KAI TSAYE, Arteta ya ce watakila Timber ya warke kafin Champions League

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 11 zuwa 16 ga watan Mayun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Mbappe da Dambele za su wakilci Faransa a gasar kofin duniya 2026, Gasar kofin duniya

    Kylian Mbappe da mai riƙe da ƙyautar Ballon d'Or, Ousmane Dembele, suna cikin jerin ƴan wasa 26 da za su wakilci Faransa a gasar cin kofin duniya a 2026.

    Olivier Giroud ne kan gaba a yawan ci wa tawagar ƙwallaye fiye da Mbappe, inda yake da 57 a raga, shi kuwa ɗan ƙwallon Real Madrid yana da 56.

    Ana sa ran Mbappe ne zai ci gaba da ƙyaftin ɗin tawagar, wanda ke jinya da bai samu damar buga El Clasico ba da Barcelona ta yi nasarar cin Real Madrid 2-0 ta lashe La Liga kuma na biyu a jere.

    Dembele kuwa ya ci ƙwallo 35 tda lashe Champions League tare da Paris Saint-Germain a kakar da ta gabata, lamarin da ya sa ya zama ɗan wasan Faransa na biyu a wannan ƙarni da ya lashe Ballon d'Or. Duk da haka, har yanzu bai ci ƙwallo ba a gasar kofin duniya duk da kasancewa cikin tawagar gasar biyu da suka gabata.

    Michael Olise na Bayern Munich da kuma abokin wasan Dembele a PSG, Desire Doue, suna cikan jerin ƴan wasan a gurbin masu cin ƙwallaye, yayin da ɗan wasan Manchester City Rayan Cherki da kuma mai tsaron bayan Arsenal, William Saliba ke cikin ƴan wasa bakwai daga Premier League.

    Lucas Hernandez da ɗan wasan tsakiya N'Golo Kante da Mbappe da Dembele suna cikin ragowar tawagar Faransa da ta lashe kofin duniya a 2018.

    Deschamps, wanda ya kai Faransa wasan ƙarshe a kofin duniya sau biyu a jere, ya gayyaci wasu ƴan wasa da aka yi mamaki, wanda daga wannan gasar zai yi ritaya a matsayin kocin Faransa.

    Ba a saka ɗan wasan Real Madrid Eduardo Camavinga da na Tottenham, Randal Kolo Muani cikin waɗanda aka sanar ba, duk da cewa suna cikin tawagar 2022.

    Haka kuma mai tsaron ragar PSG, Lucas Chevalier bai samu gurbi ba, inda mai tsaron ragar Lens, Robin Risser wanda bai taɓa bugawa Faransa wasa ba tare da Brice Samba suna matsayin masu taimaka wa Mike Maignan.

    Hugo Ekitike na Liverpool, wanda ya samu mummunan raunin a watan Afrilu na jinya, har karshen kakar bana, ba zai buga gasar kofin duniya ba.

    Faransa za ta fara wasanninta da Senegal a New Jersey ranar 16 ga watan Yuni, sannan ta kara da Iraq ranar 22 ga watan Yuni da kuma Norway ranar 26 ga watan Yuni a rukuni na I.

    Tawagar ƴan wasan Faransa da za su buga kofin duniya a 2026

    Masu tsaron raga: Mike Maignan (AC Milan), Robin Risser (Lens), Brice Samba (Rennes)

    Masu tsaron baya: Lucas Digne (Aston Villa), Malo Gusto (Chelsea), Lucas Hernandez (Paris St-Germain), Theo Hernandez (Al Hilal), Ibrahima Konate (Liverpool), Maxence Lacroix (Crystal Palace), Jules Kounde (Barcelona), William Saliba (Arsenal), Dayot Upamenaco (Bayern Munich)

    Masu buga tsakiya: N'Golo Kante (Fenerbache), Manu Kone (Roma), Adrien Rabiot (AC Milan), Aurelien Tchouameni (Real Madrid), Warren Zaire-Emery (Paris St-Germain)

    Masu cin ƙwallaye: Maghnes Akliouche (Monaco), Bradley Barcola (Paris St-Germain), Rayan Cherki (Man City), Ousmane Dembele (Paris St-Germain), Desire Doue (Paris St-Germain), Michael Olise (Bayern Munich), Kylian Mbappe (Real Madrid), Jean-Phillipe Mateta (Crystal Palace), Marcus Thuram (Inter Milan)

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  2. Arteta ya ce watakila Timber ya warke kafin Champions League, Champions League

    Kocin Arsenal, Mikel Arteta, ya ce akwai “yiwuwar” Jurrien Timber zai murmure kafin wasan ƙarshe a Champions League, yayin da ɗan wasan ke jinya.

