Yau za a tantance yiwuwar cimma yarjejeniyar nukiliya tsakanin Amurka da Iran

Asalin hoton, Reuters/ EPA
A yau ne za a gudanar da zagaye na uku na tattaunawar da ake yi tsakanin Amurka da Iran a Geneva kan shirin makamin nukiliyar Tehran.
Tattaunawar za ta tantance ko za a iya cimma wata yarjejeniya, inda Iran za ta iya haƙura da wasu daga cikin buƙatunta kan shirinta na nukiliya, ciki har da wasu ɓangarorin shirinta na Uranium.
Ana kallon wannan tattaunawar da matukar muhimmanci, musamman yayin da Amurka ke ƙara karfin dakarunta a Gabas ta Tsakiya, mafi yawa tun bayan mamayar da ta kai wa Iraƙi a shekarar 2023.
Iran itama ta ƙara karfafa shirinta domin tunkarar duk wani hari da ka iya zuwa.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan batun nukiliya, amma ya jaddada cewa yadda Iran ke dagewa kan cire batun makamai masu linzami shi ne babban ƙalubale a tattaunawar.

