Mutum shida da za su iya maye gurbin Ayatollah Ali Khamenei

Asalin hoton, BBC Monitoring
Kamar yadda kundin tsarin mulkin Iran ya tanada, Majalisar Masana ta ƙasar – wadda ta ƙunshi manyan malaman addini 88 – ce za ta zaɓi mutumin da zai zamo sabon jagoran addinin ƙasar.
Ana zaɓen wakilan majalisar malaman Iran ne a duk shekara takwas, kuma dole ne sai Majalisar Magabata ta ƙasar ta tantance su.
Masu goyon bayan Ali Khamenei ne suka lashe dukkanin kujerun majalisar a zaben shekara ta 2024, inda daga baya aka samu giɓi a kujeru huɗu bayan mutuwar wakilansu – cikin har da Ebrahim Raisi, waɗanda za a cike gurbinsu a zaɓen cike gurbi da za a yi a watan Mayun 2026.
Sashe na 111 na kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanadi cewa a samar da wata majalisa ta mutum uku ta wucin-gadi, wadda za ta gudanar da al'amuran ƙasar kafin zaɓen sabon jagoran addini.
Kwamitin riƙon-ƙarywar zai ƙunshi shugaban ƙasa Massoud Pezeshkian, da babban alƙalin alƙalan ƙasar Gholamhossein Mohseni Ejei da kuma malami masanin shari'a guda ɗaya daga Majalisar Magabata ta ƙasar.
A ranar Lahadi aka sanar da Alireza Arafi – wanda riƙaƙƙen malamin addini ne mai ra'ayin ƴan mazan jiya, kuma ɗaya daga cikin waɗanda ake ganin za su iya gadon Ayatollah – a matsayin na uku a cikin kwamitin.
A ranar ta Lahadi shugaban Iran Massoud Pezeshkian ya tabbatar cewa kwamitin riƙon ya fara aiki.
Duk da cewa ana sa ran majalisar ƙwararru ta zaɓi sabon jagoran addini cikin hanzari, amma babu takamaiman wa'adi da aka ɗiba musu na zaɓen.
Duk da cewa a halin yanzu masu goyon bayan Ayatollah Khamenei ne suka cika majalisar, amma akwai yiwuwar samun mutane irin su shugaba Pezeshkian, wanda mai ra'ayin kawo sauyi ne, ya kawo canjin al'amura.
Kusan wajibi ne Majalisar Masana ta yi aiki tare da Rundunar juyin juya halin ƙasar da kuma mutanen da ke kusa da Khamenei wajen zaɓen sabon jagoran addinin ƙasar.
Rahotanni sun bayyana cewa kwamitin mutum uku da aka kafa ya fara aiki a asirce kan wani jerin sunayen mutanen da ake tunanin za su iya cike gurbin na Ayatollah Khamenei.
To amma siriin da ke tattare da lamarin ya ƙara iza wutar raɗe-radin waɗanda za su iya samun muƙamin.
Ko ɗan Khamenei zai gaji mahaifinsa?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mojtaba Khamenei, wanda ake bayyanawa a matsayin mai matuƙar tasiri, ya kasance a bakunan kafafen yada labarai a tsawon sama da shekara 20.
Mojtaba, wanda ya yi suna wajen tafiyar da lamurran ofishin mahaifinsa, ya kasance cikin mutanen da Amurka ta sanya wa takunkumi bisa zargin shi da "iza wutar manufofin mahaifinsa na tayar da hankali a yankin da kuma danniya a cikin gida".
Yana da shekara 56, kuma har yanzu ana kallon shi a matsayin wanda zai iya gadon mahifin nasa, musamman bayan rasuwar shugaba Raisi, wanda a baya ake kallo a matsayin na gaba-gaba a jerin wadanda za su iya samun muƙamin.
Sai dai ba a ji wani bayani game da shi ba tun bayan harin da aka kai kan mahaifinsa, lamarin da rahotanni suka ce ya rutsa da matarsa.
Sai dai akwai ƙalubale, ɗaya daga ciki shi ne batun gadon mahaifi, wani abu da Ayatollah Khameini da magabacinsa Ayatollah Khomeini suka soki tsohon tsarin gwamnatin Pahlavi a kai, wadda aka tuntsurar a 1979 lokacin juyin juya hali.
Wannan ne ya sa rahotanni suka ce Khamenei ya ƙi amincewa da bayyana Mojtaba a matsayin wanda zai gaje shi.
Sauran ƴan takara
Wasu daga cikin wakilan majalisar masana ta ƙasar na cikin jerin waɗanda ake ganin za su iya samun muƙamin na Ayatollah. Wasu daga cikinsu su ne:
Alireza Arafi: Mai ra'ayin mazan jiya, kuma mataimakin shugaban Majalisar Masana. Wakili a Majalisar Magabata tun shekara ta 2019. Shi ne shugaban dukkanin cibiyoyin horas da malamai na Iran, ɗaya daga cikin manyan muƙaman addini a ƙasar.
Hassan Komeini: Ya fi karkata ɓangaren kawo sauyi. Jika ne ga Ayatollah Ruhollah Khomeini, wanda shi ne ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran kuma jagoran addini na farko daga 1979 zuwa 1989.
Mohammad Mehdi Mirbaqeri: Mai tsattsauran ra'ayin mazan jiya. Wakili ne a majalisar masana. Ana masa kallon jagoran malaman addini masu tsattsauran ra'ayi.
Hashem Hosseini Bashehri: Mai ra'ayin mazan jiya. Shi ne mataimaki na ɗaya na shugaban majalisar masana. Shi ne shugaban ƙungiyar malaman cibiyar koyar da harkokikin addini ta Qom Qom, kuma jagoran limaman juma'a na Qom.
Mohsen Araki: Mai ra'ayin mazan jiya kuma wakili a Majalisar ƙwararru ta Iran. Ɗaya ne daga cikin shugabannin ƙungiyar malaman cibiyar koyar da harkokikin addini ta Qom. An naɗa shi a matsayin wakili a majalisar daukar matakin gaggawa a 2023, bisa sahhalewar Ayatollah Khamenei a shekarar 2023