    Sai dai Ben White ya gama buga sauran wasannin bana, sakamakon raunin da ya ji, yayin da Timber ya shafe watanni biyu baya taka leda saboda jinya.

    Waɗannan raunuka sun jefa Arsenal cikin matsala a gefen dama a tsaron baya kafin wasannin ƙarshe a Premier League da Burnley da kuma Crystal Palace, tare da babban wasan gasar zakarun Turai da Paris Saint-Germain ranar 30 ga Mayu a Budapest.

    Hakan na iya sa Cristhian Mosquera ko kuma Riccardo Calafiori su maye gurbinsu.

    Arsenal tana da saura wasa biyu kacal ta lashe kofin Premier League na farko tun shekarar 2004 idan har ta yi nasara a jere.

    Idan Arsenal ta doke Burnley ranar Litinin, hakan zai tilasta sai Manchester City ta yi nasara a Bournemouth daga nan a fayyace mai kofi a ranar karshe.

    Arteta ya bayyana cewa bai kalli wasan da City ta doke Palace 3-0 a ranar Laraba ba, saboda yana halartar liyafa tare da babban mai tallafa wa ƙungiyar, Emirates.

    Da aka tambaye shi ko yana jin kamar ya kusa taɓa kofin Premier League, Arteta ya ce:

    “Ina jin muna da wata dama ranar Litinin domin matsawa kusa da kofin. Wannan shi ne kawai abin da nake tunani.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  3. Colombia ta bayyana ƴan wasa 55 na wucin gadi domin gasar cin kofin duniya, Gasar kofin duniya

    Kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta Colombia, Nestor Lorenzo, ya bayyana jerin ƴan wasa 55 na wucin gadi domin FIFA World Cup a ranar Alhamis.

    Jerin yan ƙwallon sun haɗa da fitattun kamar Luis Diaz da ƙyaftin, James Rodriguez, tare da wasu sunaye da suka ba mutane mamaki irin su Sebastian Villa da Juan Guillermo Cuadrado.

    Lorenzo zai rage su zuwa ƴan wasa 26 kafin ranar 29 ga Mayu.

    Kocin ya nuna cikakken goyon baya ga James duk da ƙarancin lokacin da ya samu yana taka leda a wannan kakar, yana cewa ɗan wasan “har yanzu muhimmi ne a gare mu.”

    An sanya Colombia a rukuni na K, inda za ta kara da Uzbekistan da Portugal da kuma Jamhuriyar Congo a gasar da Amurka da Mexico da kuma Canada.

    Kafin fara gasar, tawagar Colombia za ta buga wasannin sada zumunta da Costa Rica a Bogota sannan ta fafata da Jordan a San Diego.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  4. Mitoma ya ji raunin da ya sa ya kammala wasannin kakar bana, Brighton

    Kaoru Mitoma ba zai samu buga sauran wasanni biyu na ƙarshen kakar bana, kuma akwai yiwuwar ba zai buga gasar cin kofin duniya ba.

    Ɗan wasan tawagar Japan ya samu raunin ne a karawar da Brighton ta doke Wolverhampton Wanderers 3-0 a ƙarshen makon da ya gabata.

    Kocin Brighton, Fabian Hurzeler, ya shaida wa manema labarai kafin tafiyar su zuwa Elland Road domin fafatawa da Leeds United a ranar Asabar cewa Mitoma ya ji raunin da ba zai buga wasa biyun da suka rage ba a bana a Premier Leahue.

    Haka kuma kociyan ya kara da cewa Mats Wieffer da Diego Gomez suna fama da raunuka, amma Hurzeler ya ce akwai yiwuwar su buga wasan Elland Road, yayin da Brighton ke ƙoƙarin neman gurbin zuwa gasar zakarun Turai ta baɗi.

