Abin da APC ta ce kan matsayin Wike a jihar Rivers

Asalin hoton, BBC Pidgin
Da alama jam'iyyar APC da gwamnatinta a Najeriya, sun fara juyawa ministan Abuja, babban birnin tarayyar kasar, Nyesom Wike, baya sannan kuma sun jaddada goyon bayansu ga gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, wanda bai dade da komawa jam'iyyar ta APC daga PDP ba.
Hakan ya fara nuna yadda ake neman raba gari da ministan, sakamakon yadda ake ta bayyana fargabar kar ya zame wa jam'iyyar APC da gwamnatinta wani babban alakakai a fagen siyasar jihar.
Tun ana gunaguni da nuna gundura ta hanyar balulluba ko a kaikaice, game da yadda aka soma gajiya da tafiya irin ta angulu da kan zabo da ake yi da ministan na Abuja, asali dan jam'iyyar PDP, da gwamnatin tarayya ta jam'iyyar APC, yanzu abin ya fara fitowa fili.
Da sannu a hankali kusoshin jam'iyyar APC da mukarraban gwamnatinta suna ta jaddada rungumar dan lele wato gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, tare da nuni cewa, shi ne babban jigon jam'iyyar a jihar.
Bala Ibrahim, daraktan yada labarai na jam'iyyar APC na kasa, ya shaida wa BBC cewa idan aka dubi tsarin zababbu a jihar ta Rivers, Fubara shi ne gwamna, don haka shi ne jagoran jam'iyyar APC a Rivers.
Ya ce," Shi Wike ba dan jam'iyyar APC ba ne, kuma tun da ba dan jam'iyya ba ne ai ba yadda za a yi ya yi ruwa ya yi tsaki a cikin harkarmu ta jam'iyya."
Masana siyasa a Najeriya irinsu Farfesa Abubakar Umar Kari, da ke jami'ar Abuja, sun bayyana abin da wannan fifiko da ake nuna wa Fubara ke nufi inda ya ce abubuwa ne guda biyu.
" Na farko shi ne gasgata zaton mutane da dama cewa 'ya'yan jam'iyyar APC fa ba sa jin dadin irin kutse da wasu abubuwa da Wike ke yi, inda har ma sun fara fitowa fili suna fada inda suke masa hannunka mai sanda kan cewa ba sa kaunarsa."
"Na biyu kuma shi ne, kusan kullum tana fitowa fili cewa Wike na da babban zabi a gabansa, wato ko dai ya koma jam'iyyar APC, ko kuma ya ci gaba da zama a jam'iyyarsa ta PDP, amma kuma ya bar mukaminsa na minista. Domin idan har ya ci gaba da kasancewa minista to za a ci gaba da kalubalantarsa." In ji shi.
Yanzu dai bisa ga dukkan alamu, ministan Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, Nyesom Wike, yana cikin tsaka mai wuya a siyasance sakamakon yadda yake fama da rikici a jam'iyyarsa ta PDP, sannan kuma a jam'iyyar APC da yake yi wa aiki kuma, ana yi masa kallon wani sartse.











