Yadda dajin Kainji ke neman zama maɓoyar ƙungiyoyin ƴanbindiga a Najeriya

Lokacin da ake binne waɗanda ƴan bindiga suka kashe a Kwara

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Lokacin da ake binne waɗanda ƴan bindiga suka kashe a Kwara
    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

A farkon watan Fabrairun shekarar 2026 ne mahara sama da 100 suka yi dirar mikiya sanye da kayan sojoji a ƙauyukan Woro da Nuku da ke jihar Kwara da ke arewa ta tsakiya a Najeriya, inda suka kashe sama da mutum 75.

Sun dira a ƙauyukan ne da yammacin ranar Talata a daidai lokacin da manoman ƙauyukan suke komawa gida daga gonakinsu.

Babban abin da ya ja hankali shi ne yadda maharan suka aika da wasiƙar zuwa garin domin "wa'azi", sannan suka shiga, suka yi aika-aikarsu, sannan suke fice ba tare da fuskantar matsala ba.

Bayan harin ne gwamnatin Najeriya ta zargi mayaƙan Boko Haram da kai harin, duk da cewa ƙungiyar ba ta ɗauki alhaki ba, duk da cewa ta fi gudanar da ayyukanta a arewa maso gabashin Najeriya.

A lokacin ne mutane suka fara tambayar wai daga ina maharan suka taso, kuma su wane ne su?

Sai dai rahotanni sun nuna cewa akwai mayaƙan Boko Haram ɗin a yankunan Kwara da Neja, inda suke ƙaddamar da hare-hare a jihohi.

Amma daga ina suke fitowa, ta yaya suke shiryawa kafin su kai hare-hare, sannan ina ne babbar maɓoyarsu.

Abdulla Umar Usman, wani tsohon malami a ƙauyen Woro ya shaida wa BBC cewa maharan daga cikin dazukan da ke cikin Gandun Dajin Kainji suka fito.

Ina ne wannan gandun dajin, kuma me ya sa mahara suke ɓoya a ciki?

Gandun Dajin Kainji

Kabiru Adamu, masanin tsaro ne, kuma shugaban kamfanin Beacon security and consulting, ya ce idan ba a yi abin da ya dace ba, akwai barazanar dajin zai iya zama tamkar Sambisa.

"Akwai fargabar hakan. Mun daɗe muna bincike kan wannan daji kuma mun yi rubuce-rubuce tare da ƙoƙarin jawo hankalin gwamnati domin hana hakan ya auku," in ji shi.

Ya ce mutanen da ke zaune a kusa da dazukan sun daɗe suna fama da matsalar tsaro.

"Akwai ƙungiyoi da dama, akwai ƙugiyoyi ko dabobin ƴanbindiga, sannan a baya-baya akwai ƙungiyoyi masu alaƙa da jihadi irin su IS da al'Qaeda da suke shiga dajin suna iko da tozarta mazauna ƙauyukan da ke kusa da dajin," in ji shi.

Kabiru Adamu ya ƙara da cewa akwai barazana babba da ke fuskantar Najeriya, wadda ke buƙatar a ɗauki mataki ba tare da ɓata lokaci ba, "domin gudun kada dajin ya zama matattara irin abin da muka gani a baya a arewa maso gabas (Sambisa)."

Girman daji

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A game da yanayin girman dajin kuwa, Kabiru Adamu ya ce daji mai girma sosai da faɗi.

"A bayanan da ke fitowa, babu daji da ya kai shi girma a Najeriya. Yana iyakar jihohin Neja da Kwara. Idan ka faɗaɗa shi, akwai wasu dazuka da ya shiga cikinsa da ke da alaƙa da jihohin Kebbi da Zamfara a arewa maso yamma, da kuma idan ka nausa, yana da alaƙa da kudu ta jihohin Ondo da Osun, sannan yana zuwa har Jamhuriyar Benin."

Masanin tsaron ya ce kimanin shekara huɗu zuwa biyar ne suka fara sanin akwai ƙungiyoyin ƴanbindiga. Amma a cikin ƴan shekarun baya-bayan nan, mayaƙa masu iƙirarin jihadi suna shiga."

Ya ce yanayin faɗin dajin zai taimaka wa mahara wajen ƙaddamar da hare-hare zuwa sassan ƙasar daban-daban.

