Yaya sabon harajin Trump na kashi 10 ga ƙasashe zai yi aiki?

    • Marubuci, Grace Eliza Goodwin
  • Lokacin karatu: Minti 4

Kotun ƙolin Amurka ta yanke hukuncin cewa shugaba Donald Trump ya wuce makaɗi da rawa wajen sanyawa duniya haraji a shekarar da ta gabata.

Kotun ta ce Trump ba shi da ikon amfani da dokar 1977 - Dokar Tattalin Arzikin ƙasashen duniya watau (IEEPA) - don sanya haraji kan kayan da ake shigowa da su daga kowacce ƙasa.

Wannan hukuncin ya bayar da damar a mayarwa da ƴan kasuwa kuɗaɗen da yawansu ya kai dala biliyan 130 da aka tattara ta hanyar karɓar harajin kayayyaki, sai dai akwai yiwuwar za a fafata a kotu

Sa'o'i ƙalilan bayan sanar da hukuncin, sai Trump ya rattaɓa hannu kan dokar da ta bayar da damar amfani da wata mafita ƙarƙashin sashe na 122 shekara ta 1974 cikin dokar kasuwanci wadda ta ba shi ikon sanya harajin kashi 10 kan kayayyakin da ake shiga da su Amurka daga ƙasashen ƙetare.

Ga abinda ya kamata a sani da abinda zai zo a gaba da kuma tambayoyi game da haraji.

Harajin da aka gano ya saɓa wa doka?

Hukuncin kotun ƙolin da aka fitar ranar 20 ga watan Fabrairu ya shafi dokar da ta baiwa Trump damar sanyawa ƙasashe haraji ƙarƙashin IEEPA ne kawai.

Trump ya yi amfani da ita a watan Fabrairun shekara ta 2025 kan kayayyakin da ake shigowa da su daga Chaina da Mexico da kuma Canada inda ya ce ƙwayoyin fentanyl da ake shigowa da su daga wadannan ƙasashe ne suka sa ya ɗauki matakin gaggawa.

Bayan wasu watanni kuma, sai Trump ya sake ɗaukar wani mataki mai tsauri inda ya sanya haraji tsakani kashi 10 zuwa kashi 50 cikin 100 kan kayayyakin da ake shiga da su daga ƙasashen duniya.

Kotu da Majalisar Dokokin Amurka ne kawai ke da damar ƙirƙirar sabbin haraji.

Har ila yau wasu daga cikin harajin da Trump ya sanya a shekarar da ta gabata ba sa cikin tsarin ɗaukar matakin gaggawa da dokar ta bayar da izini.

Daga ciki akwai harajin ƙarfe da sanholama da ababen hawa waɗanda Trump ya sanya ƙarƙashin wata dokar Amurka sashe na 232 na dokar faɗaɗa kasuwanci ta shekara ta 1962 wadda ta bayar da misali da fargabar matsalolin tsaro.

Trump ya sanya sabon haraji ƙarƙashin wata doka

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayan hukuncin da kotun ƙolin ta yanke, Trump ya fitar da sanarwar sanya harajin kashi 10 cikin 100 ga ƙasashen duniya kan kusan dukkan kayayyakin da ake shiga da su Amurka ƙarƙashin sashe na 122 na wata dokar da ba a taba amfani da ita

Sashen ya ba shi damar sanya harajin kashi 15 har tsawon kwanaki 150 kuma cikin kwanakin majalisa ba ta da ikon ɗaukar wani mataki, hakan na nufin mataki ne na wucin gadi.

Sai dai akwai yiwuwar Trump zai iya amfani da wasu ƴan majalisa. Sashe na 122 na dokar bai hana shugaban ƙasa ƙara wa'adin harajin ba idan kwanaki 150 sun ƙare kamar yadda cibiyar bincike ta Cato Institute ta bayyana.

Fadar White House ta ce Trump na amfani da sashen na 122 wajen inganta kasuwancin Amurka sannan ya na duba yiwuwar sanya haraji a ƙarƙashin sashe na 301 na dokar kasuwanci ta shekara ta 1974

Dokar ta baiwa wakilin Amurka na kasuwanci - matsayin da a yanzu Jamieson Greer ke riƙe da shi- damar binciken yadda ƙasashe ke gudanar da kasuwanci. USTRna da damar sanya haraji idan ta gano rashin bin doka ko rashin adalci.

