu ƙogo-ƙogo har biyar tare da ƴan sa-kai (ciki har da wata mata), inda suka shafe tsawon watanni uku zuwa shida.
Ya lura cewa kowa yana da agogonsa da ke aiki sa'a 48.
"Sun shafe sa'a 36 suna aiki ba ƙaƙƙautawa, sai kuma baccin sa'a 12 zuwa 14," in ji shi.
"Bayan yin wancan bincike, sojojin Faransa sun yi min kyautar maƙudan kuɗaɗe. Suna son na yi nazari kan yadda soja zai iya ninƙa aikinsa idan baya bacci," kamar yadda ya faɗa wa mujallar Cabinet.
Ita ma ma'aikatar tsaron Faransa ta nuna sha'awa kan binciken saboda wani dalili: ta ƙaddamar da shirin nukiliya na ruwa kuma suna son sanin yadda zai shafi lafiyar masu ninƙaya da ke aiki na tsawon lokaci cikin ruwa.
Ba su kaɗai ne suka nuna sha'awa ba. Hukumar kula da sararin samaniya ta Amurka NASA, ita ma na son sanin tasirin balaguro zuwa sararin samaniya na tsawon lokaci.

Asalin hoton, Getty Images
Amurka ta ɗauki nauyin binciken Siffre a shekara ta 1972, shekara goma bayan zamansa na farko a ƙogo, inda ya shafe tsawon lokaci yana bincike a ƙasar.
Burinsa shi ne shafe watanni shida a wani ƙogo kusa da Del Rio, a jihar Texas.
"Ina da sha'awar yin nazari kan tasirin shekaru a kan amfani da tunani don sanin lokaci. Tsarina shi ne gudanar da bincike bayan shekara goma ko 15 don ganin ko an samu sauyin yadda ƙwaƙwalwata ke gane lokaci," in ji shi.
Ya bayyana cewa yana son fayyace shakkun abin da ya sa "dukkan mutane ke da baccin sa'a 48 da kuma tashi, amma ban da ni."
Daga ƙarshe, binciken ya laƙume kwanaki 205 (kusan watanni bakwai). Ba zan faɗi bambancin da ke tsakanin waɗannan tsawon kwanaki da kuma kwanakin da ba su wuce sa'a 24 ba," in ji shi.
"Na shafe sa'a 36 ina aiki babu tsayawa, sai kuma baccin sa'a 12.
"Wasu lokuta ina baccin sa'a biyu ko kuma sa'a 18, kuma ban ga wani bambanci ba."
"Ina tunanin wannan abu ne da dukkan mu za mu yaba," in ji Siffre.
"Matsalar amfani da tunani don sanin lokaci ne. Matsalar ɗan'adam ne. Mene ne lokaci? Ba mu sani ba."