    Live

    Asalin hoton, Getty Images

  5. , Daga Jaridu

    Bayern Munich ta cimma yarjejeniya da Anthony Gordon kuma ta fara tattaunawa da Newcastle United kan sayen ɗan wasan gaban na Ingila, mai shekara 25. (Bild)

    Tsohon ɗan wasan Ingila Mason Greenwood, mai shekara 24, yana shirin ci gaba da zama a Marseille duk da cewa ana alaƙanta shi da manyan ƙungiyoyin Turai kamar Juventus, da Borussia Dortmund da Atletico Madrid. (Sun)

    Chelsea da Manchester United sun sanya ɗan wasan gaban Real Sociedad ɗan ƙasar Sifaniya Ander Barrenetxea, mai shekara 24, a jerin sunayen waɗanda za su yi zawarci a wannan bazarar. (Marca)

    Manchester United ta shirya zawarcin ɗan wasan tsakiyar Nottingham Forest ɗan ƙasar Ingila Elliot Anderson, mai shekara 23. (Give Me Sport)

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  6. Union Saint-Gilloise ta lashe Belgium Cup na biyu a cikin kaka uku, Belgium CUP

    Union Saint-Gilloise ta lashe Belgian Cup a karo na biyu cikin shekaru uku, bayan da ta doke Anderlecht da ci 3-1 bayan ƙarin lokaci.

    A wasan da aka fafata a ranar Alhamis, Union ta buƙaci ƙarin lokaci domin tabbatar da nasara bayan an tashi 1-1 cikin mintuna 90 na wasan.

    Ƙungiyar ta fara cin kwallo a minti na 74 ta hannun ɗan wasan tawagar Argentina, Kevin Mac Allister, bayan da ta mamaye wasan gaba ɗaya.

    Sai dai an soke ƙwallon da ƙyaftin ɗinta ɗan asalin Ingila, Christian Burgess, ya ci da cewar an yi satar gida, bayan da VAR ta bibiyu abinda ya faru kafin cin wallon.

    Anderlecht ta farke a minti na 80 ta hannun Mihajlo Cvetkovic daga bugun tazara, duk da cewa magoya bayanta sun jefa abun da yake sa hayaki cikin fili wanda ya sa aka dakatar da wasan na ɗan lokaci saboda rashin ganin filin sosai.

    A ƙarin lokaci kuwa, ƴan wasan da aka sauya suka zama jarumai — Mohammed Fuseini da Kevin Rodriguez — sune suka ci ƙwallaye cikin mintuna 10 na farkon ƙarin lokaci.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  7. Kerr za ta bar Chelsea a karshen kakar bana, Ƙwallon kafar mata

    Sam Kerr — wadda ita ce mafi yawan cin ƙwallo a tarihin Women's Super League mai takaleda a ƙungiyar mata ta Chelsea — za ta bar stamford Bridge bayan kwantiraginta ya ƙare a wannan bazarar.

    Kerr mai shekara 32 ta zura ƙwallaye 115 a wasa 157 da ta bugawa Chelsea, kuma wasanta na ƙarshe zai kasance a gida da Manchester United ranar Asabar.

    Ƴar wasan tawagar Australia, wadda ta koma Chelsea a watan Nuwamban 2019, ta taimaka wa ƙungiyar lashe kofunan WSL guda biyar, FA Cup uku, League Cup uku da kuma FA Community Shield.

    Kerr ta lashe ƙyautar takalmin zinariya sau biyu, sannan aka zaɓe ta a matsayin Gwarzuwar ƴar wasan WSL a shekarar 2022, tare da lashe kyautar Professional Footballers' Association ta gwarzuwar ƴar wasan da magoya baya suka zaɓa a shekarar 2021 da kuma 2022.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  8. Sinner na kara yin fice a gasar ƙwallon tennis a duniya, Ƙwallon tennis

    Jannik Sinner ya karya tarihin Novak Djokovic na yawan cin wasanni a jere a gasar ATP Masters 1000, bayan da ya samu nasara ta 32 a jere da kaiwa wasan daf da ƙarshe a Italian Open.

    Ɗan wasan Italy wanda ke matsayi na ɗaya a duniya ya yi nasarar doke ɗan wasa mai matsayi na 12, Andrey Rublev, da ci 6-2, 6-4.

    Sinner na ci gaba da fafutukar zama mutum na biyu bayan Djokovic da zai lashe dukkanin gasar Masters 1000 guda tara — wato mafi girman matakin gasar tennis bayan Grand Slam.