Wani masanin tattalin arziƙi ya shaidawa BBC cewar abubuwan da za a nema wajen bincike za su iya sanya janye haraji ya yi wahala.

Sakataren Baitul Malin Amurka Scott Bessent ya ce sashe na 122 da sashe na 232 sa kuma sashe na 301 na dokar zasu iya hana sauya haraji a shekara ta 2026.

Za a mayar wa ƴan kasuwa harajin da suka biya ba bisa ƙa'ida ba?

Ɗaya daga cikin dalilan da Trump ya bayar game da sanya haraji shine ana zuba kuɗaɗen a baitul malin Amurka ne don bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar.

Gwamnatin Amurka ta karɓi biliyoyin daloli daga kamfanonin da ke shigar da kayan ƙasashe waje, wasu rahotanni sun ce adadin kuɗaɗen ya kusan dala biliyan 130 daidai da fan biliyan 96.

Ya yin da Kotun ƙoli ta yanke hukunci cewar harajin da Trump ya sanyawa ƙasashe ya saɓawa doka, ba ta sanar da hanyoyin da za a bi wajen mayarwa waɗanda suka biya harajin kuɗaɗensu ba.

Trump ya shaidawa manema labarai cewa ya na sa rai batun mayar da kuɗaɗen zai ɗauki shekaru ana fafata shari'a.

  • Ƴan kasuwa sun yi farin ciki da hukuncin harajin

Bayan an yanke hukuncin sakataren baitul malin Amurka Bessent ya ce za a iya shafe shekaru da dama kafin a mayar da kuɗaɗen harajin.

Alex Jacquez, shugaban cibiyar tsare-tsare da wayar da kai ta Groundwork Collective ya shaidawa kamfanin yaɗa labarai na CBS abokin hulɗar BBC cewar sama da ƴan kasuwa 1,000 ne suka nemi a mayar musu da kuɗinsu tun kafin Kotu ta yanke hukunci.

Ya ƙara da cewar akwai yiwuwar adadin ya ƙaru.

Shi ma gwamnan Jihar Illinois JB Pritzker ya nemi fadar White House ta biya kowanne iyali a Amurka dala1,700 sakamakon karɓar haraji ba bisa ƙa'ida ba.

Wane haraji ne ke aiki a yanzu?

Daga ranar 24 ga watan fabrairu sabon harajin kashi 10 zai fara aiki kan dukkan kayan da za a shigar Amurka daga ko ina kamar yadda fadar White House ta sanar.

Wani jami'in fadar White House ya shaidawa BBC cewar ƙasashen da suka ƙulla yarjejeniyar kasuwanci da Amurka da suka hada da Burtaniya da Indiya da Tarayyar Turai su ma za su fuskanci harajin kashi 10% ƙarƙashin sashe na 122 maimakon harajin da suka amince tsakaninsu a baya.

Akwai kayan da za a ware daga biyan haraji saboda buƙatar tattalin arziƙin Amurka.

Sun faɗa cikin rukunin wasu muhimman kaya kamar ma'adinai da ƙarafa da kayan makamashi da amfanin gona da magunguna da kayan lantarki da motoci da motocin dako da kuma na'urorin jiragen sama.

Akwai kuma kayan karatu da gudummawa cikin waɗanda babu haraji cewar fadar White House

Wasu ƙarin kaya masu muhimmanci da babu haraji a kansu sun haɗa da kayan da suka danganci yarjejeniyar kasuwanci tsakanin Amurka da Mexico da kuma Canada watau USMCA.

Firaiminista Mark Carney ya ce Canada na daga cikin ƙasashen da suke biyan haraji mafi ƙaranci saboda yarjejeniyar USMCA

Har ila yau kayan tufafi daga Costa Rica da El Salvador da Guatemala da Honduras da kuma Nicaragua za su ci gaba da zama ƙarƙashin yarjejeniyar kasuwanci ba tare da shinge ba tsakanin Jamhuriyar Dominica da Amurka.