Falalar goman tsakiya na Azumin Ramadan

Wasu Musulmai suna sallah

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Ramadana wata ne mai alfarma da Musulmai ke shafe tsawon watan suna ibadar azumi, ɗaya cikin shikashikan Musulunci.

Wata ne da ake son Musulmi ya siffantu da bautar Allah da addu'o'i tare da neman gafara ga mahalicci, kamar yadda malamai ke bayyanawa.

Watan Ramadan baki ɗayansa na ƙunshe da falala tun daga 10 na farko, zuwa 10 na tsakiya, da kuma kwanaki mafi daraja na 10 ta ƙarshe.

Shiekh Abubakar Baban Gwale ya yi wa BBC bayani kan falalar 10 ta tsakiya da kuma abubuwan da ake son Musulmi ya himmatu da su.

Malamin ya ce Ramadan wata ne da ake ƙara alherin mumuni a cikinsa - duk lokacin da aka ƙara kwanaki alherinsa yana kara ƙaruwa.

"Manzon Allah (SAW) ya ce farkon watan Ramadan rahama ne, tsakiyarsa kuma gafara ce ƙarshensa kuma 'yanta mutum ne daga wuta," in ji Baban Gwale.

Shehin malamin ya ce idan aka shiga zango na gafara ba wai ana goge rahama ba ne - ana son mutum ya ninka ibada domin ya haɗa rahama da kuma gafara tare da kara kusanci ga Allah.

Cigaban kwanakin Ramadan ƙarin samun falala ne da kuma kusantar dare mai albarka na Laylatul Kadari.

Ayyukan Ibadah da ake son mutum ya dage da su

Wani mutum yana addu'a

Shiekh Abubakar Baban Gwale ya bayyana ayyukan Ibadah da ake son mutum ya dage a kansu kamar haka:

Musulmi ya dage da sallolin farilla da Allah ya wajabta a cikin jam'i.

  • Annabi ya kwaɗaitar da yin sallar Taraweeh da sallolin dare - Ramadan wata ne da Allah ya lazimta azumi a yininsa da kuma raya darensa.
  • Akwai hadisin Abu Hurairah da Buhari da Musulim suka ruwaito cewa duk wanda ya tsaya ya yi sallah cikin dare a watan Ramadan yana mai imani da neman lada za a gafarta masa zunubansa da suka gabata baki ɗaya.
  • Ana son idan Musulmi ya yi Sallar Taraweeh bayan sallar Isha'i a cikin dare ya kuma dage ya raya dare. Kuma duk abin da mutum ya haddace na Al-Kur'ani ya kyautata niyya zai iya yin sallolinsa na dare da abin da ya sawwaƙa.
  • Ana kuma son a ƙara dagewa da karatun Ƙur'ani.
  • Haka nan, ana kuma son ƙara ƙoƙari wajen ciyarwa - kamar yadda ciyarwa take da falala a farkon Ramadan, haka ma a goma ta tsakiya domin ƙarin samun falala da lada.
  • Ana kuma kwaɗaitar da yin kyauta sosai a watan Ramadan. Kyautar Manzon Allah tana ƙaruwa idan Ramadan ya zo, kuma yawan kyautarsa ya fi iskar da ke ɗauke da girgije ta zubar da shi ba tare da rage komi ba.
  • Har wa yau, ana son a dinga yafiya da tausasawa tun daga iyalai da ma'aikatan da ke karkashin mutum.