    Ɗan wasan mai shekara 24 yana nuna karin samun gogewa, kafin fara French Open ranar 24 ga watan Mayu, wanda shi ne kawai babban kofin da ya rage masa domin cika tarihin lashe dukkanin Grand Slam a rayuwarsa.

    Haka kuma ya haɗu da fitaccen ɗan wasa, Rafael Nadal na ƙasar Spain a matsayin mutum na biyu da suka kai wasan kusa da na ƙarshe a dukkanin gasar Masters 1000 guda biyar a kakar wasa guda.

    A wasan gaba, Sinner zai kara da ɗan ƙasar Russia Daniil Medvedev ko kuma ɗan wasan Spain da aka ba damar shiga daga baya, Martin Landaluce, domin neman gurbin wasan ƙarshe.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  9. PSG ce ta lashe Ligue 1 na bana na biyar a jere, PSG

    Paris Saint-Germain ta lashe Ligue 1 na bana karo na 14 a tarihinta — kuma karo na biyar a jere — bayan ta doke babbar abokiyar hamayyarta Lens.

    PSG na buƙatar kunnen doki kawai domin tabbatar da kofin kakar nan, kasancewar Lens na baya da maki shida.

    Kwallayen da Khvicha Kvaratskhelia da wanda ya maye gurbinsa, Ibrahim Mbaye, suka ci a filin Stade Bollaert-Delelis suka tabbatar wa PSG da kofin saura wasa ɗaya a kammala kakar nan.

    PSG ita ce ƙungiyar da ta fi kowacce lashe Ligue 1, yayin da Saint-Etienne ke biye da kofuna 10.

    PSG ta lashe Ligue 1 sau 12 cikin shekaru 14 da suka gabata, kuma za ta je wasan ƙarshe a lig da abokiyar hamayyarta Paris FC a ranar Lahadi.

    Haka kuma za ta kara da jagorar Premier League, wato Arsenal, a wasan ƙarshe a Champions League ranar 30 ga watan Mayu yayin da take neman kare kambunta na Turai.

    A gefe guda kuma, Lens za ta fafata da Nice a wasan ƙarshe a Coupe de France ranar 22 ga watan Mayu.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  10. Carrick na cikin ƴan takarar gwarzon kocin Premier League na bana, Manchester United

    Kocin riƙon kwarya na Manchester United, Michael Carrick, ya shiga cikin jerin ƴan takarar ƙyautar gwarzon kociyan Premier League na shekarar nan.

    Carrick, wanda ya jagoranci wasa 15 tun bayan da ya maye gurbin Ruben Amorim a watan Janairu, yana takara tare da kocin Arsenal, Mikel Arteta da kuma na Manchester City, Pep Guardiola, wadanda ke fafatawa wajen kokarin lashe kofin bana.

    Sauran waɗanda ke takara har da kocin Bournemouth, wanda zai bar aikin horar da ƙungiyar a bana, Andoni Iraola, da kuma na Brentford Keith Andrews, tare da kocin Sunderland Regis le Bris.

    A bangaren gwarzon ɗan wasa na shekara nan kuwa, daga cikin ƴan wasa takwas da za a zaɓi gwani akwai uku daga Arsenal — David Raya da Gabriel da kuma Declan Rice — tare da ƴan wasan Manchester City biyu Antoine Semenyo da kuma Erling Haaland.

    Haka kuma an saka kyaftin ɗin Manchester United, Bruno Fernandes da ɗan wasan Brentford Igor, Thiago da kuma na Nottingham Forest, Morgan Gibbs-White cikin jerinsu.

    A bangaren ƙyautar fitatcen Matashin Ɗan Wasa na Shekara — ga ƴan wasan da shekarunsu ba su wuce 23 ba a farkon kakar — akwai ɗan ƙwallon West Ham United, Mateus Fernandes da na Newcastle United Lewis Hall da na Brentford, Michael Kayode da kuma ɗan wasan Manchester United Kobbie Mainoo.

    Ƴan wasan Bournemouth, Junior Kroupi da Alex Scott da na Manchester City, Rayan Cherki da Nico O'Reilly, su ma suna cikin jerin takwas da za a zaɓi ɗaya.

