Yadda ake takun-saƙa tsakanin El-Rufai da ICPC

Tsohon gwamnan Kaduna da shugaban ICPC

Asalin hoton, Social Media Handles

Lokacin karatu: Minti 7

Dambarwa ta kaure tsakanin hukumar ICPC mai yaƙi da almundaha a Najeriya da kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.

Sa-in-sar ta ɓarke ne bayan da a ranar Litinin hukumar ta shigar da shi ƙara gaban babbar kotun tarayya da Abuja.

Tun a ranar 19 ga watan Fabrairun da ya gabata ne hukumar ta tabbatar da cewa El-Rufai na hannunta, bayan da ta kama shi, jim kaɗan bayan hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta sallame shi daga gayyatar da ta yi masa.

Tun da farko hukumar ta gayyace shi domin amsa wasu tambayoyin da ta ce tana son samun amsarsu daga gare shi.

Bayan tsare shi hukumar ta kuma kai samame gidansa da ke Abuja, domin gudanar da bincike a ciki, kamar yadda Muyiwa Adekeye, kakakin yaɗa labaran El-Rufai ya bayyana a shafinsa na X.

Cikin wata hira da El-Rufai ya yi da gidan talbijin na Arise gabanin kama shi ya yi iƙirarin satar jin wayar babban mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu.

Iƙirarin ICPC

Barista Musa Adamu, SAN shugaban hukumar ICPC

Asalin hoton, ICPC/FB

Bayanan hoto, Barista Musa Adamu, SAN shugaban hukumar ICPC

Cikin bayanan ƙarar ICPC ta bayyana wasu abubuwa da ta ce ta samu a gidan tsohon gwamna a lokacin da ta kai samame, ciki har da na'urorin satar bayanan wayoyin mutane.

Hukumar ta shigar da ƙarar ne da nufin neman kotun ta yi watsi da ƙarar da El-Rufai ya shigar tun da farko kan yadda jami'an hukumar suka kai samame a gidansa.

ICPC ta ce ta je gidan nasa ne tare da jami'an ƴansanda, kuma sun binciki gidan nasa ne a gaban matarsa da kuma ɗansa.

Hukumar ta ce bayan bincikar gidan ta samu muhimman takardun aiki da na mallakar kadarorin tsohon gwamnan.

Sannan ta ce ta gano wasu na'urorin adana bayanai da kwamfutoci da manyan wayoyi da kuma sauran na'urorin da ta ce ta tattara su domin gudanar da binciken kimiyya a kansu.

Sai wani abu da ya ɗauki hankali shi ne yadda hukumar ta ce a alokacin samamen jami'anta sun gano wasu na'urorin da za iya amfani da su wajen satar jin wayar mutane, kuma hukumar ta ce ta nemi ya bai wa jami'anta damar buɗe na'urorin amma ya ƙi, kamar yadda takardar shigar da ƙarar ta nuna.

Martanin iyalan El-Rufai

tsohon gwamnan Kaduna

Asalin hoton, El-Rufai/FB

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A martanin da iyalansa suka mayar jim kaɗan bayan shigar da ƙarar, sun musanta ikirarin hukumar, suna masu cewa samamen da suka kai gidan nasa ma ya saɓa wa doka.

Iyalan sun kuma zargi hukumar ICPC da ƙoƙarin ''ɓata masa suna'' game da kayyakin da suka samu a gidan nasa.

Cikin wata sanarwa da ɗansa, Bello El-Rufai - wanda ɗan majalisar wakilan Najeriya ne - ya fitar a madadin iyalan tsohon gwamnan, ya musanta iƙirarin da ICPC ta yi cewa El-Rufai ya ƙi bayar da haɗin kai.

"Hukumar ICPC na son yin wasa da hankalinmu ta hanyar ƙoƙorin mayar da shirun da El-Rufai ya yi a matsayin makamin yaƙarsa, cewa da suka yi ''ya ƙi bayar da hadin kai'' ya nuna cewa hukumar ba ta san tsarin shari'ar Najeriya ba'', in ji sanarwar.

Bello El-Rufai ya ƙara da cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowane ɗan ƙasa damar yin shiru idan ya ga dama.

