'Mutane fiye da 300,000 aka raba da muhallansu a jihar Neja'

Gwamna Bago

Asalin hoton, @HONBAGO

Lokacin karatu: Minti 3

Gwamnatin jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya ta ce yawan mutanen jihar da suka tsere daga gidajensu saamakon hare-haren ƴanbindiga a sassan jihar ya zarce 300,000.

Gwamnatin ta ce wannan matsala ta fi zarce abin da mutane ke zato, domin kuwa ta kai yadda tantance haƙiƙanin adadin mutanen da aka sace da waɗanda aka kashe da kuma waɗanda aka tilastawa yin hijira daga ƙauyukansu ba ƙaramin aiki bane.

A wata hira da BBC, kwamishinan yaɗa labaran jihar Neja, Obeh Nuhu Nana ya ce duk da cewa matsalar na da girma sosai, gwamnan jihar Umaru Muhammed Bago na yin aiki tuƙuru domin ganin an kawo ƙarshen ta.

Ya ce ƴanbindigar suna amfani da faɗin dajin da jihar ke da shi, inda suke ɓoyewa a wurare tare da kai hare-haren kan ƙauyuka da al'ummomi ba tare da jami'an tsaro sun iya kama su ba.

''A Neja kam, abin yana da girma don kusan kowanne mako sai ka ji an je an sace mutane ko an kashe mutane.Gwamna ɗin shi kanshi ya yarda cewa lallai wannan abu ba ƙarya bane, lallai yana nan yana faruwa,'' In ji kwamishinan yaɗa labaran.

Dangane da matakan da gwamnatin jihar Neja ke yi domin shawo kan wannan matsala ta tsaro kuwa, Obeh Nuhu Nana ya ce suna da tsare-tsare da dama na tallafawa jami'an tsaro a jihar da nufin cimma nasara. ''Harkar bayar da motoci ne, harkar bayar da gudunmuwa ne, ga DSS ga police ga sojojin ma, duk gwamnatin jihar Neja na yi.''

Ya yi bayanin cewa akwai shiri na musamman da gwamnatin tarayya ta amince da shi, wanda za a aiwatar da haɗin gwiwar jihar Neja nan ba da jimawa ba kuma suna fatan zai taimaka sosai wajen mahance matsalar tsaro a jihar.

A baya-bayan nan dai ana samun karuwar hare-haren 'yan bindiga a Najeriya duk da isowar sojojin Amurka a arewacin kasar don tallafawa dakarun Najeriyar wajen kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi kasar.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wani sabon binciken ƙungiyar da ke kula da alƙaluman wuraren da aka gudanar da rikice-rikici ta ACLED ya nuna cewa kan iyakar Najeriya da Benin da kuma Jamahuriyar Nijar na neman zama wata sabuwar cibiyar rikice-rikice a 2025.

Cikin wani sabon rahoto da ƙungiyar ta fitar a ranar Alhamis, ta ce an samu gagarumar ƙaruwar hare-hare a yankin cikin shekarar da ta gabata.

Ko a cikin makon nan ma sau biyu Lakurawa suna ƙaddamar da hare-hare a jihar Kebbi tare da kashe gomman mutane.

ACLED ta ce rikice-rikicen sun shafi ƙungiyoyin JNIM mai biyayya ga ƙungiyar Al-qaeda da EIS mai biyayya ga ISIS, waɗanda suke da alhakin kashi 86 na ƙaruwar hare-haren idan aka aka kwantata da 2024.

''Haka ma an samu ƙaruwar kashe-kashe da kashi 262 cikin 100'', in ji ACLED.

Akwai kuma rahotannin da ke cewa an kai wani hari a baya-bayan nan a wasu ƙauyukan kananan hukumomin Borgu da Agwara , inda aka ƙone gidaje da dama.

Harin ya bar al'ummar yankunan rasa tudun dafawa, hakan ne ya sa suka yanke shawarar neman mafaka a Jamhuriyar Benin da ke makwabtaka da Najeriya.

Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa BBC cewa, da suka shiga da farko sai mutanen garuruwan suka ji tsoro suka gudu sannan kuma suka bar kayayyakinsu kamar kayan amfanin gona da tufafi da dai sauransu, hakan ne ya sa 'yanbindigar suka sake komawa garin tare da kona shi duka.

"Da suka koma garin ba su samu kowa ba, shi ne suka kone shi, kuma mutanen garin da suka tsere zuwa Jamhuriyar Benin yanzu haka suna cikin kwanciyar hankali domin gwamnatin can tana yakar 'yanbindigar." In ji shi.

" Ko a shekaranjiya a garin Gine, an kashe kusan mutum 100, don haka a yanzu muna cikin halin tsoro sosai." In ji shi.