    Za a tantance waɗanda za su yi nasara ne ta hanyar haɗa ƙuri’un jama’a da kuma ra’ayoyin kwararrun masana ƙwallon ƙafa.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  11. , Daga Jarida

    Chelsea da Galatasaray na sha'awar sayen ɗan wasan gaban Ingila Jonathan Rowe mai shekara 23 daga Bologna. (Gazzetta dello Sport)

    Ɗan wasan gaban Jamus Nick Woltemade ba ya jin daɗin zamansa a Newcastle kuma Atletico Madrid na cikin ƙungiyoyin da ke sanya ido kan lamarin ɗan wasan mai shekara 24. (Bild)

    Marseille ba za ta yi amfani da zaɓin da ta ke da shi na ɗaukar ɗan wasan baya na Faransa Benjamin Pavard mai shekara 30 ba, wanda a halin yanzu yake zaman aro daga Inter Milan. (Bild)

    Tottenham na neman ɗan wasan bayan Sassuolo da Bosnia-Herzegovina Tarik Muharemovic, mai shekara 23. (Caught Offside)

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  12. Ancelotti zai tsawaita kwantiragi a Brazil, aikin koci na karshe da zai yi, Brazil

    Kocin Brazil, Carlo Ancelotti, ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa akwai yiwuwar ya tsawaita kwantiraginsa har zuwa shekarar 2030, duk da cewa wannan na iya zama aikinsa na ƙarshe a matsayin koci.

    Ancelotti ya je Brazil ne da tarihin lashe Champions League sau biyar a matsayin koci, tare da ɗaukar kofunan lig a manyan ƙasashen Turai biyar, da kuma yin suna wajen iya sarrafa manyan ƴan wasa cikin nutsuwa.

    Sai dai shekara guda bayan karɓar ragamar tawagar Brazil, ya fahimci cewa wannan aiki ya bambanta — ba kamar yadda ake shan wahalar horar da kungiya a kullum ba, sai dai cike yake da matsin lamba ga al’ummar da ke matukar ƙaunar ƙwallon ƙafa.

    A yanzu, ɗan ƙasar Italy yana jin daɗin aikin horar da tawagar ƙasa, kuma ya ce batun tsawaita kwantiraginsa har zuwa 2030 ya kusa kammala.

    Ancelotti ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekara ɗaya ne lokacin da ya zama kocin Brazil a watan Mayun bara, amma yanzu ana sa ran zai ci gaba da aikin bayan FIFA World Cup a Amurka da Canada da kuma Mexico..

    Rahotanni sun ce Ancelotti na fuskantar matsin lamba wajen zaɓen tawagar Brazil da zai da su kofin duniya, musamman saboda yawaitar raunuka da kuma rashin tabbas kan lafiyar Neymar.

    Kocin ya kuma jaddada muhimmancin aikin horaswa, yana cewa dole ne koci ya iya zama jagora, mai ba da shawara, da kuma wanda ƴan wasa za su iya yarda da shi.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  13. An dakatar da wasan tennis a Rum, saboda hayaki da ya turnuke sararin samaniya, Inter Milan

    An dakatar da wani wasa a Italian Open na kusan minti 20 saboda wani hayaƙi da ya turnuke sararin samaniya, sakamakon Coopa Italia da Inter Milan ta lashe a Stadio Olimpico.

    A gasar ta tennis ɗan kasar Italy, Luciano Darderi ya samu nasara a kan ɗan ƙasar Sifaniya, Rafael Jodar da kaiwa karawar daf da karshe a lokacin da agogo ke cewa ƙarfe biyu na dare agogon Foro Italico.

    Jodar mai shekara 19 yana cin wasan 6-5 a zagayen farko lokacin da hayaƙin ya mamaye babban filin wasan sakamakon murnar nasarar da Inter ta ci 2-0 a kan Lazio, inda filin wasan yake kusan mita 500 kacal daga wajen da ake buga gasar tennis.

    An dakatar da wasan saboda ba a gani sosai a cikin fili, sannan hayaƙin ya kuma kawo matsala ga tsarin na’urar tantance layin ƙwallo ta lantarki.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  14. , Daga Jarida

    Ɗan wasan gaba na Ivory Coast Yan Diomande, wanda rahotanni suka ce farashinsa zai kai fam miliyan 80, na jan hankalin Chelsea da Liverpool amma ɗan wasan mai shekara 19 ba zai yi gaggawar barin RB Leipzig ba. (The Athletic)

    Leeds na zawarcin ɗan wasan gaban Belgium Lois Openda, wanda ke shirin komawa Juventus daga RB Leipzig, amma kulob ɗin na Italiya na fatan cefanar da ɗan wasan mai shekara 26, sakamakon rashin tagomashi da ya samu a zaman aron da ya ke yi a ƙungiyar. (TeamTalk)

