Iraniyawa na rige-rigen sayen kayan abinci saboda yaƙin da ake fafatawa

Asalin hoton, AFP via Getty Images
- Marubuci, Ghoncheh Habibiazad
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior reporter, BBC News Persian
- Lokacin karatu: Minti 3
Mazauna birnin Tehran suna rige-rigen sayen kayan abinci domin adanawa a gidajensu saboda fargabar yadda yaƙin da ake fafatawa a Iran zai iya ɗaukar dogon lokaci.
Mazauna birnin sun shaida wa BBC cewa suna cikin damuwa game da ƙarancin kayan abinci da yadda farashinsa ke hauhawa, a daidai lokacin da ake ci gaba da ruwan wuta a birnin.
"Akwai buƙatar mu jibge abinci a gidajenmu, saboda ba mu san yaushe yaƙin zai zo ƙarshe ba," inji wani mazauni Tehran mai suna Nasrin. "Muna fargabar abinci zai iya yanke mana idan ba mu adana ba."
Ko a watan Disamban bara sai da aka yi zanga-zangar tsadar rayuwa da takunkuman ƙasa da ƙasa da aka ƙaƙaba wa ƙasar, lamarin da ya haifar da martani mai zafi daga gwamnatin Jamhuriyar Musuluncin ta Iran.
Hare-hare ta sama
Hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai a 'yan kwanakin na sun ƙara dagula lamura, kamar yadd wasu mazauna yankin da suka samu damar sadarwar intanet suka shaida wa BBC biyo bayan katse sadarwar da aka yi a ƙasar.
An haramta wa kafofin yaɗa labaran ƙasashen waje samun izinin shiga Iran, lamarin da yake taƙaita samun sahihan bayanai game da abubuwan da ke faruwa a ƙasar.
Bugu da ƙari, katse intanet da aka yi a Iran ya ƙara tsananta lamarin.
Wani mazauni Tehran da ya bayyana sunansa da Pouya, ya ce farashin kayayyaki ya yi tashin gwauron zabi tun bayan da yaƙin ya ɓarke a ranar Asabar.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Ɗazu ina duba farashin shinkafa, na ga ya kai 625; abin da yake 530 kafin a fara yaƙin," in ji shi.
Ya ƙara da cewa hauhawar farashin ya fi shafar dankali.
Kafofin yaɗa labaran Iran sun ruwaito cewa "a ƙoƙarin da gwamnati take yi na ganin ta samar da kayan masarufi", an dakatar da safarar kayan abinci "har illa ma sha Allahu".
Wani mazauni garin Karaj, da ke kusa da Tehran, mai suna Shayan ya ce farashin data ma ya ƙara tsada,
Ya ce: "Yana da matuƙar wahala mutum ya iya shiga shafukan intanet a yanzu". Ya ƙara da cewa shi ma farashin intanet na Starlink mallakin Elon Musk ya ƙaru sosai.
Shi ma wani matashi mai suna Omid da ke zaune a Tehran ya ce "mutane sun fara damuwa game da tsawon lokacin da za a iya ɗauka ana kai ruwa rana."
Ya ce ya yi tsammanin zuwa yanzu lamura sun daidaita da zarar Amurka da Isra'ila sun kai hari kan wasu mutane ne irinsu Ayatollah Ali Khamenei, da aka kashe a ranar Asabar.
Sai dai ya ce tun bayan kisan na shi, an samu ƙaruwar fashe-fashe a brinin a ranar Talata, kuma saboda haka ne ma ya siya kayan abinci ya jibge a gida.
Amma kuma ba duka shagunan ake buɗewa ba. "An jibge jami'an tsaro sosai a kan hanyoyi, amma duk da haka babu kowa a gari" in ji shi.
Tserewa daga Tehran
Wasu mazauna yankin sun ce sun ji ƙarar fashe-fashe a birnin a ranakun Litinin da Talata.
Wata mata mai suna Maryam, ta ce tana kusa da wurin da aka harba makamai masu linzami a birnin a ranar Litinin.
"Hare-haren da aka kai a daren jiya akwai ta da hankali," kamar yadda ta bayyana a wani saƙon tes da ta aika. "Gidajenmu sun girgiza"
Wasu mazauna Tehran ɗin sun ce tuni suka tsere daga birnin saboda hare-haren da ake kaiwa.
Sai dai Maryam ta ce babu inda za ta je.
"Wasu mutanen sun gudu daga gidajensu, amma mu muna nan a nan," in ji ta.
"Idan ba a kashe mu ba, za mu ci gaba da zama a nan, kuma idan za a yi zanga-zanga a gari ma za mu fita da duka sauran mutanen gidan nan. Ina jin daɗin yadda ake kai hari kan waɗannan jami'an. Za mu jure hare-hare har sai sun ƙare."
Aƙalla mutum 787 ne aka kashe tun bayan da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da hare-hare kan Iran a ranar 28 ga watan Fabreru, kamar yadda ƙungiyar agaji ta Red Crescent ta bayyana.
Har yanzu ana ci gaba da zaman ɗar-ɗar, bayan da sojojin Isra'ila suka ce sun kai hari ofishin shugaban ƙasar Iran da wasu muhimman wurare a ranar Talata.
Wasu bidiyoyi da BBC ta tantance sahihancinsu, sun nuna yadda aka samu fashewar wasu abubuwa a Padris da ke gabashin birin.
Tuni Iran ta mayar da martani da makamai masu linzami tare da jirage marasa matuƙa, inda ta farmaki gwamnatin Iran da sansanonin soji a Tel Aviv da ma wasu wuraren.
Haka kuma, an kai hare-hare a ƙasashen da Amurka take da sansanoni irinsu Qatar, Bahrain, Jordan, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) da Kuwait, da kuma ƙwayen Amurka Oman da Saudiyya.
Ana zargin Iran da faɗaɗa hare-harenta a 'yan kwanakin nan, ciki har sansanonin jiragen ruwa da na fararen hula irinsu otal-otal da Dubai da kuma ofishin jakadancin Amurka da ke Riyadh a Saudiyya.











