Yaushe Wike zai sakar wa Fubara mara?

Fubara da Wike

Asalin hoton, Siminalayi Fubara

Bayanan hoto, Ana ganin cewa sulhun da aka yi tsakanin Fubara da Wike zai kawo ƙarshen rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar Rivers.
Lokacin karatu: Minti 4

Tun bayan komawar Siminalayi Fubara ofis a matsayin gwamnan jihar Rivers a ranar 18 ga watan Satumba, bayan kwashe watanni shida a dakace sakamakon dokar ta-ɓaci da shugaba Bola Tinubu ya ƙaƙaba wa jihar sakamakon rikice-rikicen siyasa, ake ta ganin Wike da Fubara inda a ƙarshen makon ma mutanen biyu suka yi wata ganawar sirri.

Ana dai ganin cewa ganawar ta sirri ba za ta rasa nasaba da rushe kwamishinoni da sauran ma'aikatan gwamnatin da Fubara ya yi ba, a ranar bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun ƴancin kai.

Masu fashin baƙin na ganin ganawar da mutum biyun suka yi na da alaƙa da koƙarin sasantawa ta hanyar raba muƙaman kwamishinonin da za a naɗa a nan gaba, wani abu da ake ganin na ɗaya daga batutuwan da aka cimma da gwamnan - wato raba mukamai tsakaninsa da Wike.

Hakan ya janyo tambayar ko yaushe ne Wiken zai sakarwa zaɓaɓɓen gwamnan mara?

Wike ba zai sakar wa Fubara maraba - Masani

..

Asalin hoton, BBC Pidgin

Farfesa Kamilu Sani Fagge, masanin kimiyyar siyasa ne ko malami a jami'ar Bayero da ke Kano.

Farfesan ya ce babu wani lokaci da ministan na Abuja, Nyesom Wike zai sakar wa tsohon yaron nasa mara har sai ya ga ya samu kykkyawa dama a kansa wadda ba zai iya yin wani motsin kirki ba a siyasance.

"Wike na da tasiri sosai a gwamnatin tarayya kuma muddin dai bai samu abubuwan da yake bukata ba to babu wani abu da zai yi tasiri. A halin yanzu ɓangaren Wike ne ke da rinjaye a majalisar dokoki sannan ga goyon bayan da yake da shi a gwamnatin tarayya."

Wannan ne zai sa shi Fubara dole ne sai ya sassauto ya bi abubuwan da shi Wike ke so ba domin hakan ne shi yake so ba domin a tsarin siyasar idan ba haka ya yi ba to zai zama yana fama da matsaloli da dama." In ji Farfesa Kamilu Sani Fagge.

Me ya kamata Fubara ya mayar da hankali a kai?

Fubara

Asalin hoton, RSGH Media

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wani mai sharhi kan siyasa a Najeriya Olalekan Ige ya shaida wa BBC cewa abin da ya kamaci Fubara shi ne ya kama aiki kan jiki kan karfi saboda babu sauran lokaci mai tsawo da ya rage masa.

Ya ce akwai ayyuka da yawa da suka kamata gwamnan ya aiwatar musamman batun ƙarasa ayyukan gwamnatin jihar da aka dakatar sanadiyyar dokar ta-baci da aka kafa da kuma kawo sabbin ayyukan ci gaban jihar.

Ige ya ce yanzu 'yan watanni suka rage kafin shekarar 2025 ta kare, sannan 2026 za ta kasance shekarar da hankula za su koma kan zaben 2027.

A cewarsa gwamnan bai da wani lokaci da zai tsaya yin bincike-binciken abubuwan da suka faru, babban abin da ya fi kamata ya mayar da hankali a kai shi ne kawo manufofi da ayyukan da za su bunkasa rayuwar al'ummar jihar Rivers.

Shi kuwa tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta Najeriya O.C.J Okocha cewa ya yi "abin da zan fada wa duk wanda wannan lamarin ya shafa, musamman gwamna Fubara da kuma shugaban majalisar dokokin jihar Rivers, Martin Amaewhule shi ne su kalli abin da ya faru a matsayin wata matashiya.

"Ya kamata su koma aiki da niyyar yin jagoranci na gari. Zan kuma shawarce su, su zauna su yi karatun ta-natsu, su sani cewa ya kamata bangarorin gwamnati su taimaka wa juna ne, ba su rika fada da juna ba." In ji O.C.J Okocha.

Matsalolin da aka samu a jihar gabanin ayyana dokar ta-ɓaci

..

Asalin hoton, Rivers State Government Press

  • Yunƙurin tsige Gwamnan Fubara da majalisar dokokin jihar ta yi cikin watan Oktoban 2023, lamarin da ya raba kan ƴan majalisar, inda ƙalilan daga cikinsu ke goyon bayan Fubara, yayin da mafiya rinjayensu ke goyon bayan Wike.
  • Batun ƙona majalisar dokokin jihar da kuma rusa ginin majalisar ga kuma batun ficewar wasu ƴanmajalisar daga PDP zuwa APC, kodayake daga baya sun musanta ficewar.
  • Ga kuma batun shari'o'in kotu daban-daban, ciki har da hukuncin Kotun Ƙolin ƙasar na tabbatar da Martin Amaewhule a matsayin halastaccen kakakin majalisar dokokin jihar, tare da rusa sakamakon zaɓukan ƙananan hukumomin jihar da aka gudanar ƙarƙashin gwamnatin Fubara.
  • Haka ma Ƙotun Ƙolin Ƙasar ta buƙaci gwamnan ya sake gabatar da kasafin kuɗin ƙasar na 2025 a gaban majalisar dokokin jihar ƙarƙashin Amaewhule, to sai dai ba a kai ga saka ranar da za a sake gabatar da kasafin ba, har Shugaba Tinubu ya sanar da dokar-ta-ɓacin.

A lokacin sanar da dokar ta-ɓacin ranar 18 ga watan Maris, Tinubu ya dokar da gwamnan jihar da mataimakinsa da kuma duka mambobin majalisar dokokin jihar.