    Manchester United na neman matsuguni na dindindin ga golan Kamaru Andre Onana, mai shekara 30, wanda a halin yanzu ya ke zaman aro a ƙungiyar Trabzonspor ta Turkiyya. (ESPN)

    Har ila yau United a shirye take ta miƙa sabuwar yarjejeniya ga mai tsaron gida Tom Heaton, mai shekara 40. (Caught Offside)

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  15. Fifa ta yi haɗin gwiwa da kamfanin zuba jari na Saudiyya, Gasar kofin duniya

    Saudi Arabia ta hannun Asusun Zuba Jari na Ƙasa, wato Public Investment Fund (PIF), zai tallafa gasar cin kofin duniya da za a gudanar a bana.

    Masu shirya gasar, FIFA, ya sanar a ranar Alhamis cewa an cimma yarjejeniya da kamfanonin PIF guda biyu — Savvy Games Group da Qiddiya City — domin yankunan Arewacin Amurka da Asiya.

    Wannan yarjejeniya ta ƙara gina alaƙar da aka fara tun gasar FIFA Club World Cup, tare da ƙarfafa haɗin kai kafin Saudi Arabia ta karɓi baƙuncin FIFA World Cup.

    Sabuwar yarjejeniyar ta zo ne makonni biyu bayan PIF ta sanar da kawo ƙarshen tallafinta ga LIV Golf a ƙarshen shekarar nan.

    PIF ta bayyana cewa ci gaba da zuba kusan fam biliyan 4 cikin LIV Golf bai dace da sabon tsarin dabarunta na zuba jari ba.

    A wata sanarwa da FIFA ta fitar, ta ce haɗin gwiwar na da nufin bunƙasa ƙwallon ƙafa a duniya daga matakin yara har zuwa na ƙwararru, ƙara kusanci da magoya baya, da samar da sabbin damar shiga harkar wasan.

    Sanarwar ta ƙara da cewa: “A yayin gasar, PIF da kamfanoninta za su samar da abubuwan tunawa na musamman tare da ƙaddamar da sababbin hanyoyin haɗa magoya baya da al’ummar ƙwallon ƙafa a babban dandalin wasan duniya.”

    Haka kuma sanarwar ta bayyana Savvy Games Group a matsayin “babban jagoran Saudiyya a harkar wasanni na bidiyo da esports a duniya”, yayin da Qiddiya City aka bayyana shi a matsayin “babban birnin nishaɗi, wasanni da al’adu na nan gaba” a ƙasar.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  16. Inter Milan ta lashe kofi biyu a bana karon farko bayan shekara 16, Inter Milan

    Inter Milan ta lashe kofi biyu a gasar cikin gida a karo na farko cikin shekaru 16, bayan da ta doke Lazio da ci 2-0 a wasan ƙarshe a Coppa Italia.

    Ƙungiyar da Cristian Chivu ke jan ragama ta riga ta ɗauki kofin Serie A na kakar nan na 21 jimilla a farkon wannan watan, saura wasanni uku a kare kakar.

    Ƙwallon da Adam Marusic ya ci gida da kuma wadda Lautaro Martinez ya zura a raga suka taimaka wajen tabbatar wa Inter lashe kCoppa Italia na 10 a filin Stadio Olimpico a ranar Laraba.

    Karo na ƙarshe da Inter ta lashe kofunan gida biyu, shi ne a zamanin nasarar kofuna uku tare da Jose Mourinho a shekarar 2010 a lokacin Chivu ya kasance cikin ƴan wasan tawagar.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  17. Wasannin mako na 37

    Liv

    Asalin hoton, BBC Sport

  18. Yadda aka taka leda a karawar, Manchester City 3-0 Crystal Palace

    Liv

    Asalin hoton, BBC Sport

  19. An tashi wasa, Manchester City 3-0 Crystal Palace

    An tashi wasan kuma yanzu saura wasa biyu a kammala kakar nan, har yanzu Arsenal ce ta daya da kuma Manchester City ta biyu.

    Tuni dai Wolverhampton da Burnley suka faɗi daga gasar bana.

  20. , Manchester City 3-0 Crystal Palace

    Phil Foden na Manchester City ne ya zama gwarzon dan wasan a karawar ta Premier Laegue.