Abincin da aka fi ci lokacin sahur da buɗe-baki a ƙasashen Afirka

Sellou

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sellou
Lokacin karatu: Minti 2

A lokacin azumin Ramadana akwai ƙaruwar marmarin cin abinci daban-daban.

Wasu kuma na la'akari ne da amfani ga lafiya da kuma yanayi wajen zaɓen irin abin da suke buɗe-baki ko kuma sahur da shi.

A daidai lokacin da iyalai suke tunanin yanayin cimakan buɗe-baki da kuma na sahur na azumin gaba, wanda ake ci da asuba, mun tattauna da wasu wakilanmu na wasu ƙasashen Afirka domin sanin wane irin abinci aka fi ci a ƙasashensu wajen sahur da buɗe-baki a Ramadan.

Moroko

"A lokacin buɗe-baki, muna fara cin dabino ne da madara. Sai mu ci abin da muke kira harira - wani nau'in fate-fate ne tamkar miya kuma tana da daɗi da ƙara kuzari da ɗumama hanji," in ji wakiliyar BBC, Basma El Atti.

A lokacin sahur kuma, "muna yawan cin abin da ake kira Sellou - wani kwaɗon burodi da gyaɗa, sai kuma ruwa da muke sha sosai.

Najeriya

Tuwo da miyar egusi wanda nau'in abinci masu nauyi da ake amfani su wajen sahur a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tuwo da miyar egusi wanda nau'in abinci masu nauyi da ake amfani su wajen sahur a Najeriya

Ahmed Ambali daga Najeriya ya ce "A wajen buɗe-baki, mun fi cin abinci mara nauyi. Muna shan kunu da ƙosai da alala. Abinci mara nauyi dai bayan cikin ya daɗe babu komai."

A wajen sahur fa?

"Gaskiya a sahur narkar abinci muke yi - kamar su tuwo da dangoginsa."

Senegal

Shinkafa dafa-duka da aka fi yin sahur da shi a Senegal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shinkafa dafa-duka da aka fi yin sahur da shi a Senegal

Al'ummar Senegal "A wajen buɗe-baki, muna shan shayin kinkeliba ne mai ɗauke da sinadarin magani da dabino. Wannan ne haɗin da zai taimaka wajen buɗe ciki da hanji," in ji Khadidiatou Cisse.

Ta ƙara da cewa "A wajen sahur kuma, kowa na cin abubuwa daban-daban, musamman shinkafa dafa-duka, amma muna amfani da miyar kayan lambu."

Kenya

Pilaf ko Pilau ko Plov da nama da ake buɗe-baki da shi a Kenya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Pilaf ko Pilau ko Plov da nama da ake buɗe-baki da shi a Kenya

"Da buɗe-baki, muna cin samosa da Bhajia da chapati kafin mu ci abinci mai nauyi kamar pilau," in ji Nasteha Mohammed.

A sahur kuma, "mun fi cin abu mara nauyi kamar shayi da madara (yoghurt) da chapati da duk wani abinci da zai iya riƙe jikinka har ka wuni ko da ana rana."