Mece ce makomar takarar Gwamnan Rivers Sim Fubara?

Asalin hoton, RSGH Media
Da alama kallo zai sake komawa sama a jihar Rivers, domin alamu sun fara nuna za a sake ɓarje gumi a tsakanin Gwamnan jihar, Sim Fubara da Ministan Abuja Nyesom Wike kan takarar gwamnan jihar a jam'iyyar APC.
Gwamnan jihar, Fubara ya halarci taron tantace ƴan takarar gwamnoni , inda rahotanni suka nuna ya fito daga wajen tantancewar ransa a ɓace, duk da bai bayyana wa ƴan jarida dalilin ɓacin ran ba.
Sai dai bayan an tantance shi, wani na hannun damar Wike, Kingley Chinda, wanda shi ne jagoran ƴan hamayya a majalisar wakilan Najeriya ma ya halarci tantancewar domin tsayawa takarar gwamnan jihar.
Wannan ya sa aka shiga mamaki, ganin har zuwa lokacin da aka gan shi a wajen tantancewar, ana masa kallon ɗan jam'iyyar PDP ne, inda yake riƙe da kujerar shugaban marasa rinjaye, duk da cewa an san na kusa da ministan ne sosai.
Har yanzu dai ministan na Abuja na cikin jam'iyyar PDP, inda yake cigaba da iƙirarin cewa tsagin da ke tare da shi ne ya samu nasara a hukuncin kotun ƙolin Najeriya.
Babban sakataren APC, Ajibola Basiru wanda shi ne ya jagoranci zaman tantacewar a madadin shugaban jam'iyyar, Nentawe Yilwatda ya ce nan gaba kaɗan za su bayyana sakamakon tantancewar.
Yanzu dai da alama Wike ba ya so Fubara ya sake tsayawa takara a APC, ballantana ya samu tikitin shiga zaɓen, shi kuma Fubara na so ya sake tsayawa takara domin komawa wa'adi na biyu.
Shin Fubara na da lokaci?
A ranar 6 ga Mayu ne jam'iyyar APC ta kamala sayar da fom ɗin takararta, wanda ta fara sayarwa a ranar 28 ga watan Afrilu.
An gudanar da tantance ƴan takarar gwamna ne a tsakanin 8 ga watan Mayu zuwa 10 ga watan Mayu, sannan a ranar 11 ga watan Mayu ne za a fitar da sakamakon tantancewar, sannan a saurara ƙorafe-ƙorafen tantancewar daga 12 ga watan Mayu zuwa 13.
A sabuwar dokar zaɓen Najeriya, an tsara fitar da ƴantakara ne ko dai ta hanyar ƴar tiƙe ko maslaha. Ita jam'iyyar APC ta tsara gudanar da zaɓen fitar da ƴan Takara ne kamar haka:
- Ƴanmajalisar wakilai 15 ga Mayu
- Sanatoci 18 ga Mayu
- Majalisar jiha 20 ga Mayu
- Gwamnoni 21 ga Mayu
- Shugaban ƙasa 23 ga Mayu.
Sannan Hukumar INEC ta sanya ƙa'idar cewa dole a gudanar tare da kammala duk abubuwan da suka shafi zaɓen fitar da ƴantakara a tsakanin 23 ga watan Afrilu zuwa 30 ga watan Mayu.
Sannan kuma za a gudanar da babban zaɓen na shugaban ƙasar da majalisun tarayya ne a ranar 16 ga Janairun 2027, sai kuma na gwamnoni da majalisar jiha a ranar 6 ga Fabrailun 2027.
Wannan ya sa wasu suke ganin tamkar gwamnan ba shi da lokacin ɓatawa, inda tuni wasu suka fara da kira da ya tsallake zuwa wata jam'iyyar ya tsaya takara.
Babu ruwana da tantancewar - Wike
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana shi babu abin da ya shafe shi da tantancewar da ake yi wa ƴan takarar gwamnan.
A wata sanarwa da mai ba shi shawara kan kafofin sadarwa na zamani Lere Olayinka ya fitar, ya ce shi ba ɗan APC ba ne, don haka ba zai sa baki ba a abin da ke faruwa game da batun.
"Ni ba ɗan APC ba ne, don abin da ke faruwa a wajen tantancewar bai dame ni ba. Ko da sun fitar da sakamakon tantancewar ni babu ruwa. Me zai sa in yi magana a abin da bai shafe ni ba?"
