Spain ta mayar da martani kan barazanar Trump saboda adawarta da harin Iran

Asalin hoton, RONALD WITTEK/EPA/Shutterstock
Firaministan ƙasar Spain, Pedro Sánchez, ya mayar da martani kan barazanar da Donald Trump ya yi na katse hulɗar kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu, sakamakon adawar Madrid ga harin da aka kai kan Iran.
A jawabin da ya gabatar ta gidan talabijin a safiyar Laraba, Sánchez ya jadadda matsayar gwamnatinsa ta hana Amurka amfani da filin jirginta domin kai wa Iran hari.
"Ba za mu goyi bayan yaƙi ba” in ji firaministan.
Ya yi kira da kada a maimaita “kurakuran da suka gabata”, yana mai nuni da mamayar da aka yi wa Iraq a 2003, wadda ya ce ba ta cimma manufofinta ba, sai ma ta haifar da rashin tsaro da kuma taɓarɓarewar rayuwar jama’a da dama.
Sánchez ya ce hare-haren kan Iran na iya haifar da irin wannan tasiri a fannin tattalin arziki ga miliyoyin mutane, kuma gwamnatinsa na duba matakan da za ta ɗauka domin rage illa.
A ranar da ta gabata, Trump ya sha alwashin “katse duk wata hulɗa” da Spain, tare da kiran ƙasar da suna marar daɗi, bayan da Sánchez ya ƙi amincewa Amurka ta yi amfani da sansanonin sojinta da ke Spain wajen kai hari kan Iran.
Madrid ta bayyana harin a matsayin “tsoma bakin soja da bai da hujja kuma mai haɗari.”







