Abincin da zai kare ku daga ƙarancin jini

Asalin hoton, Getty Images
Jini daya ne daga cikin abubuwa masu matuƙar muhimmanci a jikin ɗan'adam, wanda ɗaya daga cikin manyan aikinsa shi ne safarar sinadaran da jiki ke buƙata domin ci gaba da gudana.
Rashin isasshen jinni a jikin dan'adam na iya haifar da lalura daban-daban.
Wasu daga cikin al'umma da suka fi hadarin samun ƙarancin jini a tattare da su, su ne mata da ke dauke da ciki.
Wannan ne ya sa mata masu ciki ke da buƙatar cin abincin mai inganci domin samun isasshen jini, musamman abinci da ke ɗauke da sinadarin iron. In ji likitoci
Likita mai kula da lafiyar al'umma, Dokta Zara Zambuk wadda ke aiki a Abuja babban birnin Najeriya ta ce sinadarin yana kuma taimakawa wajen samar da kuzari da ba da ƙarfi ga jiki.
Ta ƙara da cewa" shi sinadarin iron yana da amfani daban-daban a jiki, ya kan ɗauki iskar oxygine daga huhu zuwa sassan jiki.... Yana da amfani sosai wurin aiki a cikin ƙwaƙalwa, ya kan taimaka wajen sa koyo da tunani, yana kuma ƙara garkuwar jiki."
Likitar ta kuma bayar da misalan ire-iren abincin da ke ɗauke da sinadarin na iron.
kamar haka:
- Hanta
- Naman rago
- Naman shanu
- Naman awaki
- Kifi
- Kaza
- Wake
- Tumatur
- Korayen ganyayyaki
Dokta Zarah ta ƙara da cewa a kan samu wasu nau'oin abincin da ake ƙarawa sinadarin a lokacin sarrafa su.
Sai dai ta ce domin samun cikakken amfanin sinarin bai kamata a dafa ganyayyaki su dahu luguf ba, saboda hakan na kashe sinadarin na iron da sauran sinadaran da ke ciki.
Inda ta ƙara da cewa "akwai abubuwan da ke hana jikin mutum ya zuƙi sinadarin iron idan an ci daga cikin abinci. Misalansu su ne shayi da gahawa da kuma sinadarin Calcium."
Ta ce "Idan an ci abinci kar a hada da shayi don madara na ɗauke da sinadarin calcium sosai. Akwai waɗanda sun mai da shi al'ada kullum aka ci abinci sai a sha shayi. Sai dai a bari kamar bayan sa'a ɗaya ko biyu bayan nan sai a sha shayin, saboda jiki ya samu ya amfana da sinadarin iron ɗin da ke cikin abinci."

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Akwai wasu abubuwan kuma da ke sa wa jiki ya amfana da sinadarin iron ɗin sosai misali kamar Vitamin C. Inda ta bayar da misalin cewa tumatur da lemo da wasu ƴaƴan itace na ɗauke da sinadarin.
Haka kuma yana da kyau a haɗa abinci daban-daban masu ɗauke da sinadarin a ci a lokaci ɗaya. Kamar misali wake da ganye da kifi ko nama ko kaza, sannan a sanya tunatur a ciki kuma a biyo da lemon fata.
Wasu alƙaluma da aka wallafa a wata maƙala kan matsalar ƙarancin jini sakamakon ƙarancin sinadarin iron sun nuna cewa kimanin kashi 25 cikin ɗari na mutanen duniya na fuskantar amosanin jini.
Maƙalar wadda aka sabunta a watan Agustan 2023 a shafin intanet na national Library of medicine, mallakar gwamnatin Amurka ta kuma bayyana cewa ƙarancin sinadarin iron shi ne kan gaba wajen haddasa amosanin jini, don shi ne ke janyo kashi 50 cikin ɗari na amosanin jinin da ake samu.
Haka zalika, matsalar ta fi ƙamari a ƙasashe masu tasowa idan aka kwatanta su da Amurka. Yayin da ƙarancin sinadarin na iron a tsakanin matan da ba su wuce shekarun haihuwa ba a ƙasar Amurka, ya kai kashi 10 cikin ɗari saboda jinin al'ada.
Duk da cewa matsalar ƙarancin sinadarin iron ɗin ba shi da yawa a Amurka, amma iyalai masu ƙaramin ƙarfi sun fi fuskantar haɗarin samun ƙarancin sinadarin a jiki.











