Matsaloli 7 da suka kamata sufeton ƴansadan Najeriya ya fara magancewa

Tunji

Asalin hoton, Bayo Onanuga/Facebook

Lokacin karatu: Minti 4

A ranar 25 ga watan Fabrairu ne Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya miƙa wa sabon muƙaddashin babban sufeto janar na ƴansandan ƙasar Olatunji Rilwan Disu takardar fara aiki.

Tuni sabon shugaban ƴansandan ya karɓi tutar fara aiki daga tsohon sufeto janar na ƴansandan ƙasar Kayode Egbetokun wanda ya ajiye aiki bisa wasu dalilai, ciki har da wasu al'amura da suka danganci "iyali."

A watan Yunin 2023 ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa Kayode Egbetokun a matsayin sufeta-janar na ƴansandan ƙasar.

Jim kaɗan bayan naɗa shi lokacin ritayarsa ta yi, amma Tinubu ya ƙara masa shekara huɗu, da nufin zai yi aiki zuwa watan Yunin 2027, amma sai kwatsam ya ajiye aiki.

Ganin shugaban na ƴansanda ya karɓi aiki a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar matsalolin tsaro daban-daban, sai wasu suke ganin tamkar ba dole ba ne a samu wani gagarumin sauyi.

Wannan ya sa muka yi tankaɗe da rairaya domin zaƙulo wasu muhimman abubuwa da suka kamata saboda sufeto janar ɗin ya fara mayar da hankali a kansu domin fara aiki da ƙafar dama.

Janye ƴansanda daga manyan mutane

A watan Nuwamban shekarar da ta gabata ne Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya bayar da umarni ga tsohon babban sufeto janar na ƴansandan Najeriya da ya janye ƴansanda da suke gadin ƴansiyasa da manyan mutane.

Manjo Muhammadu Bashir Galma mai ritaya, masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya, ya ce daga cikin abubuwan da suka fi muhimmanci a yanzu akwai buƙatar ya daɓɓaƙa wannan umarnin.

Ko a bara da Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro, ya buƙaci ƴansandan da aka cire daga manyan mutane a ba su horo na musamman, sannan su koma bakin aiki.

Rage wa sojoji aiki

IGP

Asalin hoton, Bayo Onanuga/Facebook

Wani abu da aka daɗe ana muhawara a kai a Najeriya shi ne yadda aikin ɗansanda da na sojoji da sauran jami'an tsaro ke shiga aikin juna.

Manjo Galma mai ritaya ya ce idan aka ƙara horar da ƴansanda hanyoyin tattara bayanan sirri, sannan aka samu haɗin kai da sojoji, za su taimaka wajen kawo ƙarshen matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta,

A ƙa'ida dai harkokin yaƙi da ƴanbindiga da ma Boko Haram na ƴansanda ne, amma sai sojoji suke shige gaba.

Wannan ya sa ake tunanin idan har sabon babban sufeton zai yi abin da ya dace, zai iya rage wa sojoji aiki

Amfani da kimiyya

Wani abu da aka daɗe ana tattaunawa shi ne yadda al'amura da suka shafi ƴansandan Najeriya suke ɗaukar lokaci, maimakon rage cunkoso a ofisoshin ƴansandan ƙasar.

A game da wannan, Kabiru Adamu ya ce majalisar zarwaswar Najeriya ta amince a mayar da wasu ayyukan ƴansanda guda 18 su zama ta na'ura ake gudanar da su, ba sai an je ofis ba, "amma har yanzu ko ɗaya ba a ɗabbaƙa ba."

Haka kuma amfani da kimiyya zai taimaka wajen tattara bayanan sirri da wasu ayyukan na musamman.

Wannan ya sa sabon shugaban ke da buƙatar ya yi gaggawar fara amfani da kimiyya a aikin na ɗansanda.

Jin daɗin ƴansanda

A shekarar 2018 tsohon shugaban Najeriya Muahammadu Buhari ya sanar da ƙarin albashin ƴansanda. To amma har yanzu ana kiraye-kirayen yin ƙarin albashi ga ƴansanda ta yadda zai wadace su, su iya buƙatunsu na yau da kullum ba tare da sanya ido kana bin hannun wasu ba.

Ya kamata Tunji Disu ya yi koƙarin ganin an biya ƴansanda albashi mai tsoka da alawus-alawus tare da tabbatar da walwalarsu.

A game da wannan, Galma ya ce ya kamata sabon babban sufeto janar ɗin ya ba walwalar ƴansanda muhimmanci.

"musamman saboda yawansu za ka ji ɗansanda na ƙorafi rashin gida, ga ƙarancin alawus-alawus. Wannan yana karya gwiwar ma'aikata sosai, kuma ba za su yi aiki da kyau ba," in ji shi.

'Ɗansanda abokin kowa'

Mutane da dama a Najeriya na zargin cewa ƴansanda ba su tafiyar da ayyukansu bisa adalci da bin ƙa'ida.

Haka kuma ana zargin rundunar da jami'anta da cin zarafi da kame-kame ba bisa ƙa'ida ba da rashin bin doka da oda.

Wani masani kan harkar ƴansanda, Dennis Amachree ya ce ɗaya daga cikin manyan ayyukan da suka rataya a wuyan Disu shi ne y asa ƴan Najeriya su riƙa kallon ƴansanda a matsayin abokansu.

Shi ma Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon security and consulting, ya ce, "An daɗe ana ƙorafi da zargin ƴansanda da cin zarafi da tauye haƙƙin ƴan ƙasa. Wannan aiki ne babba domin dole ya fahimtar da al'umma cewa ƴansanda abokansu ne."

Kayan aiki

Wani abu mai muhimmanci shi ne batun kayan aiki, musamman masu muhimmanci da rashinsu ke lalata aikin ɗansanda.

Misali za a je kai ƙara a ce babu mota mai kyau, ko kuma babu man fetur. Wannan ya sa masana da masu sharhi suke ganin akwai buƙatar a samar da kayan aiki na zamani domin sauƙaƙa aikin na ɗansanda.

Siyasa

Ƴan Najeriya dai na zargin ƴansanda da sauran jami'an tsaro na shiga harkokin siyasa, lamarin da yake zama babban abin tsokaci a fagen siyasar ƙasar.

Wannan ya sa ake ganin ƴansanda na da rawar da za ta kata domin tabbatar da an yi babban zaɓen Najeriya cikin lumana.

Sai dai kafin babban zaɓen na Najeriya, akwai zaɓukan gwamna a jihohin Osun da Ekiti, waɗanda za a yi a 2026, inda a nan ne ya kamata sabon muƙaddashin babban sufeto ya fara tauna tsakuwa kafin babban zaɓen ƙasar.

Wajibi ne sufetan ƴansandan ya tabbatar cewa na tura jami'na ƴansanda a faɗin ƙasar domin tabbatar da doka a lokacin zaɓen, ta yadda za a hana ɓata-gari cin karensu babu babbaka, musamman abin da ya shafi tayar da rigingimu da kuma masu son yin magudin zaɓe.