Champions League: Madrid da City, Barca da Newcastle, Arsenal da Bayer

Asalin hoton, Getty Images
An kammala haɗa ƙungiyoyin da za su kece raini a zakayen ƴan 16 na Gasar Zakarun Nahiyar Turai ta Uefa Champions League, inda mai kare kambi PSG za ta kara da Chelsea.
Duk da cewa ƙungiyoyin Ingila shida ne suka kai matakin ƴan 16, amma a cikinsu babu wadda za ta haɗu da ƴar'uwarta.
Sauran wasannin da ake ganin za su yi zafi a gasar su ne karon-batta da za a sake yi tsakanin Real Madrid da Manchester City da kuma Newcastle da Barcelona.
Za a buga fallen farko na wasannin ne ranakun 10 da kuma 11 ga watan Maris, sannan a buga falle biyu na wasannin a ranakun 17 da 18 ga watan na Maris.
Ga cikakken jadawalin karawar zagayen na ƴan 16:
- Paris St-Germain v Chelsea
- Galatasaray v Liverpool
- Real Madrid v Manchester City
- Atalanta v Bayern Munich
- Newcastle United v Barcelona
- Atletico Madrid v Tottenham
- Bodo/Glimt v Sporting CP
- Bayer Leverkusen v Arsenal
Wasan Chelsea da PSG tamkar maimai ne na wasa ƙarshe na gasar cin kofin duniya na ƙungiyoyi, lokacin da Chelsea ta lashe wasan da ci 3-0.
Manchester City da Liverpool da kuma Newcastle duk sun haɗu da ƙungiyoyin da za su kara da su a wasan rukuni, inda City ta lashe karawarta da Real Madrid a watan Disamban da ya gabata.
A ranar 30 ga watan Mayu ne za a buga wasan ƙarshe na gasar a filin wasa na Puskas Arena da ke birnin Budapest a ƙasar Hungary.
Ga yadda ƙungiyoyin za su fafata har zuwa wasan ƙarshe:

Wace ƙungiya ake sa ran za ta lashe Champions League a bana?
Arsenal ce ta kammala matakin rukuni a matsayi na ɗaya, kuma ita ce kaɗai ƙungiyar da ta lashe wasanninta takwasa, inda Bayern Munich ta kammala a matsayi na biyu da tazarar maki uku.
Idan ta lashe karawarta da Leverkusen, Arsenal za ta fuskanci Sporting ko Bodo/Glimt a matakin kwata-fainal.
Kwamfutar Opta ta sanya Arsenal a matsayi na ɗaya cikin jerin ƙungiyoyin da ake ganin za su iya lashe gasar, da maki 27.40%.
Bayern Munich ce ta biyu cikin ƙungiyoyin da ake sa ran za su iya lashe kofin, da maki 14.28%.
Liverpool ce matsayi na uku da maki 12.83%.
Manchester City ce a matsayi na huɗu, a cewar kwamfuta, inda ta ba ta maki 10.79%.