Rikicin Wike da Fubara

Asalin hoton, Bayo Onanuga
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A watan Yunin bara ne Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gana da Ministan Abuja, Nyesom Wike da gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara wanda a lokacin aka dakatar da shugaban majalisar jihar, Martins Amaewhule wanda shi ma a lokacin aka dakata, inda shugaban ya jagoranci sulhu da sasanci a tsakaninsu.
Bayan ganawa da shugaban ƙasar, jagororin siyasar biyu sun yi jawabai masu nuna alamun cewa a shirye suke su mayar da wuƙaƙensu cikin kube.
Ministan Abuja kuma tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike ya bayyana a lokacin cewa, "mun amince mu yi aiki tare. Yanzu komai ya wuce. Da ma asali mun fito ne daga gidan siyasa ɗaya, kuma a matsayinmu na ƴan'adam, muna samun saɓani, sannan an yi sulhu. Yanzu komai ya wuce, babu wani saɓani kuma".
Rikici ya fara ne tsakanin Ministan Abuja Nyesom Wike da magajinsa, Siminalayi Fubara bayan sabon gwamna ya ɗare kan karagar mulki, inda aka fara jin ka-ce-na-ce a tsakaninsu.
Sai a lokacin zaɓen shugabannin jam'iyyar PDP na jihar saɓani ya ƙara fitowa zahiri, bayan ɓangaren Wike ya lashe zaɓukan, lamarin da masu goyon bayan gwamnan suka ce ba za ta saɓu ba, domin a cewarsu, gwamna ne jagoran jam'iyya a jihar.
Daga bisani rikicin ya sake ɗaukar sabon salo a lokacin zaɓen ƙananan hukumomin jihar, wanda aka yi a bara inda ɓangaren Wike suka ce ba za a yi ba, ɓangaren gwamna ya ce sai an yi, lamarin da ya sa aka je kotu, aka samu hukunce-hukunce mabambanta.
Daga bisani gwamnan ya dage sai an yi zaɓen, inda aka yi zaɓen sannan jam'iyyar APP wadda ake tunanin gwamna Fubara ya goya wa baya, ta lashe kujera 22 daga cikin ƙananan hukumomiN jihar guda 23.
Haka kuma rikici ya ɓarke a majalisar dokokin jihar, inda mafiya yawan majalisar, su 27 suke tare da da Wike, sauran kuma guda uku suke tare da gwamna.
A lokacin ne ƴanmajalisar na hannun damar Wike suka sanar da komawa APC, inda sauran ukun na gefen Fubara suka sanar da cewa guda 27 sun rasa kujerarsu, lamarin da aka je kotu har aka kotun ƙoli, wadda ta dawo musu da kujerarsu, sannan ta soke zaɓen ƙananan hukumomin jihar.
Sai dai kafin nan, Fubara ya gabatar da ƙudurin kasafin kuɗin jihar a gaban ƴanmajalisar da suke tare da shi, su uku, sannan ya sanya hannu a kasafin kuɗin, sannan ya rantsar da shugabannin ƙaramar hukumomin jihar, wanda aka zaɓa a zaɓen mai cike da taƙaddama.
Ana cikin haka ne Kotun Ƙoli ta soke zaɓen, sanan ta mayar da ƴanmajalisar jihar na hanun damar Wike su 27, sannan ta buƙaci a dakatar da ba Rivers kuɗin kasonta na wata-wata har sai Fubara ya sake gabatar da kasafin kuɗin jihar a gaban ƴanmajalisar mau rinjaye, lamarin da ya dawo da rikicin ɗanye.
Ana cikin wannan yanayi ne ƴanmajalisar dokokin jihar suka zargi gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa Farfesa Ngozi Odu da saɓa wa ƙa'idar aiki da kuma ƙin amfani da hukuncin kotun ƙoli.
Ƴan majalisa 26 na jihar ta Rivers sun yi waɗannan zarge-zarge ne a wasu takardun koke biyu da suka tura wa shugaban majalisar, Martin Amaewhue.
Sun ce sun ɗauki matakin nasu ne "bisa dogaro da sashe na 188 na kudnin tsarin mulkin Najeriya na 1999", wanda ya tanadi cewa dole ne a samu kashi ɗaya cikin uku na ƴan majalisa su goyi bayan koken sannan kuma a tantance ainahin laifukan.
Yunƙurin tsige gwamnan ya tayar da ƙura, inda ya sake jefa jihar cikin tashin hankali, har aka fara samun labaran fashe-fashen bututun man fetur.
A daidai lokacin da ake batun tsige gwamnan ne, Tinubu ya sanar da dakatar da gwamnan da sauran zaɓaɓɓu tare da sanya gwamnan riƙo a jihar, bayan ƙaƙaba dokar ta-ɓaci a jihar.