''Yin hakan ba zai zama rashin bayar da haɗin kai ba, ƴancinsa ne na ɗan'adam,'' in ji shi.

Dangane da batun samun na'urarin satar wayar mutane da ICPC ta yi iƙirarin ganowa a gidan El-Rufai, iyalan nasa sun ce iƙirari ne mara tushe.

"Babu abin da suka samu a gidan sai tsoffin wayoyi da kuma bubuwan adana bayanai (flash drives) da kwamfutocin da suka ɗauka'', in ji shi.

Haka kuma iyalan sun ƙalubalanci yadda jami'an na ICPC suka shiga gidan mahaifin nasu, inda suka zargi hukumar da amfani da takardar izinin da suka samu ta hanyar da ba ta dace ba daga kotun da ba ta hurumin yin hakan.

Me ya sa El-Rufai ya kai ƙarar ICPC?

Tsohon gwamnan Kaduna

Asalin hoton, El-Rufai/FB

Bayanan hoto, El-Rufa'i ne gwamnan Kaduna daga 2015 zuwa 2023

Tun da farko dai tsohon gwamnan ta hannun lauyoyinsa ya shigar da ƙarar hukumar ta ICPC da kotun majistare da ke Abuja da babban sifeton ƴansandan ƙasar da ministan shari'a saboda samamen da ta kai gidansa, wanda ya ce ya saɓa wa ƴancinsa na ɗan'adam.

A cikin ƙarar El-Rufai ya nemi waɗanda ya ke ƙarar su biya shi diyyar naira biliyan ɗaya saboda shiga gidansa don yin bincike ba tare da amincewarsa ba.

Tsohon gwamnan ya nemi kotun ta bayyana takardar izinin bincikar gidansa - da kotun majistare ta bayar - a matsayin marar inganci, wadda kuma ba za a yi aiki da ita ba.

Ya ce bayar da izinin shiga gidan nasa da wannan kotun ta yi ya saɓa wa kundin tsarion mulkin Najeriya, musamman sashen da yake magana a kan sirrin mutum.

Me ya sa El-Rufai ya shiga komar hukumomi?

Baya ga rigimarsa da hukumar ICPC , El-Rufai na fuskantar wata shari'ar tsakaninsa da hukumar tsaron farin kaya ta DSS, wadda ta shigar da shi ƙara gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa zargin aikata laifukan intanet.

DSS ta ce ta shigar da shi ƙara ne saboda zarginsa da satar wayar babban mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro allam Nuhu Ribadu.

Cikin wata hira da gidan tanbijin na Arise ne dai El-Rufai ne dai ya yi iƙirarin cewa ya yi satar jin wayar Ribadu, har ma a ciki ya ji ya bayar da izinin kama shi idan ya koma Najeriya daga ƙasashen waje.

Gabanin kamun da ICPC ta yi masa dai, hukumar EFCC ce mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta gayyaci tsohon gwamnan domin ya ba ta amsa kan wasu bayanan da take bincike a kansu.

Tuhume-tuhumen da ake yi wa El-Rufai

Hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya, DSS ce ta kai ƙarar Nasir El-Rufai a gaban kotu, bayan wata tattaunawa da ya yi da kafar talabijin ta Arise, inda a ciki ya ambaci cewar an saurari wayar da mai bai wa shugaban ƙasa shawara ke yi, inda a ciki ya bayar da izinin kama shi.

Tuhuma ta farko: "Malam Nasir El Rufa'i, a ranar 13 ga Fabrairu, 2026, a matsayin bako a shirin gidan talabijin na Arise TV da ke Abuja, ka yi iƙirarin cewa ce da kai da wasu abokan tarayyarka, kun yi kutse ba bisa ƙa'ida ba, a layin wayar mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, inda ku ka aikata laifi da ya saɓawa sashe na 12 (1) na dokokin da suka shafi laifukan Intanet, da aka yi wa gyran fuska a 2024.''

