Me ya janyo taƙaddama tsakanin Wike da APC?

Asalin hoton, Nyesom Wike
Zazzafar cacar-baki ta kaure tsakanin Ministan Abuja, Nyesom Wike, da Sakataren Jam'iyyar APC, Ajibola Bashiru, lamarin da ya kai ga sakataren jam'iyyar kiran Wike ya sauka daga muƙaminsa na minista, bisa hujjar cewa ba ɗan jam'iyyar APC ba ne.
Lamarin na zuwa ne bayan Wike ya gargaɗi sakataren ya tsame hannunsa daga siyasar jihar Ribas, saboda sanarwar da APC ta fitar cewa Gwamna Siminalayi Fubara ne jagora kuma shugaban jam'iyyar mai mulki a jihar.
Rikicin ya faro ne tun bayan ziyarar da sakataren APCn da tawagarsa suka kai wa Gwamna Siminalayi Fubara a jihar Ribas, inda daga bisani Bashiru ya sake jaddada tsarin jam'iyyar cewa kowane gwamna shi ne jagoran jam'iyyar a jiharsa.
Sakataren ya ce Nyesom Wike ba ɗan APC ba ne, don haka ba shi da hurumin tsoma baki a harkokin jam'iyyar, tare da shawartarsa da ya sauka daga muƙamin minista kuma ya daina halartar taron Majalisar Zartarwar ƙasar.
Sai dai a martaninsa, Nyesom Wike - wanda tsohon gwamnan jihar ta Ribas ne kuma tsohon mai gida na siyasa ga Gwamna Fubara - yayin wani rangadi da ya kai ƙaramar hukumar Gokana ta jihar Ribas ɗin, ya buƙaci sakataren jam'iyyar da ya tsame hannunsa daga siyasar jihar.
A watan Disamban da ya gabata ne dai Gwamnan jihar Ribas, Similanayi Fubara ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki, a wani mataki da wasu ke ganin tamkar shatale ƙafa ne ga Wike.
Wike ya zargi Bashiru da karɓar kuɗi
Wike ya kuma yi barazanar sanar da Shugaban Ƙasar Bola Ahmed Tinubu game da zargin karɓar kuɗi da kuma rawar ƙafar da suke kan naira biliyan ɗari shida da ke kwance a asusun gwamnatin jihar:
''Kada ka yi tunanin za ka mana wayo ko kana da wata dabara, sam ba zai yi aiki a kanmu ba.
''Ko da ka kawo mutane daga wasu jihohi su riƙa magana da yawunka, hakan ba zai yi wani tasiri ba. Na faɗa wa mutane, idan ka ɗauki wani mataki ko ka karɓi cin hanci, ba lallai ba ne sai ka fito ka bayyana wa jama'a'', a cewar Wike.
''Akwai mutanen da suka ƙasa samar wa da Shugaba Tinubu nasarar zaɓe a jihohinsu, duk da kusancinsu da shi, amma mu mun yi, mun lashe zaɓe, mun ci kujerar gwamna da ta 'yan majalisar jiha da na tarayya,'' in ji Wike.
Martanin APC
A martanin da jam'iyyar APC ta mayar wa ministan ta zarge shi d ahaddasa rikici a duk inda ya sanya ƙafarsa.
Cikin wata hira da BBC, Daraktan yaɗa labarai na jam'iyyar, Malam Bala Ibrahim, ya ce ya kamata Wike - wanda ba ɗan jam'iyyarsu ba ne - ya natsu ya sani cewa mulki ba da hauragiya ake yi ba.
''Shi fa Wike ko a can ma [PDP] ba a rabu da shi lafiya ba. Kuma ya kamata a sani duk inda fa ya sa ƙafarsa wuta ce ke tashi, ana tir da shi,'' in ji Bala Ibrahim.
Shi ma sakataren jam'iyyar na ƙasa cikin wata sanarwa da ya fitar, Ajibola Bashiru ya ce ba za su bari Wike ya hargitsa musu jam'iyya 'kamar yadda ya yi a PDP ba'.
Abin da ya janyo taƙaddamar
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dokta Kabiru Sa'id Sufi Malamai a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a da ke Kano, kuma mai sharhi kan al'amuran siyasar Najeriya ya ce rikicin ya samo asali ne daga komawar Fubara jam'iyyar APC mai mulki.
''Ya yi tsammanin zai ci gaba da kasancewa jigon siyasar jihar ko jagoran APC da gwamnatin tarayya a jihar, amma kuma sai ya fuskanci ba haka ba ne'', in ji shi.
A ƙa'idar kusan duka jam'iyyun Najeriya, gwamnan shi ne jagoran jam'iyya a jiha.
''Amma shi Wike yana ganin muƙaminsa na ministan gani yake hakan zai sa ya kasance jagoran jam'iyyar a jihar'', kamar yadda masanin siyasar Najeriyar ya bayyana.
Haka kuma Dokta Sufi na ganin cewa wani abu da ya janyo taƙaddamar shi ne yadda Wike ba ya son wasu su riƙa tsoma baki a siyasar jihar Ribas.
''Ɗaya daga cikin dalilan shi ne baya son ganin wasu manya ko wakilan gwamnatin tarayya na tsama baki a siyasar jihar Ribas'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa wannan ne ma dalilan da ya sa ministan ya riƙa musayar yawu da zargin sakataren APC na ƙasa.
Ina makomar Wike a gwamnatin APC?
Dokta Kabiru Sufi ya ce idan aka tafi a haka Nyesom Wike zai iya rasa kujerarsa ta ministan Abuja.
''Idan aka yi la'akari da komawar gwamnan jihar APC, to kusan duk wani amfani da Wike zai yi wa APC a jihar a iya cewa ya ƙare, saboda duk amfanin da zai yi wa APC a jihar ba zai kai yadda gwamnan zai yi, duk kuwa da ƙarfin ikonsa a jihar'', in masanin kimiyyar siyasar.
Don haka Dokta Sufi ya ce matsawar ministan ya ci gaba da taɓa wasu manyan mutane a jam'iyyar da ma cikin gwamnati to lallai da yiwuwar zai iya rasa kujerarsa ta minista.
''In ya ci gaba da haka, to lallai APC za ta iya haƙura da shi tare da riƙe gwamnan da take ganin zai yi mata aiki fiye da Wike a jihar'', in ji Dokta Sufi.











