Yadda mutane ke mutuwa a hannun ƴansanda saboda azaba - Amnesty

Painting on wall wey show a tiger and for di unda dem write 'Tiger Base'

Asalin hoton, AmnestyNigeria/X

Lokacin karatu: Minti 3

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Amnesty International ta ce sashen da ake kira 'Tiger Base' na ƴansandan Najeriya a jihar Imo da ke kudu maso gabashin ƙasar ya zama wata cibiyar cin zarafi da kisa ba tare da ƙa'ida ba.

Amnesty ta bayyana haka ne a rahoton da ta fitar bayan bincike na tsawon lokaci da ta ce ta ɗauki lokaci tana yi biyo bayan yawaitar ƙorafe-ƙorafe da ta ce ta samu kan "wuce iyaka na sashen na Tiger Base."

"Sashen Tiger Base ya fara ƙaurin suna wajen gudanar da aiki ba bisa ƙa'ida ba, da kuma amfani da ƙarfi wajen karɓar kuɗaɗe a hannun mutane da sauran su," in ji shugaban ƙungiyar a Najeriya, Isa Sanusi.

Rahoton na ƙungiyar ya ƙara da cewa sashen na ƴansandan ba ya girmama ƴancin ɗan'adam, "wanda ke ƙara nuna gazawar hukumomin Najeriya wajen daƙile zargin tauye haƙƙin ƴan ƙasarta."

Isa Sanusi ya ce duk a ƙorafe-ƙorafen da aka daɗe ana yi kan ayyukan sashen ƴansandan, har yanzu babu wanda aka tuhuma da laifi a hukumance.

BBC ta yi yunƙurin jin ta bakin kakakin rundunar ƴansandan jihar Imo, Henry Okoye da kwamishinan yaɗa labaran jihar, Declan Emelumba, amma bai ce komai ba.

Rashin imani, tsare mutane a wuri mai muni

Ƙungiyar Amnesty ta ce sashen na Tiger Base na kamawa da tsare mutane, sannan ya azabtar da su.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Mutanen da aka tsare ne suka tabbatar da cewa ana azabtar da su, sannan ana tilasta musu rubuta bayanai, wanda suke amincewa su bayar saboda azaba, sannan ana dukan su da rodi da wayar kebur da watsa musu ruwan sanyi.

"Wasu kuma ana ɗaure su ne ta sama, ya zama kansu na ƙasa, ƙafafunsu na sama, sannan a yanke su, a bar jini ya yi ta zuba," kamar yadda rahoton ya nuna.

Rahoton ya ƙara da cewa akwai daƙin tsare masu laifi guda huɗu a sashen na Tiger Base, kuma kowanne na tsawo da faɗin ƙafa 12-12 ne, "amma kuma a haka suke tsare sama da mutum 70 a kowane daƙi ɗaya."

Rahoton ya kuma nuna cewa akwai waɗanda suka mutu a hannun sashen na Tiger Base, lamarin da rahoton ya alaƙanta da bayanan da ƙungiyar daga waɗanda suka shiga komar ƴansandan suka bayyana.

"A shekarar 2022, wasu jagororin matasa uku sun miƙa wa sashen wani wanda suke zargi da aikata laifi, amma bayan kimanin wata uku, sai suka samu labarin wanda ake zargi mai suna Okechukwu Ogbedagu ya mutu. Amnesty ta nazarci binciken gawar mutum, inda ta gano ya mutu ne saboda rashin shaƙar iska saboda cunkushewarsu."

"Domin ɓoye wannan aika-aikar da suka yi, sai suka tuhumi jagororin matasan guda uku da laifin kisa. Amma daga bisani aka sake su bayan wata shida."

Sashen Tiger base ya fara ƙaurin suna ne a 2025

A ƙarshe-ƙarshen 2025 ne jami'an Tiger Base suka fara ƙaurin suna a kafofin sadarwa na zamani a Najeriya, inda mutane suka fara ƙorafe-ƙorafe kansu, da kuma abubuwan da suka fuskanta.

Haka kuma kafofin yaɗa labarai da dama a cikin ƙasar sun ruwaito irin zaluncin da wasu suka yi zargin musu.

A wancan lokacin ne rundunar ƴansandan jihar, da gwamnati sun musanta zargin, tare da bayyana shi a matsayin maras tushe.

"Tiger Base sashe ne na musamman, kuma aikin su ya ƙunshi yaƙi da masu garkuwa da mutane da fashi da makami da ƙungiyoyin tsafi da sauran manyan laifuka. Ba sashe ba ne na aikata aiki ba bisa ƙa'ida ba, ko wajen yanka mutane."

"Sashen ya samu nasarar daƙile manyan laifuka, kuma duk aikin da ake yi a wajen, yana daidai da doka da oda," in ji Henry Okoye, kakakin rundunar ƴansandan jihar Imo.

BBC ta yi ƙoƙarin sake jin ta bakin Okoye, amma bai ce komai ba.