"Sannan abu na biyu shi ne babu gwamnati a dajin, wanda shi ne ya fi muhimmanci. Sannan ƙauyukan da ke maƙwabtaka da dajin, ba su da ababen more rayuwa irin su makarantu da asibitoci, sannan ba kasafai ake samun jami'an tsaro da aka jibge a yankin ba."

Ya ƙara da cewa rashin jami'an tsaro a kusa na sa maharan suna cin karensu babu babbaka.

"Ƙauyukan suna fama da matsalolin rashin ababen more rayuwa. Sannan akwai ɗimbin matasa jibge da suke fama da rashin aikin yi. Waɗannan dalilan, da wasu ma sun taimaka wajen ba maharan sauƙin gudanar da harkokinsu," in ji shi.

Zama kamar Sambisa?

Sambia

Asalin hoton, Nigeria Army

Wata fargabar da ake yi, ita ce yiwuwar dajin ya zama kamar Sambisa a nan gaba, lamarin da Kabiru Adamu ya ce akwai dalilai da ke nuna haka.

Ya ce ba ma zama tamkar Sambisa ba, daji ne da zai iya fin Sambisa hatsari saboda, "Ka ga daji ne da ya haɗa ƴanbindiga da ƴanta'adda dabam-daban. Ba ƙungiyar ɗaya ba ce, ƙungiyoyi ne da yawa."

Haka kuma Kabiru Adamu ya ce gwamnati ta matsa lamba kan mayaƙa da ke gabas ta tsakiya, "sannan matakan gwamnatin na aiki. Sai dai yanzu maharan na yanzu akwai alamar sun fahimci salon gwamnati, don haka ita ma gwamnati akwai buƙatar ta canja salo."

Ya ce babban abin da ake buƙata shi ne canja salo, "a lalubo hanyoyin magance matsalar tsaro ta dindindin, kamar magance matsalolin da suke ingiza matsalolin tsaron irin su talauci da jahilci da sauransu."

Rayuwa a dajin Kainji

A game da yadda rayuwar maharan za ta kasance a Gandun Dajin Kainji, masanin na tsaro ya ce akwai abubuwan da suke buƙata.

"Duk da cewa babu cikakken bayani kan yanayin dajin, amma babu abin da zai hana su tsarawa da ɗaukar matakan da Boko Haram ta ɗauka domin rayuwa a arewa maso gabas."

Ya yi misali da baburan da maharan suke amfani da su da suke ɗauke da bindiga a sama, "ka ga ɗaura bindiga a saman babur dole akwai buƙatar walda, walda kuma na buƙatar lantarki. Ka ga ke na dole ko dai da janareta ko kuma amfani da hasken rana wato solar."

Sai dai Kabiru Adamu ya ce da a ce akwai tsari mai kyau na bibiya, za a riƙa gano hanyoyin da suke bi wajen nemo abubuwan buƙatar rayuwa.

"Ai misali kayan walda dole a cikin gari za su saya, da ma wasu kayayyakin da suke buƙata. Amma dai a taƙaice ban ga dalilin da zai hana su gudanar da rayuwarsu ba a cikin dajin," in ji shi.

Matakan kariya

Kabiru Adamu, ya ce matuƙar ba a ɗauki matakin gaggawa ba, za a kai wa ga matakin da za a zo ana da-na-sani.

Sai dai ya ce matakan soji kaɗai ko kuma amfani da ƙarfi ba zai iya hana komai ba, "a ɗauki matakan soji ɗin wato amfani da ƙarfi, sannan a ƙara a haɗa da dabarun tattalin arziki," in ji shi.

Ya ce za a iya mayar da dazukan wurin da gwanati za ta amfana ta hanyar samun kuɗaɗen shiga.

"Na ga ministan tsaron Najeriya ya kafa kwamiti kan nazari dazukan, amma wannan ba aikin ministan ba ne kawai. Ana buƙatar haɗin gwiwar sauran ma'aikatun gwamnati, da kuma a ga sha'awar hakan daga gwamnati."

Ya kuma ce akwai buƙatar a riƙa tafiya da sauran ƙabilu a ayyukan tallafin sauƙaƙa rayuwa da ake yi.

"Kamar makiyaya, za a iya koya wa matasansu sana'o'i irin su kiwon kifi da sarrafa madara da sauransu. Irin wannan ne zai hana ƙungiyoyin samun nasarar jan hankalin matasa zuwa aikata ayyukan assha."