Tuhuma ta biyu: "Kai, Malam Nasir El Rufa'i, a ranar 13 ga Fabrairu, 2026, a matsayin bako a shirin gidan talbijin na Arise TV a Abuja, ka ce akwai sanayya da kuma alaƙa tsakaninka da wani mutum, wanda ya yi kutse a layin wayar tarho na Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro, Nuhu Ribadu, wanda hakan kke nufin ka aikata laifi a ƙarƙashin sashe na 27 (b) na laifukan da suka shafi Intanet wadda aka yi wa gyaran fuska a 2024.''

Tuhuma ta uku: "Kai, Mallam Nasir El Rufa'i da waɗansu mutane da har yanzuu ba a san inda suke ba, a cikin shekarar 2026 a Abuja, kun yi amfani da na'urorin da ke yin illa ga lafiyar jama'a da tsaron ƙasa da kuma sanya fargabar rashin tsaro a zukatan ƴan Najeriya ta hanyar yin kutse a layin wayar tarho na mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkaokin tsaro, Nuhu Ribadu, kuma ka amsa cewa ka yi hakan a shirin gidan talabijin na Arise TV a Abuja a ranar 13 ga watan fabrairu 2026, kuma hakan na nufin kun aikata laifi a ƙarƙashin sashe na 131 (2) Dokar Sadarwa ta Najeriya 2003."

Wane ne Nasir El-Rufai?

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, kuma tsohon ministan Abuja, babban birnin Najeriya, na daga cikin mutanen da suka fi yamutsa hazo a siyasar Najeriya.

Akwai lokacin da sanatocin Najeriya suka taɓa yin yajin aiki domin tursasa wa shugaban Najeriya na wancan lokacin Olusegun Obasanjo ya cire shi daga muƙamin ministan Abuja saboda wani kalami da ya yi game da su, wanda suke ganin tamkar cin fuska ne.

An haife shi ne a watan Fabarairun 1960 a ƙaramar hukumar Faskari da ke jihar Katsina, arewa maso yammacin Najeriya.

Sai dai ya yi akasarin rayuwarsa da karatu ne a jihar Kaduna.

Ya yi karatunsa na sakandare a sananniyar makarantar nan ta Barewa College da ke Zariya, inda ya gama a matsayin ɗalibi mafi hazaƙa a shekara ta 1976.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda a nan ma ya kammala da sakamako mai kyawu, a ɓangaren karatun safiyo.

Ya kuma yi digiri kan harkar shari'a a Jami'ar Landan da ke Ingila sannan ya yi karatun digiri na biyu kan aikin gwamnati a shahararriyar jami'ar nan ta Harvard da ke Amurka, baya ga yin kwasa-kwasai da dama.

Ya kafa kamfanin safiyo da kula da ayyuka a shekara ta 1982.

A tsakanin shekara ta 1999 zuwa 2003 ya shugabanci ma'aikatar kula da kuma sayar da kadarorin gwamnati.

Daga nan kuma ya zama ministan Abuja daga 2003 zuwa 2007.

Ya zama gwamnan jihar Kaduna daga 2015 zuwa 2023.

Nasir El-Rufai mutum ne da ake wa kallon mai kaifin ƙwaƙwalwa da sanin dabarun tafiyar da al'amura, kuma ya ɗauki matasa masu ƙwazo a matsayin waɗanda yake aiki da su a duk muƙaman da ya riƙe.

Mutum ne mai yawan faɗar abubuwan da ke tayar da ƙura, ya yi kakkausan suka ga mutanen da suka soki yadda aka tafiyar da shirin sayar da kadarorin gwamnati a lokacin gwamnatin Olusegun Obasanjo.

Aikin da ya yi a matsayin ministan Abuja na daga cikin abubuwan da suka sa ya yi ƙaurin suna, lokacin da ya ce zai tabbatar da bin ainahin tsarin birnin.

Wannan ya haifar da rushe-rushe a lokuta da dama, inda daga nan ne ya samu laƙabin 'Mai rusau', saboda rusa gine-ginen da aka yi ba bisa ƙa'ida ba.

Kuma har yanzu akan auna aikin duk wani minstan Abuja ne da ayyukan da El-Rufai ya gudanar a zamaninsa na ministan Abuja.